Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya ɓarke ne ranar Asabar, kuma ya ci gaba har zuwa safiyar Lahadi, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.
Wani mazaunin yankin, Danlami Ibrahim, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa rikicin ya samo asali ne bayan wasu makiyaya sun shigar da dabbobinsu cikin gonar gyaɗa da ba a girbe amfanin gonar cikinta ba.
A cewarsa, lokacin da mai gonar ya tunkari makiyayan domin magance matsalar, ɗaya daga cikinsu ya sare shi a hannu da adda.
Lamarin ya fusata wasu mutanen gari, inda rikici ya ɓarke, wanda ya yi sanadin mutuwar makiyaya uku, a cewar rahoton.
Ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), reshen ƙaramar hukumar Gwagwalada, ta tabbatar da mutuwar makiyaya ukun.
An tura jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya
Kakakin rundunar ’yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ba ta ƙarin bayani ga jaridar ba a lokacin da aka tuntube ta.
Sai dai rahotanni sun ce shugaban ’yan sandan yankin, SP Aaron H. Kaura, ya ziyarci wurin da lamarin ya faru.
Bayan haka, an tura jami’an sojoji, ’yan sanda, Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC) da ’yan banga zuwa yankin domin shawo kan lamarin da dawo da zaman lafiya.
Rikicin manoma da makiyaya ya kasance ɗaya daga cikin matsalolin tsaro da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi a wasu sassan Nijeriya, musamman a yankin Arewa ta Tsakiya.
Yawanci, irin waɗannan rikice-rikice na faruwa ne sakamakon takaddama kan filayen noma, lalacewar amfanin gona da kuma shigar dabbobi cikin gonaki.
