Putin na ziyara a China bayan Trump ya gaza sauya ra’ayin Xi kan yaƙin Ukraine
Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a ƙasar China a yau Talata, kwanaki kaɗan bayan ziyarar da Donald Trump y...
Ammasco Radio90.7 FM · Gaskiya Tushen NasaraAMMASCO RADIO NEWSROOM
Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a ƙasar China a yau Talata, kwanaki kaɗan bayan ziyarar da Donald Trump y...
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta kuɓutar da ɗalibai da malamai da aka sace daga makarantu a jihar Oyo State da ke kudancin ƙasar. A cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya yi Allah-wadai da rahotannin da ke cewa an kashe ɗaya daga cikin malaman makarantar da aka sace tare da ɗaliban a garin Ogbomosho na jihar Oyo. A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu ƴan bindiga suka kai hari yankin Esiele na ƙaramar hukumar Oriire a jihar Oyo State, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da malamai daga makarantu huɗu. Rahotan
Mace mafi ƙanƙanta a duniya wacce ke yawo da taimakon keken guragu mai sarrafa kansa, Wildine Aumoithe, ta kafa tarihi wajen samar da damammaki a guraben da babu wanda ya taɓa samu. A tsawonta da ya kai inci 2 ft 4 ko kuma 72cm, ita ce mace mafi gajarta a fannin kwararriya mai tallan kayan ƙawa a duniya. Sai dai waɗannan bajinta da ta lashe guda biyu na Guiness World Record suna ne da suka karaɗe kafafen watsa labarai. Ainihi labarin shi ne yadda take amfani da su. An haife ta kuma ta girma a birnin Miami na Amurka ga iyayenta ‘yan asalin Haiti, Wildine tana da cutar SADDAN dysplasia, wani nau
Bayan gaza cimma matsaya ta hanyar sulhu a mafi yawan jihohin Najeriya, magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki na ci gaba da gudanar da zaɓukan fidda gwani ta hanyar kaɗa ƙuri’a. A jihohi da dama ciki har da Jigawa State da Nasarawa State da Plateau State baya ga Katsina State, an ga yadda wasu daga cikin ƴan majalisun da ke kan kujerunsu suka gaza samun tikitin sake tsayawa takara a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar. Salon siyasar Najeriya a wannan karo ya zo da sauye-sauye masu ɗaukar hankali, tun daga yawaitar sauya sheƙa tsakanin jam’iyyu har zuwa yadda aka gudanar da zaɓuka
Shugabar makarantar Community Grammar School da ke garin Esiele a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo State, Alamu F.O, wacce ke cikin malamai da ɗaliban da aka yi garkuwa da su a ranar Juma’ar da ta gabata, ta roƙi gwamnatin Najeriya da ta jihar Oyo tare da ƙungiyar kiristoci ta Najeriya da su kai musu ɗauki domin kuɓutar da su daga hannun masu garkuwa da mutane. A cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, malamar ta bayyana cewa ta yi bidiyon ne domin sanar da halin da suke ciki tare da kira ga hukumomi da masu ruwa da tsaki su ɗauki matakan da suka dace domin ceto su da mayar da
Bayan samun 'yan sa'o'i na nishi, tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sake afkawa hannun jami'an tsaro na DSS, jim kaɗan bayan da kotu ta bayar da belinsa a kan kuɗi naira miliyan 100. Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ta gindaya tsauraran sharaɗan beli da suka haɗa da neman ma'aikacin gwamnati na matakin Level 17 mai gida a Maitama ko Asokoro da zai tsaya masa, to sai dai jami'an DSS ba su ba shi damar cin moriyar wannan beli ba. Wannan sabon kamun ya biyo bayan zargin El-Rufai da datsar wayar Mashawarcin Shugaban Ƙasa a kan Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, wa
Hukumar rundunar sojin Amurka a Afrika (AFRICOM) ta tabbatar da cewa dakarunsu da na Najeriya sun fito lafiya kalau daga wannan samame, ba tare da an samu asarar rai ko jikkata ba. To sai dai a daya bangaren, Hedikwatar Tsaron Najeriya ta nuna cewa 'yan ta'addan na ISIS da ISWAP sun dandana kudarsu, inda aka kashe sama da guda 20 daga ciki. Harin, wanda aka kai shi a sansanin 'yan ta'addan da ke garin Metele a Arewacin jihar Borno, ya biyo bayan kwararan bayanan sirri da jami'an tsaro suka tattara a kai-a-kai kan motsinsu. Daraktan Yada Labarai na Hedikwatar Tsaron, Manjo Janar Samaila Uba, ya
Mai magana da yawun rudunar sojin ta Najeriya Sama'ila Uba ya fitar a jiya Asabar, ya ce: "Mun samu nasarar kai wani tsararren hari da muka shirya ƙarƙashin shirinta na yaƙi da ta'adanci, wanda yayi sanadiyar kisan Abu-Bilal al-Minuki, wanda yana ɗaya daga cikin ƴan ta'addan da ake da su a duniya". Ta ce an samu nasarar harin ne da taimakon haɗin-gwiwa da tallafin haɗin-gwiwar Amurka wajen musayar bayyana shirri. "Tare da Amurka mun yi nasarar rusa gungun muggan ƴan ta'adda da ke barazana ga rayukan ƴan Najeriya, da sauran ƙasashen da ke Afirka ta yamma", inji sanarwan. Sai dai, rundunar sojin
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da karamar Ministar Ilimi ta kasa Suwaiba Sa’id Ahmed ta kai masa ziyara a gidan gwamnatin Kano. Gwamnan ya ce shirin AGILE ya zama wata babbar kafa ta inganta ilimi musamman ta fuskar gine-ginen makarantu da inganta malamai. Tun da farko a jawabin ta, karamar Ministar Ilimi Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmed, ta sanar da Gwamnan cewa jihar Kano ta samu amincewar bankin duniya kan gina sabbin makarantu 49 da za su lashe sama da naira biliyan 23, inda ta ce tuni aka baiwa ‘yan kwangila kudin fara aikin. Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Minista
Hukumar Dakile Yaɗuwar Cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta tsaurara sa ido kan cutar Ebola bayan sake ɓullar cutar a ƙasashen Kongo da Uganda. Hukumar ta bayyana cewa ta ɗauki matakan shiri domin hana shigowar cutar cikin Nijeriya, ciki har da ƙarfafa bincike a filayen jiragen sama da sauran mashigai na ƙasa. NCDC ta kuma buƙaci ‘yan ƙasa da su kiyaye tsafta, su riƙa wanke hannu akai-akai, tare da kai rahoton duk wani mutum da ke nuna alamun cutar domin dakile yaduwarta. Hukumar ta ce tana aiki tare da hukumomin lafiya na duniya domin tabbatar da an dakile duk wata barazanar yaɗuwar Ebola a ƙasar.
Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya buƙaci al’ummar Musulmi da su fara duba watan Zul-Hajji, wanda shi ne watan Sallah babba, daga gobe Lahadi 17 ga watan Mayun 2026 daidai da 29 ga Zulƙida 1447 Hijiriyya. Wata sanarwa da shugaban kwamitin bayar da shawara kan harkokin addinin musulunci na majalisar Sarkin Musulmi kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, ya fitar, ta buƙaci duk wanda ya ga wata ya sanar da hakimi ko uban ƙasa na kusa da shi don sanar da Majalisar Sarkin Musulmi.
Shugaban Rasha, Vladimir Putin, zai kai ziyara ƙasar China daga ranar 19 zuwa 20 ga watan Mayu, kwanaki kaɗan bayan ziyarar da shugaban Amurka Donald Trump ya kai Beijing. Fadar Kremlin ta bayyana cewa Putin zai gana da shugaban China, Xi Jinping, domin tattauna yadda za a ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da alaƙar dabarun siyasa da tattalin arziki tsakanin Moscow da Beijing. Sanarwar ta ce shugabannin biyu za su tattauna muhimman batutuwan duniya da na yankuna tare da sanya hannu kan wata sanarwar haɗin gwiwa bayan ganawarsu. Haka kuma ana sa ran Putin zai gana da firaministan China, Li Qiang, domin
The Kano State Hisbah Board has commended officials of the Kano Road Traffic Agency (KAROTA) for intercepting 349 cartons of alcoholic beverages at different locations across the state. While handing over the seized alcoholic drinks to the Hisbah Board, KAROTA, in a statement signed by Aminu Hassan Shehu, listed the various brands confiscated to include Brambaj, Ballamour, Mafia, Orijin Bitters, Derok, Action Bitters, and Palwine. A KAROTA official who provided further details explained that 27 cartons of the alcoholic beverages were intercepted along Enugu Road in Sabon Gari, within Fagge Loc
Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta kama wani mai suna Bala Yusuf dan karamar hukumar Dutse da ke jihar Jigawa da ake zargi da yinƙurin halaka wani direban mota tare da ƙoƙarin sace motar. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Bauchi, SP Nafiu Habib ne ya bayyana hakan, yana mai cewa wanda ake zargin ya umarci direban ya kai shi Jos daga Abuja, inda bayan isar su Jos, sai wanda ake zargin ya lallashi direban da nufin ya kai shi Bauchi domin ya ga iyala nshi. Sanarwar ta ce, bayan sun isa Bauchi, sai mutumin ya sanyawa direban kwayoyin saka bacci a abinci, inda yayi yunkurin gu
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai mummunan hari ƙauyen Lakwaya da ke ƙaramar hukumar Gwarzo a Jihar Kano, inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu da dama. Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai harin ne da yammacin ranar Alhamis, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, inda suka shiga ƙauyen a kan babura sama da 30 suna harbe-harbe kan mai uwa da wabi, lamarin da ya haddasa tashin hankali da firgici a tsakanin al’umma. Wata majiya daga masarautar yankin, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida cewa maharan sun kutsa yankin ne ta hanyar Gidan Biris, wani gari da ke kan iyakar jih
Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ya janye shirinsa na sayen ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal da ke buga gasar Firimiya ta Ingila, saboda yana buƙatar kuɗin domin kammala aikin matatar mai tasa da ta kai darajar dala biliyan 20 a Legas. Hamshaƙin attajirin ya bayyana hakan ne a wata hira ta podcast da Nicolai Tangen, Babban Daraktan Hukumar Zuba Jari ta Norges Bank Investment Management, wadda aka fitar a ranar Laraba ta shafin YouTube na hukuma na kamfanin. Dangote, wanda shi ne wanda ya kafa kuma Babban Daraktan Kamfanin Dangote Group, ya ce a lokacin da y
Ministan kudi, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da Najeriya ke aiwatarwa sun zama shaida ga kasashen Afirka cewa daukar matakai masu karfi da aiwatar da tsare-tsare yadda ya kamata na kawo ci gaba. Oyedele ya ce Najeriya ta nuna cewa lokaci ya yi da za a daina yawan maganganu kawai, a mayar da hankali wajen aiwatar da manufofin tattalin arziki domin samun ingantaccen ci gaba da habaka tattalin arzikin kasa. Ya kara da cewa sauye-sauyen da ake yi na taimakawa wajen karfafa tattalin arziki da kuma bude sabbin damammaki ga masu zuba jari da ‘yan kasuwa.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kare matakin da gwamnatinsa ta dauka na tallafawa matatar Dangote, yana mai cewa da ba a samu karfin tace mai a cikin gida ba, da Najeriya ta shiga cikin babbar matsala sakamakon rikice-rikicen da ke faruwa a duniya. Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin taron Africa CEO Forum karo na 13 da aka gudanar a kasar Rwanda. Shugaban kasar ya ce yawan al’ummar Najeriya da kuma dogaro da kayayyakin man fetur ya sa ya zama wajibi gwamnati ta mara baya ga ayyukan tace mai na cikin gida kamar matatar Dangote. “Duba da rikice-rikicen da ke faruwa a sassan duni
Najeriya da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari Ta Yuro Miliyan 365 Kasashen Najeriya da Jamus sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta yuro miliyan 365 domin bunkasa tattalin arziki, makamashi, noma da kuma ci gaban bangaren masu zaman kansu. Yarjejeniyar na da nufin karfafa zuba jari na dogon lokaci tare da inganta ci gaban tattalin arziki da samar da damammaki a fannoni daban-daban na kasar
A shekarar 2019, babban limamin Jami'ar Musulunci ta Al-Azhar a ƙasar Masar ya yi wani kalamin da ya yamutsa hazo, inda ya ce auren mace fiye da ɗaya "zai iya zama rashin adalci ga mata da yara". Sheikh Ahmed el-Tayeb, wanda mashahurin malamin Musulunci ne ya ce auren mace fiye da ɗaya, wanda abu ne da ya yawaita tsakanin Musulmai sanadiyyar halascinsa a addini, na faruwa ne sanadiyyar "rashin fahimtar ayoyin Qur'ani yadda ya kamata game da mas'alar." Malamin ya yi kalamin ne a wani shirin talabijin na mako-mako. To amma kalaman malamin sun tayar da ƙura, lamarin da ya kai ga har sai da hukumo