Hukumar ta kuma kama wani ɗan Najeriya mai shekaru 58, bisa zargin safarar kusan kilo 25 na ƙwayar Methamphetamine.

Dukkan waɗannan mutanen an kama su ne a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas.

A cewar NDLEA, wanda ake zargin ɗan wasan ƙwallon kwandon, mai suna Greene Da’monte Khiree, ya shigo Najeriya ne daga Thailand ta Dubai a ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba.

Hukumar ta ce jami’anta sun lura da shi lokacin da yake ƙoƙarin barin jakunkunansa guda biyu da aka yi wa rajista, kafin ya fice daga filin jirgin da ƙaramar jakarsa kawai.

Da yake amsa tambayoyi, Da’monte ya bayyana cewa ya zo Najeriya ne domin yawon buɗe ido da kuma ƙulla alaƙar da za ta taimaka masa a harkar ƙwallon kwando.

Sai dai NDLEA ta ce binciken da ta gudanar a wayarsa ya gano wasu bayanai da ke nuna cewa yana da masaniya kan safarar miyagun ƙwayoyi.

A wani samame na daban, jami’an hukumar sun kama wani ɗan Najeriya mai suna Chinedu Onwude, mai shekaru 58, bisa zargin safarar kilo 25 na Methamphetamine daga Afirka ta Kudu.

Hukumar ta ce an gano ƙwayar ne a ɓoye cikin kwalayen kayan abinci da ke cikin akwatunansa.

Shugaban NDLEA ya yi kira ga al’umma da su taimaka wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi, ta hanyar kai rahoton duk wani motsi ko lamari da suke zargi ga hukumomin tsaro.