Wani kazamin faɗa tsakanin ’yan bindiga da ’yan banga ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 50 a jihar Zamfara, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Rahotanni sun ce ’yan banga daga ƙauyen Zoma da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum sun yi wa ’yan bindigar kwantan ɓauna ne a lokacin da suke wucewa ta wani ƙauye a ranar Alhamis, bayan sun sace mutane da dama a garin Gummi.
Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa AFP cewa ’yan banga sun kashe ’yan bindiga 44, yayin da su kuma suka rasa mutum tara a artabun.
Rahotannin sun kuma bayyana cewa an kashe wani fitaccen shugaban ’yan bindiga mai suna Jiji, wanda ake zargin ya jagoranci sace mutanen a ƙauyen.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya da ke fama da matsalar ’yan bindiga, waɗanda ke kai hare-hare, yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da kuma satar dabbobi.
