AMMASCO RADIO NEWSROOM

top stories

Masu amfani da layukan sadarwa a Najeriya sun sake samun damar cin gajiyar ayyukan aron katin waya na gaggawa

Masu amfani da layukan sadarwa a Najeriya sun sake samun damar cin gajiyar ayyukan aron katin waya na gaggawa bayan Hukumar Kare Gasa da Kare Haƙƙin Mabukata ta Tarayya (FCCPC) ta dakatar da aiwatar da dokokinta na bayar da rancen kuɗi ta yanar gizo da hanyoyin zamani, wato ‘Digital, Electronic, Online or Non-Traditional Consumer Lending (DEON) Regulations 2025’. Matakin ya biyo-bayan umarnin da Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta bayar, inda ta umurci hukumar da ta dakatar da aiwatar da sabbin dokokin har sai an kammala shari’ar da ke ƙalubalantar ikon FCCPC na sa-ido kan tsarin aron katin wa

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya ba al'ummar jihar damar yin layya su raba nama ga mutanen da basu samu damar yin layyar ba

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya buƙaci al'ummar jihar da suka samu damar yin layya su raba nama ga mutanen da basu samu damar yin layyar ba kamar yadda Musulunci ya tanada. Gwamnan ya yi wannan bayani ne a saƙonsa na ranar Idi a jiya Laraba. A cewarsa, yin hakan zai kawo “sauƙi ga mutane masu rauni, baya ga samun lada daga Allah”. Ya ƙara da cewa Musulunci ya riga yayi bayani kan yadda ake raba naman layya, saboda haka ya kamata al'umma su bi ƙa'idar. A cewarsa, gwamnatin jihar na kashe maƙudan kuɗaɗe a kowace shekara wajen tallafa wa malaman addini da mabuƙata da ƴan-gudun hijira waɗanda

Rahoton Amurka ta ce masu tayar da ƙayar baya 30,000 ne ke haddasa tabarbarewar tsaro a Najeriya

Wani rahoto daga Hukumar Kula da ‘Yancin Addini ta Amurka (USCIRF) ya yi zargin cewa akwai kusan masu ɗauke da makamai 30,000 da ke gudanar da hare-hare a sassan Najeriya, lamarin da ke ƙara rura wutar rashin tsaro musamman a yankin Middle Belt da kudancin ƙasar. Rahoton na watan Mayun 2026 mai taken “Masu Take ‘Yancin Addini da Ba na Gwamnati ba a Nijeriya: Mayaƙan Fulani” ya bayyana cewa mayaƙan na aiki ne cikin ƙananan ƙungiyoyi masu mutum tsakanin 10 zuwa 1,000. A cewar rahoton, hare-haren da suke kaiwa sun yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, da tarwatsa al’ummomi daga muhallansu, tare da

Zamu yi duk mai yuwa wajen dawo da malamai da Dalibai da aka sace a Oyo - seyi Makinde

Gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde, ya tabbatarwa iyaye da al'ummar juharsa cewa Gwamnatinsa za ta yi duk mai yuwa wajen ganin ta kubutar da dukkan yara da malamai da aka yi garkuwa da su a ranar 16 ga watan Mayu a Karamar Hukumar Oriire, kuma za a dawo da su gida lafiya ga iyalansu. Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a gidansa da ke Ikolaba yayin da yake karbar bakuncin mataimakinsa Bayo Lawal, da sauran masu mukaman gwamnati Musulmai a Jihar Oyo cikin shagulgulan salah

Shugaban Tunisia shugaba Kais Saied ya yi afuwa ga ɗan majalisar dokokin ƙasar da aka yankewa hukuncin ɗaurin watanni takwas Sabida Yana sukarsa

Afuwar da shugaba Kais Saied ya yi masa na cikin shagulgulan sallar layya da ake gudanarwa a ƙasar a yau Laraba. A watan Faburairu dai aka yankewa Saidani hukuncin zaman gidan yari na watanni 8, bayan da ya wallafa wani rubutu da yayi kan shugaban ƙasar a lokacin da ya ziyarci wani yankin da aka samu ambaliyan ruwa, inda ya bayyana shi a matsayin babban kwamandan duba gari. Shi dai Saidani ya kasance ya kasance mai goyon bayan yadda gwamnatin Saied musamman yadda ta ke kulle ƴan adawa, sai dai a baya-bayan nan anga yadda shima ya ke sukar gwamnatin.

Gwamnatin kano ta bayar da gudumawar kayan abinci shanu 15, buhunan shinkafa 115da jarkokin man girki manya guda 40 ga gudajen gyaran Hali

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da shanu 15 da kayan abinci ga fursunoni da ke cibiyoyin gyaran hali daban-daban a fadin jihar domin bikin babbar Sallah. An bayar da tallafin ne ta hannun Shugabar Kwamiti ta Musamman na Jihar Kano, Hajiya Azumi Namadi-Bebeji, a ranar Talata a Kano. Kayan abincin da aka bayar sun hada da shanu 15, buhunan shinkafa 115 masu nauyin kilo 50, jarkokin man girki manya guda 40 da sauran kayan girki Namadi-Bebeji ta ce wannan tallafin na sake tabbatar da kudirin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na kula da jin dadin fursunoni da gyaren halayensu. Ta kara da cewa gwamna

Haryanzu Najeriya na da damar ciwo bashi daga waje don aiyukan cigaba da more rayuwa

Mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga, ya furta hakane yayin da yake kare manufofin gwamnatin tarayya na karbar bashi, inda ya ce har yanzu Najeriya na da kima ta fuskar amincewar masu bada bashi, kuma tana iya sake samun karin rance domin daukar nauyin manyan ayyukan more rayuwa masu muhimmanci. Onanuga ya bayyana hakan ne a ranar Talata cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, yayin da ake ci gaba da sukar yadda bashin kasar ke karuwa daga bangaren jama’a

jami’an tsaro a Jihar Kebbi sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da damfarar maniyyatan aikin Hajjin bana.

Jami’an tsaro a Jihar Kebbi sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da damfarar maniyyatan aikin Hajjin bana. Ana zargin mutanen da karɓar kuɗi daga hannun mutane da sunan samar musu guraben zuwa ƙasa mai tsarki. Rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya karɓi kuɗi har Naira 860,000 daga wani mutum, inda ya yi masa alƙawarin samar masa kujerun Hajji guda biyu. Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya ce kamen ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da waɗanda abin ya shafa suka kai wa hukuma tare da haɗin gwiwar Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar. Rundunar ta tabba

Rundunar yansandan jihar Kano ta sanar da samun nasarar kama wasu manyan dilolin muggan kwayoyi tare da kama wasu kwayoyin da dama.

Rundunar yansandan jihar Kano ta sanar da samun nasarar kama wasu manyan dilolin muggan kwayoyi tare da kama wasu kwayoyin da dama. Haka kuma rundunar ta sake kama wasu mutanen na daban da ake zargin suma suna ta’ammalin da muggan kwayoyin. Ta cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun rundunar yansanda CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce rundunar ta ci gaba sake bincike da sanya idanu kan wuraren da ta samu rahotanni ana aikata laifuka

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Laraba 27 ga watan Mayu da Alhamis, 28 ga watan a matsayin ranakun hutu domin shagulgulan Babbar Sallah.

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Laraba 27 ga watan Mayu da Alhamis, 28 ga watan a matsayin ranakun hutu domin shagulgulan Babbar Sallah. Cikin wata sanarwa da sakataren din-din na ma'aikatar cikin gida a madadin, ministan cikin gidan ƙasa, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce gwamnati ta bayar da hutun ne domin nuna martabawa ga miliyoyin musulman ƙasar. Sanarwar ta ce an bayar da hutun ne domin musulmai su samu damar yin shagulgular Babbar Sallah kamar yadda sauran Musulman duniya ke gudanarwa. Ministan ya kuma taya al'ummar musulmai na ciki da wajen ƙasar su yi amfani da muhimmin lokacin domin yi w

Muhammad Sani Abacha ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na gwamna da jam’iyyar PDP ta gudanar a Kano

Dan gidan tsohon shugaban kasa Sani Abacha, wato Muhammad Sani Abacha, ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na gwamna da jam’iyyar PDP ta gudanar a Kano. Rahotanni sun bayyana cewa Muhammad Bello Dalhatu ne ya kayar da shi, inda ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a babban zaɓen dake tafe. Da yake bayyana sakamakon zaɓen, shugaban kwamitin gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna, Umar Danjani Hadejia, ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana tare da bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar da kuma ƙa’idojin zaɓe. Ya bayyana cewa Muhammad Sani Abacha ya samu ƙuri’u 749, yayin da Muhammad Bello Dalhatu ya

Ban janye daga Neman takarar kujerar Majalisar Jiha a jam'iyar APC ba - Hon. Isa Adamu Bashir Tarauni

Mai neman takarar kujerar majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Tarauni, Hon. Isa Adamu Bashir (Isa Jaa), ya musanta ikirarin da dan majalisa mai ci, Hon. Kabiru Dahiru Sule ADS ya yi na cewa ya janye masa takara bisa maslaha. Hon. Isa Adamu Bashir (Isa Jaa) ya bayyana cewa har zuwa wannan lokaci bai janye daga takarar ba, kuma babu wanda ya tuntube shi domin tattaunawar maslaha ko neman ya hakura da kudirinsa na tsayawa takara. A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce labarin da aka yaɗa wa na cewa ya janye wa Hon. Kabiru Dahiru Sule ADS ba gaskiya ba ne, yana mai cewa babu

Iska mai ƙarfi ta lalata gidaje da gine-gine a wasu yankuna shida da ke Karamar Hukumar Tambuwal a Jihar Sokoto.

Wannan na cikin sanar da Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA ta fitar. Sanarwar ta ce al’ummar Nasarawa Tudu, Nasarawa Rahi, Kofar Attahiru, Danyali, Illela Takalmawa da Mai Banche ne lamarin ya shafa, inda mutane da dama suka samu raunuka yayin da gidaje da dama suka lalace. Hukumar ta ce ta tattauna da shugabannin al’umma da waɗanda abin ya shafa domin tantance irin tallafin gaggawa da ake buƙata musamman matsuguni, kayan amfanin gida da tallafin lafiya.

Jakadan Nijeriya a ƙasar Amurka, Kayode Are, ya fara aiki a hukumance

Jakadan Nijeriya a ƙasar Amurka, Kayode Are, ya fara aiki a hukumance bayan miƙa takardun kama aikinsa ga Shugaban Amurka, Donald Trump. Gabatar da takardun kama aikin na daga cikin muhimman matakan diflomasiyya da ke tabbatar da fara aikin jakada a ƙasar da aka tura shi aiki. Rahotanni sun bayyana cewa bikin ya gudana ne a wani taro na musamman da aka shirya a fadar shugaban ƙasar Amurka, inda aka karɓi sabbin jakadu daga ƙasashe daban-daban.

Ndiaye ya sauka daga shugabancin majalisar dokokin Senegal

Matakin murabus da shugaban majalisar ya ɗauka, ya sharewa tsohon firaminista Ousmane Sonko hanya na neman kujerar shugabancin majalisa, inda jam'iyyarsa ta Pastef ke da gagarumin rinjaye. Wata sanarwa da aka fitar a yammacin jiya Lahadi ta nuna cewar, an gayyaci ƴan majalisar a gobe Talata, don gudanar da wani zama na musamman da za a rantsar da Sonko a matsayin ɗan majalisar, da kuma zaɓen sabon shugaban majalisar. Faye dai ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a shekarar 2024 tare da goyon bayan Sonko, wanda da ace ba a hana shi tsayawa takara a zaɓen ba saboda zargin la

An ceto mutum 92 da Boko Haram suka sace a Borno

Dakarun Najeriya sun kuɓutar da aƙalla mutum 92 daga hannun mayaƙan Boko Haram a wani samame da suka kai a jihar Borno, tare da kwance nakiyoyi da aka dasa a kan hanyar Buratai zuwa Kamuya da ke ƙaramar hukumar Biu. A wata sanarwa da kakakin rundunar Operation Haɗin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar, ya ce waɗanda aka ceto sun haɗa da maza 52 da mata 33 da kuma yara bakwai. Sanarwar ta ce dakarun sun gano mayaƙan ne yayin da suke tilasta wa mutanen da suka sace tafiya zuwa cikin daji tare da wasu ababen hawa. Rahotanni sun ce bayan da mayaƙan suka fahimci cewa sojoji na binsu, sai suka das

An kashe ‘yan ta’adda 12 a wani samame da sojoji suka kai a Borno

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai a arewa maso gabashin Najeriya sun kashe aƙalla mayaƙa 12 da ake zargin ƴan ta’adda ne tare da ƙwato makamai a wani samame da suka kai a jihar Borno. An gudanar da aikin ne a yankin Kirawa da ke ƙaramar hukumar Gwoza, bayan wasu da ake zargin mayaƙan Daesh-WAP/Boko Haram ne sun yi ƙoƙarin kai hari sansanin Bataliya ta 153 da sauran jami’an tsaro da ke yankin kan iyakar Najeriya da Kamaru. A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar, ya ce dakarun sun gano harin cikin gaggawa tare da mayar da martani ma

Alhazai sun fara aikin Hajjin 2026 bayan isa Mina

Dubban Musulmai daga sassan duniya sun fara gudanar da aikin Hajjin shekarar 1447/2026 bayan fara kwararowa zuwa Mina a ranar Litinin 8 ga watan Zul-Hijjah, ranar da ake kira Tarwiyah. Mahajjatan na barin masaukansu a birnin Makka cikin farin ciki da tawali’u, suna masu amsa kiran Hajji da kalmar “Labbaikallahumma Labbaik”, yayin da maza ke sanye da fararen tufafin harami, mata kuma cikin tufafin da suka dace da ibada. Ana sa ran kusan Musulmai miliyan biyu ne za su gudanar da aikin Hajjin bana, kamar yadda Hukumar Kididdiga ta Saudiyya ta bayyana. Ranar Tarwiyah ita ce farkon ayyukan Hajji, i

Hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya Federal Road Safety Corps ta shawarci direbobin da ke tafiya ta hanyar Abuja zuwa Kaduna

Hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya Federal Road Safety Corps ta shawarci direbobin da ke tafiya ta hanyar Abuja zuwa Kaduna da su yi amfani da wasu hanyoyi domin kauce wa cunkoson da ke addabar babban titin a wannan lokaci na bukukuwan Babbar Sallah. Hukumar ta ce ana samun taruwar ababen hawa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna sakamakon yawan masu tafiya Sallah da kuma ayyukan gyaran hanya da ke gudana a wasu sassa na titin. Wannan hali ya sa motsin ababen hawa ya ragu musamman a yankin Katari zuwa Jere. A dalilin haka ne FRSC ta shawarci matafiya su yi amfani da wasu hanyoyi, kamar hanyar Kaduna

Rundunar 'yan sandan jihar kwara ta tabbatar da sace mutum 10 a garin Yashikira na karamar hukumar Baruten

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta tabbatar da cewa wasu ’yan bindiga sun sace mutane 10 a fadar Sarkin Yashikira da ke ƙaramar hukumar Baruten a jihar. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Adetoun Ejire-Adeyemi a ranar Litinin, ta ce maharan sun kuma kai hari ofishin ’yan sanda na Yashikira da misalin ƙarfe 2 na dare ranar Litinin. Sanarwar ta ce Yan bindigar, cikin wani hari na haɗin gwiwa sun kai farmaki hedikwatar rundunar ’yan sanda ta Yashikira da kuma fadar Sarkin Yashikira. A yayin harin maharan sun kuma banka wa wani ɓangare na fadar wuta, yayin da suka yi awun