Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Tinubu ya ce an ba shi wata babbar dama ta shiga cikin Ka’aba Mai Tsarki tare da wasu mambobin tawagarsa, inda suka gudanar da addu’o’i tare da ibadar Umrah.
A cikin saƙon nasa, shugaban ya ce: “Na kammala ziyarar ibada ta a Saudiyya, tare da mambobin tawagata, muka samu wata gagarumar karramawa ta shiga cikin Ka’aba Mai Tsarki domin yin addu’a, tare da gudanar da Umrah.”
Ya kuma bayyana ziyarar da abubuwan da ya gani a Saudiyya a matsayin wata shaida ta ɗorewar alaƙar addini, abota da mutunta juna tsakanin Najeriya da ƙasar Saudiyya.
A makon da ya gabata ne Shugaba Tinubu ya tafi ƙasar Saudiyya domin gudanar da ibadar Umrah, tare da wasu mambobin tawagarsa
