Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta gano gawarwaki tara a kan hanyar Wawa-Lumma da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja, lamarin da ake zargin ’yan bindiga ne suka aikata.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun , ya tabbatar wa BBC cewa jami’an ’yan sanda da sojoji sun isa wurin bayan samun rahoton gano gawarwakin a ranar Talata.
Ya ce jami’an tsaron sun kwashe gawarwakin daga wurin, yayin da suka ƙara tsaurara sintiri da binciken wuraren da ake zargin ’yan bindiga na fakewa .
SP Abiodun ya bayyana cewa an ƙara yawan jami’an tsaro a kan hanyar Wawa-Lumma da yankunan da ke kewaye da ita, domin hana sake faruwar irin wannan hari da kuma tabbatar da tsaron matafiya.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a wasu sassan Jihar Neja, musamman yadda matafiya ke fuskantar barazanar hare-haren ’yan bindiga.
Hanyar Wawa-Lumma na daga cikin hanyoyin da ke haɗa wasu yankunan jihar, yayin da hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan Neja suka jefa matafiya da mazauna yankunan cikin fargaba.
Rundunar ’Yan Sandan ta ce ayyukan jami’an tsaro na ci gaba da gudana a yankin domin gano waɗanda ke da hannu a kisan tare da tabbatar da cikakken tsaro a hanyar.
