Kamfanin NNPC Limited da abokan hulɗarsa na OML 118 sun rattaba hannu kan muhimman yarjejeniyoyi da za su ciyar da aikin Bonga Southwest/Aparo gaba zuwa matakin yanke shawarar zuba jari na ƙarshe.

A cewar wata sanarwa da Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin, Andy Odeh, ya fitar, ana sa ran aikin zai jawo zuba jari har dala biliyan 21 , abin da zai mayar da shi cikin manyan ayyukan hako mai daga teku da aka taɓa gudanarwa a Najeriya.

Ana sa ran aikin zai iya samar da gangar mai har 175,000 a kowace rana a lokacin da ya kai kololuwar samarwa.

Babban Daraktan Gudanarwa na NNPC Limited, Bashir Ojulari, ya ce yarjejeniyar wata shaida ce da ke nuna cewa sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya aiwatar a fannin mai da iskar gas suna fara sauya manufofi zuwa ainihin zuba jari.

Aikin Bonga Southwest/Aparo ya kuma kammala aikin pre-engineering design , yayin da aka riga aka zaɓi kamfanin da zai gina babbar na’urar samar da mai da ke iyo ( Floating Production Facility ).

Jami’an sun bayyana cewa aikin zai taimaka wajen bunƙasa amfani da kamfanonin cikin gida da ƙara ƙwarewar ’yan Najeriya a fannin mai da gas, tare da samar da guraben ayyukan yi da ƙara kuɗaɗen shiga ga gwamnatin tarayya.

Ana kuma sa ran aikin zai ƙara ƙarfafa matsayin Najeriya a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙasashen Afirka wajen samar da man fetur daga rijiyoyin da ke ƙarƙashin teku.