AMMASCO RADIO NEWSROOM

Lafiya

Gwamnatin kano ta sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da zagon kasa ga kokarinta na wadata asibitocin kano da magunguna

Shugaban hukumar Samar da magunguna ta Jihar Kano Pharm. Ghali Sule ne ya bayyana hakan ga manema Labarai, a yayin kaddamar da shirye shiryen da hukumar ta shirya don gudanar da bikin cikar Gwamna abba shakera uku da kokarin wadata Jihar kano da magunguna masu sauki a asibitoci. Bikin da hukumar ta Fara a safiyar yau a harabarta dake nan Kano, da aka soma da saukar Alfur'qani mai girma, don Nasarar Gwamnan da wanzuwar zaman lafiya a kano. Pharm. Ghali ya Kara da cewa, a ranar 14 za a gabatar da taron wayar da Kan mutane Kan aiyukan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya Samar a Jihar Kano a fannin lafi

MDD: Hare-haren Jirage Marasa Matuƙa Sun Kashe Ƙananan Yara 330 A Sudan Cikin Watanni Shida

Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta bayyana cewa hare-haren jirage marasa matuƙa a Sudan sun yi sanadin mutuwar ƙananan yara 330 a cikin watanni shida na farkon shekarar bana. A cewar MDD, mafi yawan hare-haren sun auku ne a yankunan Darfur da Kordofan, waɗanda suka kasance cikin tsananin tasirin rikicin da ke ci gaba da addabar ƙasar. Hukumar ta ce wannan ne adadi mafi yawa na ƙananan yara da aka kashe sakamakon hare-haren jirage marasa matuƙa tun bayan fara rikicin Sudan. Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna matuƙar damuwa kan ƙarin ta'azzarar rikicin da tasirinsa ga fararen hula, musamman yara, tar

Gwamnatin tarayya ta samar da kayan haihuwa a asibitocin Jihar jigawa na kimanin Naira Biliyan 10

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da rabon kayayyakin kula da mata masu juna biyu da jarirai a lokacin gaggawa, da kayan haihuwa da magunguna na kimanin Naira biliyan 10 domin ƙarfafa ayyukan kula da lafiyar mata da yara a Jihar Bauchi. Wakilinnmu Adamu Abdullahi ya rawaito cewa, Ma'aikatar Lafiya da Jin Daɗin Al'umma ta Tarayya ce ta ƙaddamar da wannan shiri a ranar Asabar, da nufin rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai ta hanyar samar da kayan aikin asibiti, motocin daukar marasa lafiya (ambulance), kayan haihuwa da kuma muhimman magunguna ga cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin jihar. Da yak

An Fara Gwajin Sabon Maganin Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da fara gwajin wani sabon magani da ake fatan zai taimaka wajen yaƙi da nau'in ƙwayar cutar Ebola mai suna Bundibugyo , wadda ke ci gaba da yaɗuwa a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo). Shugaban WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus , ya bayyana a ranar Alhamis cewa an yi wa majiyyaci na farko rajista domin fara gwajin maganin a ƙasar. Alƙaluman WHO sun nuna cewa cutar ta riga ta kama sama da mutum 1,400 , yayin da 438 suka rasa rayukansu sakamakon ɓarkewar cutar. Hukumar ta ce har yanzu babu wani allurar rigakafi ko magani da aka amince da shi don

Gwamnatin Kano ta kaddamar da rabon maganin sama da miliyan 2.9M ga yara dake kananun hukumomi 36 karkashin Shirin SARMAAN II zagaye na uku

Gwmanatin kano ta jaddada kudurin na Cigaba da inganta kula lafiyar yara ta hanayar raba magunguna ga kana nan yara a kananun hukumomi 36 Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan, yayin kaddamar da shirin SARMAAN 11 zagaye na uku, na rabon magunguna kyauta ga yara Yan wata daya zuwa Shekara biyar. Magungunan sun hadar da na gudawa da ciwon sanyi da ciwon kunne da Sauran cututtuka dake tasiri wajen nakasa yara. Wakilinnmu Adamu Abdullahi ya rawaito Kwamishinan Lafiya Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne cewa, Gwamnantin Kano ta tanadi akalla kwalban magani

Alamomin Farko na Cutar HIV da Ya Kamata a Sani

Masana lafiya sun bayyana cewa mafi yawan mutanen da suka kamu da cutar HIV kan fara nuna alamomi masu kama da na mura cikin makonni biyu zuwa shida bayan kamuwa da cutar. Sai dai bayan waɗannan alamomin sun gushe, mutum na iya rayuwa na tsawon shekaru ba tare da wata alama ba , duk da cewa ƙwayar cutar na ci gaba da raunana garkuwar jikinsa a hankali. Alamomin farko da aka fi gani sun haɗa da: Zazzabi Ciwon wuya Kuraje a jiki Kasala ko gajiya mai yawa Ciwon gaɓoɓi Kumburin ƙwayoyin lymph (kaluluwa) a wasu sassan jiki Masana sun ce idan mutum ya ga irin waɗannan alamomi, musamman bayan kasance

Jihohin Najeriya da Suka Fi Samun Sabbin Masu Dauke da HIV a 2025

Rahoton "The State of the Health Nation Report 2025" da Ma'aikatar Lafiya da Walwalar Jama'a ta Najeriya ta fitar ya nuna cewa an samu sabbin masu ɗauke da cutar HIV 102,251 a faɗin ƙasar cikin shekarar 2025. Rahoton ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da gwamnati da abokan hulɗarta ke yi wajen rage yaɗuwar cutar, har yanzu ana samun ƙarin sabbin masu kamuwa da ita. A cewar Hukumar NACA , a halin yanzu akwai kusan mutane miliyan 1.9 masu ɗauke da cutar HIV a Najeriya. Jihohin da suka fi samun sabbin masu HIV a 2025 Lagos – 10,430 Rivers – 6,287 Kano – 6,106 Akwa Ibom – 5,413 Taraba – 4,854 Benue –

MDD TA CE ANA AMFANI DA CIN ZARAFI A MATSAYIN MAKAMIN YAƘI A RIKICIN SUDAN

Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa ana amfani da cin zarafi na jima'i a matsayin makamin yaƙi a rikicin Sudan, inda ta ce adadin lokutan da aka tabbatar sun kasance kaɗan ne idan aka kwatanta da ainihin yawan laifukan da ake aikatawa. A wani rahoto da Ofishin Kare Haƙƙin Dan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ya fitar, an ce an samu rahotannin lokuta 546 na cin zarafi masu alaƙa da rikici a jihohi 16 daga cikin 18 na Sudan tsakanin watan Afrilun 2023 da Afrilun 2026. Rahoton ya nuna cewa aƙalla mutum 838 ne abin ya shafa, ciki har da mata 539, yara mata 284, maza takwas da yara maza bakwai.

MDD ta ye Gargadi Kan pillar core Tallafin Hiv da Amurka Ta yi wa Afrirka to Kudu

Shugabar Hukumar UNAIDS ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Winnie Byanyima, ta yi gargaɗin cewa janye tallafin yaƙi da cutar HIV da Amurka ta yi wa Afirka ta Kudu na iya haifar da asarar rayuka da kuma jefa masu ɗauke da cutar cikin mawuyacin hali. Ta bayyana hakan ne gabanin taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan cutar HIV, inda ta ce tallafin Amurka ya taka muhimmiyar rawa musamman wajen shirye-shiryen hana yaɗuwar cutar a ƙasar. Rahotanni sun nuna cewa jami'an Amurka sun danganta matakin da zargin rashin kare haƙƙin fararen fata a Afirka ta Kudu, zargin da gwamnatin Pretoria ta musanta. A nata ɓangaren

Gwamnatin Kano ta rufe Makarantun koyar da harkokin Lafiya na IBN SINA College of Health Science and Technology da ke Dakata da kuma Life Line College of Health Science and Technology da ke titin bela.

Gwamnatin Jihar Kano ta rufe makarantun koyar da harkokin lafiya na IBN SINA College of Health Science and Technology da ke Dakata Kawaji kusa da Masallacin Juma’a, da kuma Life Line College of Health Science and Technology da ke Dakata Industrial Area, kan titin Bela Road, Tsamiyar Gare, tare da titin Mai Sikeli. Wannann na cikin wata Sanarwa da Mai magana da yawun hukumar Nabilisi Abubakar Kofar na'isa ya sanyawa hannu. Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki matakin rufe cibiyoyin ne bayan wani cikakken bincike da Ma’aikatar Lafiya ta gudanar, wanda ya nuna cewa cibiyoyin biyu ba su cika ƙa’idoji

Cutar Ebola ta kashe mutane 200 inda Sama da mutane 900 suka kamu a Afrika

Cutar Ebola cikin Yan kwanaki ta yi ajalin mutane sama da 200, tare da kama jimillar mutane sama da 900, a cikin ƙasashen gabashin Afrika musamman Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo. Dr. Jean Kaseya shugaban na CDC ya ce jiran tallafin magunguna da rigakafi da kuma kayan kariya daga ƙetare na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke ƙara baiwa cutar damar bazuwa la’akari da irin tsahon lokacin da ake ɗauka kafin ƙasashen da ke bayar da tallafi su saki kuɗaden. Lokaci yayi da ya kamata Afrika ta kula da kanta ba tare da jiran masu bayar da taimako ba. Dr Jean ya bayar da misalin irin yadda ƙasashen Tur

Hukumar Lafiya a matakin farko Haɗin gwiwa da shugabanin Kananun hukumomin kano sun fito da wani Daftari mai matakai shida na inganta kiwon Lafiya a jihar kano

Hukumar Kula da Lafiya ta Matakin Farko ta Jihar Kano (KSPHCMB) tare da Shugabannin Kananan Hukumomi 44 na jihar sun amince da wani daftarin tsarin aiki mai matakai shida da nufin ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya a matakin farko da inganta gaskiya da riƙon amana, da kuma kyautata shugabanci a fannin lafiya a faɗin Jihar Kano. Wannann na cikin wata Sanarwa da Mai magana da yawun hukumar ta Jihar Kano Sa'adatu Sulaiman ta rabawa manema Labarai. An cimma waɗannan matsaya ne a yayin taron rabin shekara da aka gudanar na tsawon kwanaki biyu da aka gudanar a Jihar kaduna Taron ya mayar da hankali kan ne

Sama da mutum dubu Goma sha uku 13 masu fama da cutar amosanin jini ne ke amfana da kulawa da magani kyauta a karkashin cibiyar Abba Care Sickle Cell Diseases Centre a Jihar Kano.

Sama da mutum dubu Goma sha uku 13 masu fama da cutar amosanin jini ne ke amfana da kulawa da magani kyauta a karkashin cibiyar Abba Care Sickle Cell Diseases Centre a Jihar Kano. Shugabar Hukumar Taimakon Lafiya ta Jihar Kano, Dr. Rahila Mukhtar, ce ta bayyana hakan yayin wani gangamin tattaki da aka gudanar a ranar Asabar, a matsayin wani bangare na bikin ranar wayar da kan al'umma kan cutar amosanin jini. Dr. Rahila ta ce an yi amfani da wannan rana ne wajen jan hankalin jama'a da su kara kaimi wajen ba masu fama da cutar kulawa da goyon baya. Ta kuma yabawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Y

FAAN ta ɗauki tsauraran matakan kariya a dukkan filayen jiragen saman ƙasa da ƙasa domin dakile yaduwar cutar Ebola bayan bullarta a wasu sassan Afirka ta Tsakiya

Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya, FAAN ta ɗauki tsauraran matakan kariya a dukkan filayen jiragen saman ƙasa da ƙasa domin dakile yaduwar cutar Ebola bayan bullarta a wasu sassan Afirka ta Tsakiya. A wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a da Kare Haƙƙin Fasinjoji na hukumar, Henry Agbebire, ya fitar, FAAN ta ce tana aiki tare da cibiyar dakile yaduwar cututtuka, Hukumar Kula da Lafiyar Tashoshin Jiragen Ruwa da Sama, da sauran hukumomi domin ƙarfafa sa ido kan fasinjojin da ke shigowa Najeriya, musamman daga yankunan da ake fuskantar haɗarin cutar. Hukumar ta bayyana cewa ana