Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Lawan Shiisu Adam, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a ƙauyen Malamawar Fulani da ke ƙaramar hukumar Garki.
Ya ce rikicin ya ɓarke ne bayan zargin wasu makiyaya da shigar da dabbobinsu gonakin manoma, lamarin da ya sa manoma da wasu mazauna ƙauyen suka yi yunƙurin korar dabbobin.
A sakamakon haka, an samu arangama tsakanin ɓangarorin biyu, wadda ta yi sanadin mutuwar mutum uku tare da jikkata wasu biyu.
''Sakamakon hakan ne aka samu arangama tsakanin ɓangarorin biyu, lamarin da ya haddasa rasuwar mutum uku da raunata biyu,'' in ji shi.
SP Shiisu ya ce zuwa yanzu hankula sun kwanta a yankin, kuma an ci gaba da gudanar da harkokin yau da kullum.
Ya ƙara da cewa rundunar ƴansandan na ci gaba da gudanar da bincike domin gano waɗanda ke da hannu a tashin hankalin tare da kama su.
''Muna ci gaba da gudanar da bincike domin kama waɗanda ke da hannu a tashin fitinitar,'' in ji kakakin ƴansandan.
