Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Trabzonspor ta Turkiyya na dab da kammala ɗaukar fitaccen ɗan wasan Masar, Mohamed Salah , bayan tarbar da magoya bayanta suka yi masa lokacin da ya isa ƙasar.
Ɗaruruwan magoya bayan Trabzonspor sun taru a wajen Filin Jirgin Sama na Atatürk da ke Istanbul a ranar Laraba domin tarbar Salah, wanda ya fito sanye da kayan da ke ɗauke da launukan ƙungiyar.
Salah, mai shekaru 34, ya bar Liverpool a ƙarshen kakar wasan da ta gabata bayan shafe shekaru tara a Anfield, inda ya zura ƙwallaye 257 tare da taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin da ƙungiyar ta samu.
Har yanzu ba a bayyana cikakken albashin da Salah zai riƙa karɓa a Trabzonspor ba. Sai dai kasancewarsa ya koma ƙungiyar a matsayin ɗan wasa mai zaman kansa, ana sa ran Trabzonspor za ta mayar da hankali wajen samar masa da albashi mai tsoka.
Fitaccen ɗan wasan, wanda ya zura ƙwallaye 50 a gasar UEFA Champions League, zai samu damar ci gaba da taka leda a gasar zakarun Turai tare da Trabzonspor a kakar wasa mai zuwa, bayan ƙungiyar ta kammala kakar da ta gabata a matsayi na uku a gasar Super Lig ta Turkiyya, da tazarar maki takwas tsakaninta da zakarun gasar, Galatasaray.
