AMMASCO RADIO NEWSROOM

top stories

NNPC ta zargi matatar Dangote da neman mamaye kasuwar man Nijeriya

Kamfanin mai na Nijeriya, NNPC, ya zargi matatar mai ta Dangote da yunƙurin mamaye kasuwar man fetur ta ƙasar ta hanyar ƙalubalantar lasisin shigo da mai da aka bai wa wasu kamfanonin da ke gogayya da ita, kamar yadda takardun kotu da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani suka nuna. A cikin bayanan kariya da ya gabatar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas, NNPC ya ce idan har aka amince da buƙatar Dangote na soke ko rage yawan lasisin shigo da mai, hakan na iya haddasa matsala wajen samar da mai, da rashin daidaiton farashi, tare da barazana ga tsaron makamashin Nijeriya. Hukumar K

Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye, ya kori Firaminista Ousmane Sonko

Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya kori Firaminista Ousmane Sonko daga muƙaminsa a wani mataki da ya jawo cece-kuce a fagen siyasar ƙasar. Rahotanni sun bayyana cewa matakin korar ya biyo bayan zazzafar muhawara da aka yi a majalisar dokokin Senegal, inda Firaminista Sonko ya fito fili ya soki salon mulkin shugaban ƙasar. Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin rikice-rikicen siyasa a ƙasar, inda masu sa ido ke ganin cewa zai iya ƙara haifar da saɓani a tsakanin manyan jami’an gwamnatin Senegal

Ambasada Yusuf Maitama Tuggar bai samu tikitin takarar gwamnan jihar Bauchi ba.

Yusuf Tuggar bai samu tikitin takarar gwamnan jihar Bauchi ba. Ambasada Yusuf Maitama Tuggar bai samu tikitin takarar gwamnan jihar Bauchi ba, a jam’iyyar APC. Hakan ya biyo bayan kai ruwa rana tsakanin masu ruwa da tsaki na jihar, kafin daga ƙarshe su tabbatar da tsohon gwamnan Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar a matsayin ɗan takarar gwamnan Bauchi na Jam'iyyar APC, a zaɓen 2027.

Farfesa Usman Yusuf ya shigar da kara gaban DSS kan Kwankwaso bisa zaegin yi masa barazana

A cikin takardar ƙorafin mai ɗauke da kwanan watan 22 ga Mayu, 2026, Farfesa Usman Yusuf ya ce kalaman sun biyo bayan sharhin da ya yi kan haɗakar siyasa da kuma batutuwan siyasar yankuna. Ya bayyana cewa ko da yake Sanata Kwankwaso bai ambaci sunansa kai tsaye ba, amma bayanin da ya yi ya isa ya sa masu sauraro gane wanda ake nufi. Farfesa Yusuf ya kuma yi zargin cewa Sanatan ya bukaci magoya bayan Kwankwasiyya da wasu ƙungiyoyin matasa su “tarwatsa” wanda ake magana a kansa da kalmar Hausa ta “fata-fata,” lamarin da ya ce na iya jawo tsoratarwa ko tashin hankali.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato ta cafke wasu mutane shida bisa zargin satar shanu

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Filato ta cafke wasu mutane shida bisa zargin satar shanu, hada baki wajen aikata laifi da kuma mallakar bindigu ba bisa ka’ida ba. Arewa Updates ta rawaito cewa, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Bassey Ewah ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da sashen yaki da manyan laifuka na VCRU a Jos. Ya ce an cafke daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Yahuza Sale bayan wani bidiyo da ya wallafa a Facebook wanda ake zargin yana tayar da hankalin jama’a. Sanarwar ta ce Yahuza ya amsa cewa yana hada baki da wani Victor Danladi wanda aka fi sani da Boka wajen satar shanu ta am

Osimhen ya kai ziyara tsohuwar makarantar firamare da ya yi karatu

Osimhen ya kai ziyara tsohuwar makarantar firamare da ya yi karatu, ya kuma bai wa mai gadi kyautar Naira miliyan 20. “Shi ne mai gadin makarantar lokacin da nake karatu a nan. Yakan siya min biskit da ice cream lokacin muna yara ƙanana. Wasu lokutan nakan zo makaranta ban ci komai ba, sai ya ɗauki abincinsa ya ba ni. Ga sauran ɗalibai shi mai gadi ne kawai, amma a wurina tamkar uba yake gare ni. Ba zan taɓa mantawa da shi ba.”

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke wasu sassan jadawalin zaben 2027 da Hukumar INEC ta fitar

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke wasu sassan jadawalin zaben 2027 da Hukumar INEC ta fitar, bayan wata kara da jam'iyyar YP ta shigar. Mai shari'a Mohammed Umar ya ce wasu wa'adin da INEC ta kayyade wa jam'iyyun siyasa sun saba wa Dokar Zabe ta 2026, musamman batun lokacin gudanar da zaben fidda gwani, gabatar da sunayen 'yan takara, janye takara da maye gurbin 'yan takara. Kotun ta bayyana cewa INEC ba ta da ikon rage ko sauya wa'adin da doka ta tanada, tare da cewa ba za ta iya kayyade karshen yakin neman zabe ko fitar da jerin 'yan takara ta hanyar da ta saba wa doka ba

Majalisar Dinkin Duniya: ‘Yan Najeriya miliyan 35 na fuskantar barazanar matsananciyar yunwa a watanni masu zuwa

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa kusan mutane miliyan 35 a Najeriya na cikin hadarin fama da matsananciyar yunwa daga watan Yuni zuwa Agusta na wannan shekara. Kungiyar kula da harkokin jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana hakan a birnin New York na kasar Amurka, inda ta ce Najeriya na fuskantar karin matsalar karancin abinci yayin da lokacin fari da wahalar samun abinci ke kara matsowa. A cewar rahoton, kusan mutum daya cikin mutane bakwai a Najeriya na iya fuskantar matsananciyar rashin wadataccen abinci a watanni masu zuwa. Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa Najeriya ya

Sace Dalibai a Oyo: Wadanda ake zargi da ta’addanci sun fara tattaunawa, sun gindaya sharadi

Mutanen da ake zargi da kai harin sace dalibai da malamai a makarantu uku da ke garuruwan Esinele, Yamota da Alawusa a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo sun bude hanyar tattaunawa da gwamnatin jihar. Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa masu garkuwar sun ki yin magana da iyalan wadanda aka sace, inda suka ce suna son tattaunawa kai tsaye da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, kuma wannan ne sharadin da suka bayar. Wata majiya ta ce har yanzu ba a bayyana cikakken bayanin tattaunawar ko bukatun masu garkuwar ba domin kare rayukan wadanda ke hannunsu. Har yanzu ba a tabbatar ko gwamnan ne da kans

Pep Guardiola zai bar Manchester City a ƙarshen kakar wasa

Pep Guardiola ya tabbatar da cewa zai bar Manchester City a ƙarshen kakar wasa, inda hakan zai kawo ƙarshen shekaru goma masu cike da nasarori da kofuna. Ku gano irin tasirin da Guardiola ya yi a Manchester City.

Mataimakin gwamnan jihar Lagos, Obafemi Hamzat, ya lashe zaɓen fidda gwani na APC

Mataimakin gwamnan jihar Lagos, Obafemi Hamzat, ya lashe zaɓen fidda gwani na APC domin takarar gwamna a 2027 bayan samun ƙuri’u 657,917 cikin 657,974 da aka kaɗa. Abokin takararsa Lanre Jim-Kamal ya samu ƙuri’a ɗaya kacal. Shugaban kwamitin zaɓen, Janar Jon Temlong mai ritaya, ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana a sakatariyar APC da ke Ikeja. Hamzat ya gode wa Shugaba Tinubu, Gwamna Sanwo-Olu da shugabannin APC bisa goyon baya, sannan ya gabatar da tsarinsa na “My Lagos Dream” wanda ya mayar da hankali kan ayyukan yi, ababen more rayuwa, ilimi, lafiya da tsaro.

Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da fara biyan albashin watan Mayu ga dukkan ma'aikatan gwamnati kafin bikin Eid al-Kabir

Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da fara biyan albashin watan Mayu ga dukkan ma'aikatan gwamnati kafin bikin Eid al-Kabir domin ba su damar yin shirye-shiryen Sallah cikin sauki. A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Yada Labarai da Al'adu ta jihar ta fitar, Kwamishinan Yada Labarai da Al'adu, Alhaji Mahmud Muhammad Dantawasa, ya ce matakin ya nuna kudirin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na kula da walwalar ma'aikata da iyalansu. Gwamnatin ta bayyana cewa biyan albashin da wuri zai taimaka wajen rage wa ma'aikata matsin tattalin arziki da ke tattare da lokutan bukukuwa, musamman a wannan lokaci da

Masarautar Zazzau ta dakatar da shugaban ƙauyen Matarawa bisa zargin damfara da cin zarafin al’umma a harkokin rabon gado.

Masarautar Zazzau ta dakatar da shugaban ƙauyen Matarawa bisa zargin damfara da cin zarafin al’umma a harkokin rabon gado. A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ya fitar, Sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, ya gargaɗi hakimai da shugabannin ƙauyuka da su guji cutar da jama’a musamman a harkokin rabon gado. Sanarwar ta ce Sarkin ya umarci hakimai da su sanya ido sosai kan yadda shugabannin ƙauyuka ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum da al’umma. Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa bayan kammala dawo da kuɗaɗen da aka ka

Gwamnan kano Abba Kabir yusuf ya kafa kwamitin mutum 13 domin shirya gagarumin bikin cikarsa shekara uku akan mulki

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ne zai jagoranci kwamitin a matsayin shugaba. Sauran mambobin kwamitin sun hada da: Engr. Marwan Ahmad – Kwamishinan Ayyuka Dr. Abubakar Labaran Yusuf – Kwamishinan Lafiya Dr. Dahir Muhammad Hashim – Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi Dr. Danjuma Mahmoud – Kwamishinan Noma da Albarkatun Kasa Dr. Gwani Ali Haruna Abubakar Makoda – Kwamishinan Ilimi Hon. Abduljabbar Umar Garko – Kwamishinan Kasa da Tsare-tsaren Hon. Abdulkadir

Gwamnatin Jihar Jigawa ta samar da kwale-kwalen gudu guda 20 domin ƙarfafa ayyukan kwashe mutane da bayar da agajin gaggawa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta samar da kwale-kwalen gudu guda 20 domin ƙarfafa ayyukan kwashe mutane da bayar da agajin gaggawa a yankunan da ambaliya ke yawan shafa a jihar. Mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara na musamman kan muhalli, Hamza Muhammad, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a Dutse. Ya ce matakin zai tabbatar da saurin kwashe mutanen da ambaliya ta rutsa da su a al’ummomin da ke fama da ambaliya.

Ministan Tsaro Janar Christopher Musa ya bayyana cewa ayyukan ta’addanci na daga cikin manyan barazanar da ke addabar ƙasar nan.

Ministan Tsaro Janar Christopher Musa ya bayyana cewa ayyukan ta’addanci na daga cikin manyan barazanar da ke addabar ƙasar nan. Da yake jawabi a Abuja yayin ƙaddamar da wani littafi mai taken ayyukan yaki da Ta’addanci da tada Ƙayar Baya a Arewa maso Gabas, Wanda tsohon Kwamandan Rundunar Haɗin Gwiwa ta MNJTF kuma tsohon Shugaban Kwalejin horas da sojoji Manjo Janar Ibrahim Yusuf mai ritaya ya rubuta. Christoper Musa ya jaddada cewa nasarar kawar da ta’addanci na buƙatar haɗin kai da jajircewar rundunar soji, hukumomin gwamnati da kuma al’umma baki ɗaya. Ya yi kira da a ƙara ƙarfafa haɗin gw

Rundunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da nasarar kama waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban harsu 248 a cikin wata guda.

Rundunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da nasarar kama waɗanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban harsu 248 a cikin wata guda, waɗanda suka kunshi ƴan fashi da makami da masu garkuwa da mutane da masu safarar miyagun kwayoyi da ƴan daba da dai sauransu. Kwamishinan ƴansandan jihar CP Ibrahim Adamu Bakori ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke gabatar da waɗanda ake a shalkwatar rundunar dake Kano. Ya ce a lokacin wannan aiki da suka gudanar daga 20 ga watan Afrilu zuwa 20 ga Mayu, sun samu nasarar kama ƴan fashi da makani 18 da masu garkuwa da mutane 5 da masu safarar miyagun kwayoyi 32

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya musanta rahotannin da ke cewa yana shirin sauya sunan Najeriya tare da soke Shari’ar Musulunci a Arewacin kasar nan.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya musanta rahotannin da ke cewa yana shirin sauya sunan Najeriya tare da soke Shari’ar Musulunci a Arewacin kasar nan. wannan na cikin sanarwar da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga ya fitar. Sanarwar ta ce babu gaskiya a rahotannin da ke yawo cewa Tinubu na shirin gabatar da kudirin gyaran kundin tsarin mulki domin sauya sunan kasar nan zuwa United States of Nigeria. Ya ce wasu ‘yan siyasa ne ke yada rahotannin karya domin haddasa rikici da tayar da hankalin jama’a gabanin babban zaben 2027. Fadar shugaban kasa ta kuma bukaci ‘y

NAHCON ta kammala jigilar Mahajjatan Nijeriya zuwa Saudiyya

NAHCON ta kammala jigilar Mahajjatan Nijeriya zuwa Saudiyya Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON ta sanar da kammala jigilar Mahajjatan 2026 zuwa ƙasar Saudiyya. Hukumar ta ce an kammala jigilar ne bayan jirgin ƙarshe na kamfanin Max Air da ya tashi daga filin jirgin saman Gusau ɗauke da Mahajjatan jihar Zamfara. Jaridar Daily Trust ta ruwaito NAHCON ta bayyana cewa an kammala tashin jiragi na 98 cikin kwanaki 18, inda Nijeriya ta samu guraben maniyyata 50,000 a Hajjin bana

Mayaƙan Boko Haram sun kashe matsunta da masu sarar itatuwa 33 a wasu hare-hare biyu da suka ƙaddamar a jihar Borno.

Wasu majiyoyi biyu ne suka tabbatar da afkuwar harin ga kamfanin dillancin labaran Faransa, a cewar wasu masu yaƙi da ayyukan mayaƙan da kuma jami’in ƙungiyar masunta da ke yankin sun ce tun a ranar litinin ɗin da ta gabata mayaƙan suka kai hari a yankin Mafa inda suka kashe masunta 27, sai kuma a yankin Dikwa da suka kashe masu sarar itatuwa shida. Shugaban ƙungiyar masu kamun kifin na Maidugurin Abdullahi Sani ya ce matsuntan na kan hanyar su ta dawowa daga aiki lokacin da maharan suka afka musu. Gabanin nan, mayaƙan Boko Haram sun harɓe masu sarar itatuwa shida lokacin da suke karɓar itace