A cikin wata sanarwa da Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya sanya wa hannu, PRP ta bayyana cewa yawaitar kashe-kashe da sace mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, na nuna cewa tsarin doka da oda a ƙasar na fuskantar babban ƙalubale.
local
PRP Ta Zargi Gwamnatin Tinubu Da Gazawa Wajen Magance Matsalar Tsaro
Jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gazawa wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya, yayin da hare-hare, kashe-kashe da sace-sacen mutane ke ci gaba da zama babban ƙalubalen tsaro a sassan ƙasar.
