Kamfanin Dillancin Labaran Japan, Kyodo, ya ruwaito cewa wani babban jami’in gwamnatin Iran da ba a bayyana sunansa ba ya ce ƙasar na shirin buɗe Mashigar Hormuz cikin mako guda, domin sassauta takunkumin da aka kakaba mata.
A cewar rahoton, matakin na daga cikin yunƙurin Tehran na komawa kan teburin tattaunawa da Amurka domin kawo ƙarshen yaƙin.
Kyodo ya ce jami’in ya bayyana cewa Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran da Jagoran Addinin ƙasar, Mojtaba Khamenei, sun amince da wannan shawara.
Rahoton ya ƙara da cewa masu shiga tsakani sun riga sun gabatar da shawarar Iran ga gwamnatin Amurka.
Jami’in ya ce Iran na son ganin wasu alamomi da za su tabbatar da cewa Amurka na da niyyar komawa teburin sulhu, ciki har da dakatar da ayyukan soji a Mashigar Hormuz da kuma kawo ƙarshen ci gaba da toshe tashoshin jiragen ruwa na Iran.
Mashigar Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar man fetur a duniya, kuma duk wani sauyi kan zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin na iya yin tasiri ga kasuwannin makamashi na duniya.
