AMMASCO RADIO NEWSROOM

top stories

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta lalata jabun kayayyaki, magungunan da wa’adin su ya ƙare

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta lalata jabun kayayyaki, magungunan da wa’adin su ya ƙare da kuma marasa inganci da darajarsu ta haura naira biliyan 1.8 a birnin tarayya Abuja. An gudanar da aikin lalata kayayyakin ne a ƙaramar hukumar Kuje, inda aka ƙone magunguna, kayan abinci, kayan kwalliya, sinadarai, na’urorin lafiya da barasa da hukumar ta kwace daga hannun masu sayarwa da masu safararsu. Babbar Daraktar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana yaɗuwar jabun kayayyaki a matsayin barazana ga tsaron ƙasa. NAFDAC ta bayyana cewa masu jabun kaya sun ƙara a

Wani matashi mai suna Abdulmutallab Yusuf ya rasa ransa sakamakon zaɓen fid-da-gwani na jam’iyyar APC a Mazaɓar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna.

Wani matashi mai suna Abdulmutallab Yusuf ya rasa ransa, yayin da wasu mutum 12 suka jikkata bayan rikicin da ya ɓarke sakamakon zaɓen fid-da-gwani na jam’iyyar APC a Mazaɓar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna. Rahotanni sun nuna cewa Nasiru Idris ne ya lashe zaɓen bayan samun ƙuri’u 853, yayin da abokin takarar sa Bashir Zango ya samu ƙuri’u 213. Rahotanni sun ce rikicin ya fara tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu bayan kammala zaɓen, lamarin da ya rikide zuwa tashin hankali a wasu unguwannin yankin. Malam Yusuf Abdullahi, mahaifin mamacin, ya bayyana cewa yana gida lokacin da aka sanar da shi c

Wani hatsarin mota da ya afku a yankin Sabuwar Mil Uku da ke kan titin Gombe zuwa Yola ya yi sanadin mutuwar mutane biyu

Wani hatsarin mota da ya afku a yankin Sabuwar Mil Uku da ke kan titin Gombe zuwa Yola ya yi sanadin mutuwar mutane biyu, ciki har da wata jami’ar ’yan sanda, yayin da wasu da dama suka samu ji manyan raunuka. Lamarin ya faru a ranar Laraba lokacin da wata tirela ƙirar DAF mai ɗauke da buhunan hatsi ta kwacewa direban ta, inda ta kutsa cikin babura uku da masu tafiya a ƙasa tare da wasu shaguna da ke bakin hanya. Rahotannin farko daga jami’an tsaro sun nuna cewa direban motar ya yi ƙoƙarin kutsawa hanyar da ba ta dace ya shiga ba, sannan birkin motar ya gaza aiki, lamarin da ya haddasa hatsari

Rundunar yansandan jihar Kano ta ce ta samu nasarar kame fiye da mutane 200, da ake zargi da fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka, a faɗin jihar Kano.

Rundunar yansandan jihar Kano ta ce ta samu nasarar kame fiye da mutane 200, da ake zargi da fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka, a faɗin jihar Kano. Kwamishinan yansandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori, shine ya sanar da haka ya yi wani taron manema labarai da aka gudanar a shelkwatar rundunar. Haka kuma ya ce rundunar ta samu nasarar kuɓutar da mutane uku da akayi garkuwa da su, tare da kama mutum 5 daga cikin masu garkuwar. Rundunar tace ta samu wadannan nasarori ne a ayyuka na musamman da ta gudanar a watan Afrilun da ya gabata a sassa daban-daban.

Wasu yan bindiga sun yi fashin raguna 11 daga wasu yan kasuwar Karamar Hukumar Ajingi a Nan Kano

Wasu ‘yan bindiga sun yi fashin raguna 11 daga wasu ‘yan kasuwar Karamar Hukumar Ajingi a Nan Kano, yayin da suke hanyar su ta zuwa jihar Kogi domin cin kasuwar Babbar Sallah. Daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa, Alhaji Hamisu Abdu Sakalawa, ya shaida wa Arewa Updates, cewa lamarin ya faru ne cikin dare a garin Dakatsalle, a karamar hukumar Bebeji. Hamisu ya ce sun tsaya jiran motar da za ta dauke su zuwa garin Ankwa da ke Jihar Kogi, sai ga maharan sun zo a cikin mota ɗauke da bindigu. Yace ayan sun yi harbe-harbe a iska, sai su ka umarci su kwanta su rufe idanun su, daga nan suka kwashe

Hukumar NDLEA Ta Kame Ƙwayoyi Naira Biliyan 480, Tare da Kama ’Yan Asalin Mexico

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta sake gano wani gagarumin kamu na ƙwayoyi da darajarsu ta kai naira biliyan 480, tare da kama wasu ƴan asalin ƙasar Mexico da hannu a cikin wannan sana’ar. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ya fitar a larabaci, an bayyana cewa NDLEA ta tarwatsa wata gungiyar masu safarar ƙwayoyi tsakanin Najeriya da Mexico. Hukumar ta ce ta gano wani haramtaccen kamfani na sarrafa ƙwayoyi, wanda ta bayyana a matsayin mafi girma da ta taɓa ganowa, a yankin Ijebu na jihar Ogun. Baya ga gano kamfanin, NDLEA ta kama jagoran gungiy

Mikel Arteta na shirin sabunta sabon kwantiragin sa a 𝐀𝐑𝐒𝐄𝐍𝐀𝐋

Mikel Arteta na shirin sabunta sabon kwantiragin sa a 𝐀𝐑𝐒𝐄𝐍𝐀𝐋 a wannan bazarar, shirin kulob ɗin ya tabbata. An tabbatar da karin albashi da cikakken amincewa daga kulob ɗin, inda Arsenal ta riga ta miƙa masa sabon kwantiragi watanni kaɗan da suka gabata kuma ana shirin kammala komai nan ba da jimawa ba. Arteta ya fi mayar da hankali wajen kammala kakar wasa, amma babu wani sauyi: tattaunawar za ta ci gaba sosai a wannan bazarar. Kwana 𝟓𝟑𝟕𝟔 bayan zuwansa, kofin Premier League

Gwamna Sim Fubara ya janye daga neman tikitin takarar Gwamnan jihar Rivers a jam'iyyar APC

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya janye daga takarar neman tikitin tazarcen kujerar Gwamna da yake a kai a APC wanda aka shirya gudanarwa ranar Alhamis. A cikin wata sanarwa mai taken “My Decision to Withdraw from the Rivers State Gubernatorial Primaries”,da jaridar Daily Trust ta gani, wadda ya sanya wa hannu da kansa a daren Laraba, Fubara ya bayyana cewa zai mara wa duk wanda ya fito a matsayin dan takarar jam’iyyar APC baya.

Mutum Huɗu Sun Mutu Bayan Motar Golf Ta Nitse A Madatsar Ruwan Tomas Da Ke Danbatta

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da aukuwar wani mummunan hatsarin mota da ya raba mutane hudu da rayukansu, bayan da wata mota kirar Golf Wagon ta fita hanyar ta fada cikin madatsar ruwan Tomas (Tomas Dam) da ke karamar hukumar Danbatta. Yadda Al'amarin Ya Faru Kiran Gaggawa: A ranar Talata, 19 ga watan Mayu, 2026, da misalin karfe 7:10 na yamma, jami'an hukumar na shiyyar Danbatta sun sami kiran gaggawa daga wani mazaunin yankin mai suna Suleman. Hanyar Da Motar Ke Bi: Motar, wacce ba a tantance lambar ta ba, ta taso ne daga birnin Kano ta dosa garin Roni da ke Jihar Jigawa, da

kamfanin Ammasco ya shirya taron bayar da horo ga shugabannin makanikai daga sassa daban-daban na ƙasar nan, domin ƙara musu ilimi kan sabbin dabaru amfani da injina.

A rana ta biyu da Kamfanin samar da baƙin mai na Ammasco, ya shirya taron bayar da horo ga shugabannin makanikai daga sassa daban-daban na ƙasar nan, domin ƙara musu ilimi kan sabbin dabaru amfani da injina. A yau ƙungiyar matuka babura masu ƙada Uku da dangogin su ne aka baiwa horo domin sanin hanyoyin amfani da fasahar CNG. Taron wanda ya gudana da ya haɗa ƙwararru a fannin baƙin mai da kula da injinan ababen hawa, ya baiwa mahalarta damar sanin sabbin hanyoyi da dabarun da za su taimaka wajen inganta ayyukansu Da yake jawabi a wajen taron, manajan darakta na rukunin kamfanonin Ammasco, Alha

Matasa Biyu Dauke da Bindigogi Sun Bude Wuta a Babban Masallacin San Diego, Amurka

Wasu matasa biyu dauke da bindigogi sun kai hari a babban masallacin da ke gundumar San Diego, Jihar California, Amurka. Rahotanni sun ce maharan sun harbe wani jami'in tsaron masallaci da wasu mutane biyu har lahira a Cibiyar Musulunci ta San Diego a ranar Litinin. Limamin masallacin ya yi baƙin ciki Limamin masallacin kuma daraktan Cibiyar Musulunci, Taha Hassane, ya ce, "Ba mu taɓa fuskantar bala'i irin wannan ba a baya. Wannan abin takaici ne ƙwarai a kai hari kan wurin ibada." Daruruwan jami'an tsaro da aka kira zuwa wurin sun iske gawarwakin maza uku da ke da alaƙa da masallacin. Jami'ai

Pantami ya janye daga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC na gwamna a jihar Gombe, sakamakon zargin take dokokin zaɓe.

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani na Nijeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya janye takararsa daga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC domin neman kujerar gwamnan Jihar Gombe. Ya bayyana hakan a wata sanarwa da lauyansa, Barista Ibrahim M. Attahir, ya fitar ranar Talata. Pantami ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki da kuma nazarin abubuwan da suka faru game da zaɓen. Ya danganta janyewar da zargin take Dokar Zaɓe ta 2026 da rashin gaskiya a tsarin zaɓen cikin gida na jam’iyyar. Ya kara da cewa duk da ya bi dukkan ka’idojin APC kuma ya amsa kiran mata

Tsohon minista Sa'idu Ahmed Alkali ya janye daga takarar fidda gwani a jihar Gombe

Tsohon ministan sufuri kuma ɗan takarar gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar APC, Sa'idu Ahmed Alkali, ya sanar da janye kansa daga shiga zaɓen fidda gwani na gwamna da jam’iyyar za ta gudanar ranar 21 ga watan Mayun 2026. A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Umar Alkali Jibrin ya fitar, Sanata Alƙali ya ce ya ɗauki matakin ne saboda abin da ya kira rashin gaskiya da karya dokokin zaɓe a jihar. Sanarwar ta bayyana cewa Alƙali ya cika dukkan sharuɗɗan shiga takarar gwamna, ciki har da sayen fom ɗin nuna sha’awa da na tsayawa takara tare da wuce tantancewar da jam’iyyar

Tsohon ministan tsaro, Theophilus Danjuma, ya bayar da gudunmawar Naira biliyan 3 yayin ƙaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban ƙasa

Tsohon ministan tsaro, Theophilus Danjuma, ya bayar da gudunmawar Naira biliyan 3 yayin ƙaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban ƙasa, Yakubu Gowon mai suna “My Life of Duty and Allegiance” da aka gudanar a Abuja ranar Talata. Haka kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya sayi kwafi 25 na littafin kan Naira miliyan 500 ta hannun wakilinsa, Mansur Ahmed. Shugaban BUA Group, Abdul Samad Rabiu, shi ma ya sayi kwafi na littafin da kudinsu ya kai naira miliyan 25. Rahotanni sun bayyana cewa Danjuma ya kuma umarci a saya tare da rabawa dakunan karatu na jami’o’i 20 da suka bai

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jinjinawa shugaban Amurka Donald Trump dangane da goyan bayan da ya ke bai wa ƙasar,

Sanarwar haɗin gwuiwar tsakanin sojin Najeriya da kuma rundunar sojin Amurka dake Afirka ta ce, al-Minuki da aka kashe ne ke taimakawa wajen harkokin kafofin yaɗa labaran ƴan ta’addan da kuma kuɗaɗen da ake amfani da su wajen samar da makamai tare da jirage marasa matuƙa. Kwamandan rundunar Amurkar Janar Dagvin Anderson ya tabbatar da wannan nasarar lokacin da yake yiwa majalisar dokokin Amurka bayani dangane da aikin da suke yi na haɗin gwuiwa, inda ya kuma bayyana irin taimakon da suke samu daga sojojin Najeriya wajen gabatar musu da bayanan asiri da kuma taimaka musu wajen aikin. Shugaban N

Dakarun Soji Sun Tarwatsa Shirin Mayakan Ta'addanci a Arewa Maso Gabas

Yayin da suke tsaka da gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro, dakarun hadin gwiwa na "Operation Hadin Kai" sun yi nasarar fatattakar wasu 'yan bindiga da suka yi yunkurin kaddamar da gagarumin hari a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan. Baya ga dakile harin, sojojin sun kuma kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su, tare da damke wasu mutane da ake zargi da bai wa 'yan ta'addan bayanai da kayan aiki. Yadda Aka Fafata a Sansanin Gajibo Shirin Makirci: Rahotanni sun nuna cewa dakarun da ke sansanin FOB Gajibo ne suka fuskanci barazanar, inda ake zargin mayakan Boko Haram da ISWAP ne suka taho

Dan Sanda Ya Rasa Ransa Gab da Ritaya a Kano Sakamakon Fadan Daba.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta fuskanci babban rashi na wani gogaggen jami'inta mai suna Sani S.O, wanda ya rasa ransa sakamakon rikicin daban da ya ɓarke a yankin Hotoro. Abin bakin ciki shi ne, jami'in ya rayu ne da sauran 'yan makonni kalilan ya ije aikin sarki domin ya tafi ritaya. Yadda Lamarin Ya Faru Kiran Gaggawa: An tura marigayin ne tare da tawagarsa domin su kwantar da tarzoma tare da raba wani fada da ya barke tsakanin gungun matasan banza. Harbin Bindiga: Yayin kokarin dawo da doka da oda, wani daga cikin 'yan daban ya harbe shi da makami. Rasa Rai: Ko da aka garzaya da shi ba

Gwamnatin jihar Kwara ta buƙaci masu ruwa da tsaki a ɓangaren lafiya da su haɗa kai wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya a faɗin jihar.

Gwamnatin jihar Kwara ta buƙaci masu ruwa da tsaki a ɓangaren lafiya da su haɗa kai wajen samar da ingantaccen tsarin aiwatar da kiwon lafiya na zamani domin inganta ayyukan lafiya a faɗin jihar. Kiran ya fito ne yayin buɗe wani taron kwana uku da aka gudanar a birnin Ilorin kan samar da tsarin aiwatar da shirin lafiya na zamani da ya dace da bukatun jihar Kwara. Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta jihar, Dakta Taoheed Abdullahi, wanda ya wakilci Kwamishiniyar Lafiya, Amina El-Imam, ya ce taron na da nufin mayar da manufofin lafiya na ƙasa zuwa ayyuka na zahiri da za su dace da halin da ake

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya lashe takarar Sanatan Gombe ta Arewa a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC

Jam’iyyar APC ta bayyana gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, a matsayin dan takarar Sanatan Gombe ta Arewa bayan samun kuri’u masu rinjaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a jihar. ‎Shugaban kwamitin zaben fidda gwani na APC a jihar, Mallam Labiru Musa Kafur, ya ce an gudanar da zaben cikin lumana da gaskiya a dukkan kananan hukumomi 11 na jihar. ‎Haka kuma, tsohon mataimakin kwamishinan ’yan sanda, Mohammed Ahmed, ya zama dan takarar APC na Sanatan Gombe ta Tsakiya. ‎Kwamitin ya tabbatar da cewa duk wadanda suka yi nasara sun cika sharuddan kundin tsarin mulki da na ja