An bayar da lambar yabon ne yayin wani taron horaswa kan shirin Digital Literacy for All, wanda aka gudanar a Abuja, babban birnin Nijeriya.
Hukumar ZITDA ta bayyana cewa wannan karramawa na nuna nasarorin da aka samu wajen faɗaɗa ilimin fasahar zamani a Jihar Zamfara, ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal.
A cewar hukumar, ƙoƙarin ya haɗa da bunƙasa ƙwarewar ɗalibai, ma’aikatan gwamnati da ’yan kasuwa wajen amfani da fasahar zamani, domin sauƙaƙa ayyuka da inganta harkokin tattalin arziki.
Hukumar ta ƙara da cewa faɗaɗa ilimin fasahar zamani na da muhimmanci wajen bai wa al’umma damar cin gajiyar sabbin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa kasuwanci a duniyar zamani.
Lambar yabon na ƙara jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin fasahar sadarwa na jihohi da na tarayya wajen inganta ilimin fasahar zamani da kuma ƙarfafa ƙwarewar al’umma a Nijeriya.
