Ghana Ta Tallafa wa ‘Yan Ƙasarta da Aka Maido Daga Afirka Ta Kudu da Ayyuka 120
Ma’aikatar Harkokin Wajen Ghana Ta Samar da Guraben Aiki 120 Ga Waɗanda Aka Maido Daga Afirka Ta Kudu Ma’aikatar Harkokin Wajen Ghana ta samar da guraben ayyukan yi guda 120 ga ‘yan ƙasar da aka dawo da su daga Afirka Ta Kudu, biyo bayan tashin rikicin ƙin jinin baƙi da ya addabi ƙasar. A cewar ma’aikatar, an samar da ayyukan ne ta hanyar haɗin gwiwa da ‘yan kasuwa a ƙasar, a wani yunƙuri na tallafa wa mutanen da suka baro dukiyoyinsu da sana’o’insu a Afirka Ta Kudu domin tsira da rayukansu. Ministan harkokin wajen Ghana ya yi kira ga ‘yan kasuwa da masu kamfanoni masu zaman kansu da su ba wa
