AMMASCO RADIO NEWSROOM

Nishaɗi

Kamfanin shirya fina-finai Abnur Entertainment, masu film din KADDARATA sun nesanta kansu da kalaman Nafeesa Abdullahi Kan batun Aure

Cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar sun bayyana cewa "Muna sanar da jama’a cewa fim din Kaddara da daukacin masu shirya fim din ba su da wata alaka da kalaman da Nafisa Abdullahi tayi kan batun aure" Inda suka Kara da cewa, Ra’ayin da ta bayyana ra’ayinta ne na kashin kanta, kuma ba ya wakiltar manufar fim din Kaddara, masu shirya shi, ko duk wani bangare da ke da alaka da aikin. Sanarwar ta cigaba da bayyana cewa " Mu a matsayinmu na masu shirya fina-finai, muna mutunta darajar aure da muhimmancinsa a cikin addini da al’adunmu" . Haka kuma muna Allah wadai da duk wani furuci da zai iya r

Nafisa Abdullahi Ta Jawo Ce-ce-ku-ce Bayan Furucinta Kan Aure

Fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta janyo muhawara a kafafen sada zumunta bayan bayyana ra’ayinta game da aure, inda ta ce a ganinta babu wani abu a cikin aure face nauyi da ya fi rataya a wuyan mata. Jarumar ta bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta, inda ta tattauna kan yadda take kallon rayuwar aure da kuma matsayin mata a cikinta. A cewarta, wasu daga cikin abubuwan da mata ke fuskanta bayan shiga rayuwar aure na sa ta ganin cewa akwai nauyi mai yawa da ke kan mata idan aka kwatanta da maza. Kalaman nata sun haifar da martani mabambanta daga

Mawaki soja Boy ya kalubalanci salon jagorancin Ali Nuhu

Mawakin ya ce da ace shi aka ba irin wannan kujera, da ya gindaya sharudda ga Shugaban Kasa kafin ya karba, kuma da zai yi murabus idan har bai iya kawo canji mai anfani cikin shekaru uku ba. Ya ce: “Duk inda ba zan iya kawo sauyi mai anfani ba, bana son kasancewa a wurin. Bata lokaci ne kawai.” Soja Boy ya kuma yi zargin cewa babban abin da shugaban Hukumar Fina-finai ta Nijeriya ke yi shi ne halartar tarukan Kannywood a kasashen waje kamar India, Paris, London da Jamus ta hanyar takardun izinin gwamnati (memos), yana daukar hotuna yana wallafawa a shafukansa. Ya yi kira ga masana’antar kirki