An naɗa tsohon kyaftin ɗin Arsenal da tawagar Faransa, Patrick Vieira, a matsayin sabon babban kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta maza ta Senegal, Teranga Lions. Wannan ne karon farko da Vieira zai jagoranci tawagar ƙasa a matsayinsa na koci.

Vieira, mai shekaru 50 , ya maye gurbin Pape Thiaw, wanda Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal ta sallama bayan da ƙasar ta fice daga gasar Kofin Duniya ta 2026 a zagayen ’yan 16.

An haifi Vieira a Dakar , babban birnin Senegal, kafin iyalinsa su koma Faransa yana ɗan shekara takwas. Daga baya ya wakilci Faransa sau 107 , inda ya lashe Kofin Duniya na 1998 da kuma gasar Euro 2000. A matakin ƙungiyoyi kuma ya yi fice sosai musamman a Arsenal, inda ya lashe kofunan Premier League uku.

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal ta bayyana naɗin Vieira a matsayin wani zaɓi na dabarun wasanni da ya yi daidai da burin ƙasar na gina ingantaccen tsarin ƙwallon ƙafa.

Ana sa ran Vieira zai fara aikinsa a lokacin hutun wasannin ƙasashe na watan Satumba , lokacin da Senegal za ta fara shirye-shiryen neman gurbin shiga gasar AFCON 2027 .

Kafin wannan naɗi, Vieira ya horar da ƙungiyoyi irin su New York City FC, Nice, Crystal Palace, Strasbourg da Genoa . Ya bar Genoa a watan Nuwamban 2025, kuma tun daga lokacin bai riƙe wata ƙungiya ba.

A Crystal Palace, ya jagoranci ƙungiyar zuwa matsayi na 12 a Premier League a kakar 2021/22, tare da kai wa wasan kusa da na ƙarshe na FA Cup. Najeriya...