Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasarnan, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya nuna shakku kan ikirarin cewa jami’an tsaron kasarnan ba sa iya gano inda ‘yan bindiga
Tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasarnan, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya nuna shakku kan ikirarin cewa jami’an tsaron kasarnan ba sa iya gano inda ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane suke, duk da cewa suna yawan wallafa bidiyoyi tare da sadarwa daga maboyarsu. Buratai ya jaddada cewa hukumomin tsaro suna da ƙarfin gano irin waɗannan masu laifi. Buratai ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na TVC a ranar Litinin, yayin da yake mayar da martani kan damuwar da ake nunawa game da yadda ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke amfani da kafafen sada zumunta da bidiyo wa
