AMMASCO RADIO NEWSROOM

top stories

Alhaji Aminu Ado Bayero ya shirya gudanar da taron addu’a domin neman zaman lafiya da ci gaban Kano da Arewaci da ƙasa bakiɗaya.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya shirya gudanar da taron addu’a domin neman zaman lafiya da ci gaban Kano da Arewaci da ƙasa bakiɗaya. Sanarwar na cikin takardar gayyata da sakataren Sarkin, Malam Abdullahi Haruna Kwaru ya sanya wa hannu. Takardar ta ce za a gudanar da taron addu’ar ne a ranar Litinin 25 ga watan Mayu, 2026 da ƙarfe 10:00 na safe a fadar Sarkin da ke gidan Nassarawa. Ya ce, za a yi addu’ar ne domin samun ingantaccen zaman lafiya da karuwar arziki a Kano da jihohin Arewa tare da roƙon Allah Ya ba da ikon yin zaɓen 2027 lafiya.

Sojojin Najeriya sun yi nasarar ceto aƙalla mutane 92 daga hannun mayaƙan Boko Haram

Sojojin Najeriya sun yi nasarar ceto aƙalla mutane 92 daga hannun mayaƙan Boko Haram, tare da kwance wasu nakiyoyi da ƴan ta’addan suka dasa a kan hanyar Buratai zuwa Kamuya da ke ƙaramar hukumar Biu. Sanarwar da kakakin rundunar musamman ta ‘Operation Haɗin Kai’ Laftanat Kanal Sani Uba ya fitar, ta ce mutanen da dakarun Najeriyar suka ceto sun haɗa da maza 52, da mata 33 da kuma ƙanan yara 7. Dakarun Najeriyar, sun gano gungun ƴan ta’addan ne a lokacin da suke kora mutanen da suka sace tare da ababen hawansu zuwa cikin daji, bayan da suka gano ana biye da su ne kuma suka dasa nakiyoyi guda uk

Najeriya ta ci gaba da riƙe kambunta na ƙasa ta uku da tafi kowace kasa karɓan bashi daga Hukumar Bunƙasa Ƙasa da Ƙasa

Najeriya ta ci gaba da riƙe kambunta na ƙasa ta uku da tafi kowace kasa karɓan bashi daga Hukumar Bunƙasa Ƙasa da Ƙasa (IDA), reshen Bankin Duniya da ke bayar da rance mai sauƙin biya a duniya, duk da an biya wasu, akwai kudaden da suka rage mata a zangon farko na shekarar 2026. A cewar bayanan kuɗi na IDA na watan Maris na Shekarar 2026, kudin da hukumar ke bin Najeriya ya kai dala biliyan 18.5 zuwa ranar 31 ga Maris, 2026, wanda ya ɗan ragu kadan daga dala biliyan 18.7 da aka samu a ƙarshen watan Disamba 2025. Raguwar dala miliyan 200n na nufin an samu ragin kaso 1.1 cikin ɗari a cikin watan

Gwamnatin tarayya ta nuna damuwa kan lalata layin dogo a jihohin Filato da Bauchi.

Gwamnatin tarayya ta nuna damuwa kan ci gaba da lalata layin dogo a wasu sassan ƙasar nan musamman a jihohin Filato da Bauchi. Shugaban Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya, Dakta Kayode Opeifa ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar a birnin Legas. Sanarwar ta ce an samu sabbin hare-haren lalata layin dogo a jihohin Filato da Bauchi, lamarin da gwamnatin ta bayyana a matsayin barazana ga tsaro da ci gaban ƙasa. Sanarwar ta ce irin waɗannan ayyuka na iya jawo hatsarin jirgin ƙasa, rasa rayuka da kuma lalata dukiyar gwamnati da aka kashe biliyoyin Naira wajen ginawa.

Gwamnatin Jihar Kano ta kama wasu jabun magunguna da kuɗinsu ya haura Naira miliyan 200.

Wannan na cikin sanarwar da Amir Abdullahi Kima, mamba a Kwamitin Kar-takwa na Yaƙi da Fatauci da Safarar Miyagun Kwayoyi, Muggan Makamai da Ƙananan Yara da Gwamnatin Kano ta kafa ya fitar. Sanarwar ta ce jami’an Civil Defence, NDLEA, ’yan sanda da Immigration ne suka haɗa hannu wajen gudanar da samamen ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamitin, Major A. A. Usman mai ritaya. Yayin sumamen an gano jabun magungunan a cikin wani kango inda ake adana su cikin matsanancin zafi ba tare da kulawa mai kyau ba, sannan ba su da sahalewar Hukumar NAFDAC.

Atiku Abubakar, ya jaddada cewa jam’iyyar ADC na bukatar fitar da dan takara mai kwarewa, gogewa da karfin tasiri a fadin kasa domin fuskantar zaben 2027

Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Lahadi. Ya ce zaben shekarar 2027 ba zai kasance na kalamai ko siyasar ra’ayi kawai ba, illa yana bukatar shugabanci mai kwarewa da zai iya tunkarar matsalolin tattalin arziki da tsaro da ke addabar Najeriya.

Wakilan AES sun halarci bikin rantsar da shugaban Benin

An rantsar da Romuald Wadagni a matsayin sabon shugaban Jamhuriyar Benin a wannan Lahadi, bayan nasararsa a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar ranar 12 ga watan Afrilu. Tsohon ministan kuɗin ƙarƙashin gwamnatin Patrice Talon ya yi rantsuwar kama aiki ne a gaban Kotun Tsarin Mulki, tare da halartar wakilan ƙasashe sama da 15, ciki har da ƙaramar ministar Faransa mai kula da hulɗa da ƙasashen waje. Abin da ya ja hankali a bikin shi ne halartar wakilai daga ƙasashen ƙungiyar AES — Burkina Faso da Mali da Niger — duk da rashin jituwar siyasa da aka dade ana samu tsakaninsu da gwamnatin Benin. A ja

Jami’an tsaro sun gaggauta martani bayan harbe-harbe kusa da White House

Jami’an tsaro na sirri a Amurka sun tabbatar da mutuwar wani ɗan bindiga da ake zargi ya buɗe wuta kusa da fadar gwamnatin ƙasar, White House, bayan musayar wuta da jami’an tsaro. Rahotanni sun ce mutumin ya isa wani wurin binciken ababen hawa da ke kusa da fadar kafin ya fara harbi kan jami’an tsaron da ke bakin aiki. Nan take jami’an tsaron suka mayar da martani, lamarin da ya jikkata wanda ake zargin da kuma wani mutum da ke kusa da wurin. Daga bisani an kai wanda ake zargin asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsa. Lokacin da harin ya faru, shugaban Amurka, Donald Trump, na cikin fadar Whit

Trump ya ce an kusa cimma matsaya kan kawo ƙarshen yaƙin Iran

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce an cimma matsaya kan yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin da ke tsakanin ƙasarsa da Iran. A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da shugabannin wasu ƙasashen Larabawa da kuma Firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu. Ya ce daga cikin abubuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa akwai batun sake buɗe mashigar Hormuz, wacce ke da muhimmanci wajen jigilar mai a duniya. Trump ya ƙara da cewa yanzu haka ana tattauna mataki na ƙarshe kafin a sanar da cikakken abin da aka cimma. Sai dai kafar yaɗa

Kungiyoyi za su fafata a ranar ƙarshe ta Premier ta Ingila

A yau ne za a kawo ƙarshen Gasar Firimiya ta Ingila ta bana, ɗaya daga cikin gasannin ƙwallon ƙafa mafi jan hankali a duniya. Tuni dai Arsenal FC ta lashe kofin gasar bayan shafe shekaru 22 tana jiran samun nasarar. Abin da ya fi ɗaukar hankali a wasannin ranar ƙarshe shi ne yadda za a tantance ƙungiyar da za ta faɗi daga gasar, inda ɗaya daga cikin Tottenham Hotspur FC ko West Ham United za ta koma Gasar Championship mai mataki na biyu a Ingila. Duka ƙungiyoyin biyu na Landan sun taɓa lashe kofunan Turai cikin ƴan shekarun nan, inda West Ham ta lashe Europa Conference League a 2023, yayin da

Aƙalla mutum 20 sun mutu bayan harin jirgin ƙasa a Pakistan

Aƙalla mutum 20 ne suka mutu a wani hari da aka kai wa jirgin ƙasa ɗauke da jami’an soji a birnin Quetta da ke kudu maso yammacin Pakistan, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Sai dai wasu majiyoyi na cewa adadin waɗanda suka rasa rayukansu ya fi haka, yayin da mutane da dama suka samu munanan raunuka. Fashewar ta haddasa gobara a wasu daga cikin taragaggin jirgin, tare da lalata gidaje da motoci da ke kusa da wurin. Jami’ai sun ce an dasa abin fashewar ne a cikin wata ƙaramar mota da aka ajiye kusa da layin dogo kafin ta tashi. Rahotanni sun ce da dama daga cikin fasinjojin jirgin na kan hany

Yadda mutane suka fito zaben fidda gwani na Shugaban kasa a APC alamace ta amincewa da tsarin Dimukradiya - Murtala Sule Garo

Mataimakin gwamnan Kano ya ce yawan fitowar jama’a a zaɓen fidda gwani na APC alama ce ta yadda ’yan Najeriya suka sake amincewa da dimokuraɗiyya Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Murtala Garo, ya bayyana cewa yawan jama’ar da suka fito domin kaɗa ƙuri’a a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC ya nuna yadda ’yan Najeriya suka sake nuna amincewa da tsarin dimokuraɗiyya

Tinubu ya samu jimmillar kuri'u 915,840 na zaben fidda gwani a jihohin Kano da Borno

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu jimillar ƙuri’u 915,840 a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da aka gudanar a jihohin Kano da Borno gabanin babban zaɓen shekarar 2027. A Jihar Kano, Tinubu ya samu ƙuri’u 500,852 inda ya kayar da abokin takararsa guda ɗaya, Mista Osifo Osayamen Stanley, wanda ya samu ƙuri’u 2,675 a zaɓen da aka gudanar a ƙananan hukumomi 44 na jihar. An sanar da sakamakon a hukumance ranar Asabar yayin tattara sakamakon da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Kano. A Jihar Borno kuwa, Gwamna Babagana Zulum ya ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen

Jam’iyyar PRP na shirin gudanar da zaɓukan fidda gwani ga ƴantakara 300

Jam’iyyar PRP a Najeriya ta ce ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaɓukan fidda gwani domin tantance ƴan takarar da za su tsaya mata takara a babban zaɓen 2027. Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya shaida wa BBC cewa jam’iyyar ta bi dukkan sharuddan doka kafin fara zaɓukan fidda gwanin da za a gudanar a faɗin ƙasar ranar Litinin 25 ga watan Mayun 2026. Ya ce PRP ta samu nasarar cimma matsaya a mafi yawan muƙamai, sai dai a takarar shugaban ƙasa inda aka samu rashin jituwa tsakanin masu neman takarar. A cewarsa, mutum biyar ne suka nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a ja

Leao da Bowen sun shiga jerin ‘yan wasan da Man United ke nema

Manchester United na gaba da sauran ƙungiyoyi wajen zawarcin ɗan wasan gaba na AC Milan kuma ɗan ƙasar Portugal, Rafael Leao, mai shekara 26, wanda aka sanya wa farashin fam miliyan 43. Haka kuma United na iya komawa neman ɗan wasan gaba na West Ham United kuma ɗan Ingila, Jarrod Bowen, mai shekara 29, idan West Ham ta faɗi daga gasar Firimiya. A wani ɓangaren kuma, Chelsea FC ta amince da sayen tsohon ɗan bayan gefe na Brighton & Hove Albion, Valentin Barco, mai shekara 21 daga Strasbourg. Mai tsaron ragar Liverpool FC, Alisson Becker, mai shekara 33, na shirin komawa Juventus FC domin sake a

Sabuwar fahimta kan sauya sheƙar siyasa bayan hukuncin kotu

Hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke kan wa’adin da Hukumar Zaɓe ta Najeriya, INEC, ta gindaya wa jam’iyyun siyasa ya haifar da sabon yanayi a siyasar ƙasar, musamman ga ƴan siyasar da ke son sauya sheƙa kafin zaɓen 2027. Kotun ta ce INEC ba ta da ikon tilasta wa jam’iyyun siyasa lokacin da za su kammala zaɓukan fidda gwani ko gabatar da sunayen ƴantakara, inda ta mayar da wa’adin tattara bayanan mambobi zuwa watan Satumban 2026. Mai shari’a M.G. Umar ya bayyana cewa dokar zaɓe ta bai wa INEC damar sanya ido kan zaɓukan cikin gida na jam’iyyu da kuma karɓar sunayen ƴantakara, amma ba ta b

An tabbatar da mutuwar mutum 82 a wani hatsarin ma’adinai a China

Aƙalla mutum 82 ne suka mutu, yayin da wasu biyu suka ɓace bayan fashewar gas a wani mahaƙar ma’adinan kwal a arewacin China, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito. Jami’an ceto sun sake rage adadin waɗanda suka mutu bayan sun fara sanar da cewa mutum 90 ne suka rasa rayukansu. Fashewar ta afku ne a mahaƙar ma’adinan Liushenyu da ke lardin Shanxi, kuma ana kallonta a matsayin mafi muni da aka samu a China tun shekarar 2009. Rahotanni sun ce ma’aikata 247 ne ke bakin aiki lokacin da lamarin ya faru da misalin ƙarfe 7:29 na safiyar Juma’a agogon GMT. An ceto fiye da mutum 100 daga

Tattaunawar Iran da Amurka ta kusa haifar da yarjejeniya

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Amurka da Iran na dab da cimma yarjejeniya ta ƙarshe kan tattaunawar da ke gudana tsakanin ɓangarorin biyu. Trump ya bayyana cewa zai amince ne kawai da yarjejeniyar da ta dace da muradun Amurka, kamar yadda ya shaida wa CBS. Ya kuma jaddada cewa duk wata yarjejeniya za ta tabbata ne idan Iran ta amince ba za ta mallaki makamin nukiliya ba, tare da miƙa sinadarin uranium ɗinta. A cewarsa, idan Iran ba ta amince da waɗannan sharuɗɗa ba, “ba zai yiwu a ci gaba da tattaunawa ba.”

Magoya bayan Senegal sun samu ‘yanci bayan tsarewa a Maroko

Sarkin Maroko Mohammed na shida ya yi afuwa ga wasu magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Senegal da aka daure bayan samun su da hannu a tayar da tarzoma a wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afrika da aka gudanar a birnin Rabat a watan Janairun 2026. An saki magoya bayan ne a wani mataki na jin ƙai da kuma ƙarfafa dangantaka tsakanin Maroko da Senegal, musamman yayin da ake shirin gudanar da Babbar Sallah. Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya bayyana a shafinsa na X cewa nan ba da jimawa ba magoya bayan za su koma wajen iyalansu. “Ina miƙa godiyata ga mai martaba saboda wannan mataki na ta

China za ta daina karɓar haraji kan kayayyakin ƙasashen Afirka 53

A ranar Juma’a ne China ta sanar da faɗaɗa cire haraji kan kayayyakin da ake shigar mata daga dukkan ƙasashen Afirka da ke da alaƙar diflomasiyya da ita, a wani mataki da ke da nufin ƙarfafa kasuwanci da bunƙasa masana’antu a nahiyar, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati suka ruwaito. A ƙarƙashin sabon tsarin, ƙasashen Afirka 53 ne za su amfana da cire harajin shigo da kaya, ciki har da Nijeriya da Kenya da Masar, a cewar kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Sabuwar manufar ta ƙara faɗaɗa tsarin da China ta riga ta aiwatar, wanda ya bai wa ƙasashe 33 mafi ƙarancin ci gaba a Afirka damar