Kotu Ta Yanke Wa Mutum Huɗu Hukuncin Kisa Kan Harin Cocin Owo
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutum huɗu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin hannu a harin da aka kai Cocin Katolika ta Saint Francis da ke Owo a Jihar Ondo a ranar 5 ga Yunin 2022. Mai Shari’a Emeka Nwite ya yanke hukuncin ne bayan kotun ta same su da laifuka tara da suka haɗa da ta’addanci, haɗa baki domin aikata laifi, satar mutane da kuma kashe masu ibada sama da 40 a harin da ya girgiza Najeriya. Waɗanda aka yanke wa hukuncin na daga cikin mutum biyar da Hukumar Tsaro ta DSS ta gurfanar kan zargin hannu a harin, wanda ya kuma yi sanadin jikkatar fiye
