Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su , tare da dakile wani yunƙurin sace wasu mutane a yayin samamen da dakarunta suka kai kan ’yanbindiga a Jihar Zamfara.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar Operation Fansan Yamma , Kanal Aliyu Danja, ya ce an gudanar da ayyukan ne a ƙananan hukumomin Anka da Bungudu .
Kanal Danja ya ce binciken farko ya nuna cewa ’yanbindigar sun yi garkuwa da mutanen ne daga ƙaramar hukumar Gummi , inda suka shafe kusan makonni uku a hannun masu garkuwar kafin a ceto su.
Ya ce a halin yanzu waɗanda aka ceto suna samun kulawar lafiya da sauran tallafin da ya dace, kafin a miƙa su ga iyalansu.
A wani samame da aka kai a ƙaramar hukumar Bungudu kuma, rundunar ta ce ta dakile yunƙurin yin garkuwa da wasu mutane bayan da ’yanbindiga suka kai hari garin Dankurmi .
Rundunar ta ce dakarunta za su ci gaba da gudanar da ayyuka domin dakile ayyukan ’yanbindiga da kuma tabbatar da tsaron al’ummar yankin.
