AMMASCO RADIO NEWSROOM

top stories

Yansandan Kano Sun Kama ’Yandaba da Dilolin Ƙwaya 345 Cikin Kwana Uku

Rundunar 'Yansandan Jihar Kano ta sanar da kama mutane 345 da ake zargi da hannu a ayyukan daba, safarar miyagun ƙwayoyi da kuma mallakar makamai masu haɗari a wani samame na musamman da ta gudanar a faɗin jihar cikin kwanaki uku. Da yake jawabi ga manema labarai a Hedikwatar Rundunar da ke Bompai a ranar Litinin, Kwamishinan 'Yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce an gudanar da aikin ne bisa umarnin Babban Sufeton 'Yansandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, tare da amfani da sahihan bayanan sirri da kuma rahotannin da aka samu daga al'umma. A cewarsa, samamen ya gudana ne tsa

Talauci Ya Ƙaru a Najeriya, Mutum Miliyan 60 Sun Kara Faɗawa Matsin Rayuwa – IMF

Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Najeriya ta aiwatar sun taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar, amma kuma sun zo da ƙalubale masu tsanani ga rayuwar al'umma, inda sama da 'yan Najeriya miliyan 60 suka ƙara faɗawa cikin talauci. A cikin wani rahoto da hukumar ta fitar, IMF ta ce matakan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka cikin shekaru uku da suka gabata, ciki har da cire tallafin man fetur, sauya tsarin kasuwar canjin kuɗaɗen waje da kuma gyaran tsarin haraji, sun taimaka wajen daidaita wasu fannoni na tattalin ar

Najeriya Ta Yi Barazanar Daukar Mataki Kan Hare-Haren da Ake Kai wa 'Yan Ƙasarta a Afrika ta Kudu

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana nazarin matakan da za ta ɗauka kan abin da ta kira hare-hare da cin zarafin da ake yi wa 'yan ƙasarta a Afrika ta Kudu, yayin da take shirin fara kwashe wasu daga cikinsu daga ƙasar a ranar Laraba. Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Ojukwu, ta ce gwamnati na duba yiwuwar mayar da martani kan abubuwan da ke faruwa, tare da ci gaba da tattaunawa domin cimma matsaya kan matakin da ya dace a ɗauka. Ta zargi hukumomin South Africa da rashin ɗaukar matakan da suka dace domin dakile hare-haren da ake kai wa 'yan Najeriya, duk da cewa yawancin waɗanda ke z

Babu wanda ya isa ya hana ni zuwa ko ina a Najeriya - Sheikh Gumi

Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya magantu kan ziyarar da ya kai garin Ibadan a ƙarshen shekarar da ta gabata, bayan ce-ce-ku-ce da suka biyo baya cewa yana ƙoƙarin yaɗa manufofin addinin Musulunci a Jihar Oyo. Gumi ya jaddada cewa babu wanda zai hana shi ziyartar ko'ina a cikin ƙasar nan, yana mai cewa ba wata ƙungiyar Musulmi ko wani mutum daga yankin Kudu maso Yamma ne ya gayyace shi ba. A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata, ya ce ya je Ibadan ne a matsayin wakilin malaman addinin Musulunci na Arewacin Najeriya. Ya bayyana hakan ne kwana gu

Isra'ila Ta Kara Karfafa Hadin Gwiwa da Najeriya a fannin Noma da Kiwon Lafiya

Kasar Isra’ila ta ce tana ci gaba da karfafa hadin gwiwa da Najeriya a bangaren noma, inda manoman Najeriya ke amfana da iri da sabbin fasahohin noma na Isra’ila. A cewar jaridar Punch, Jakadan Isra’ila a Najeriya, Michael Freeman, ya bayyana cewa kasarsa ta tallafa wa Najeriya da motocin daukar marasa lafiya domin inganta ayyukan kiwon lafiya.

Sabbin Ministoci Biyu Sun Kama Aiki Bayan Tinubu Ya Rantsar da Su

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da sabbin ministoci biyu, inda ya naɗa Joseph Tegbe a matsayin Ministan Lantarki, yayin da Sola Enikanolaiye ya zama Ƙaramin Ministan Harkokin Waje. An gudanar da bikin rantsarwar ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, tare da halartar iyalan sabbin ministocin da manyan jami’an gwamnati. Joseph Tegbe, ɗan asalin Ibadan da ke Jihar Oyo, ƙwararren masani ne a fannin sauye-sauyen tattalin arziki, harkokin kuɗi da tsarin hukumomi. Ya shafe sama da shekaru 35 yana aiki a gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, inda ya taka muhimmiyar rawa a fannoni da

Mutum Uku Sun Mutu, Kimanin 40 Sun Jikkata a Hatsarin Jirgin Ƙasa a Delta

An tabbatar da mutuwar mutum uku tare da jikkatar kusan mutum 40 a wani hatsarin jirgin ƙasa da ya faru a Najeriya. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin, inda fasinjoji da dama suka samu raunuka daban-daban. Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ƙasar ya sauka daga kan layin dogo ne yayin da yake kan hanyarsa daga Warri zuwa Itakpe, a yankin Agbor na jihar Delta da ke kudancin Najeriya. A cikin wata sanarwa da NRC ta fitar, ta ce ta tura jami’an kai ɗaukin gaggawa tare da sauran hukumomin da abin ya shafa zuwa wurin da hatsar

Najeriya na bukatar shugabanni masu nagarta da kwarewa ba Yan shiyar kudu ko Arewa ba - Hakeem Baba

Shugaban Jam’iyyar PRP Hakeem Baba-Ahmed, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina duba yanki ko shiyya wajen zaɓen shugabanni, maimakon haka su zaɓi mutanen da ke da ƙwarewa, nagarta da hangen nesa. Baba-Ahmed ya yi wannan kira ne cikin shirin kamfanin dillancin Labarai na kasa NAN, mai taken Personality Interview Series a ranar Talata a Abuja. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa shugaban na PRP ya yi wannan bayani ne a daidai lokacin da tsohon gwamnan Cross River State, Donald Duke, ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar domin zaɓen gama gari na shekarar 2027.

Gonakin Gwamnati ya kamata a kai matasa da aka kama a kano - Abba Hikima

Fitaccen lauya mai fafuktukar kare hakkin Dan adam Barista Abba Hikima, ya wallafa wannan sharawa ce a shafinsa na Facebook, kwana guda bayan da hukumar 'yan sanda ta jihar Kano tayi baje kolin wasu matasa masu dunbin yawa data kama Kan aikata laifuka daban daban a jihar. Hikima ya kara da cewa, idan har kotu ta tabbatar da laifin da ake zargin matasan da aikatawa, to mai makon a mika su gidan Gyaran hali, a Kai su wani fili ko gona su yi noma wasu kuma su share gari. Musamman ma waɗanda basu yi nisa a harkar ba. Inda ya cigaba da cewa yana yabawa jami’an yan sanda kan ƙoƙarinsu na kamo waɗann

Hukumar INEC ta fitar da jerin ƴan takarar zaben cike gurbi

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta wallafa jerin sunayen ƴan takarar da za su fafata a zaɓukan cike gurbi da aka shirya gudanarwa a ranar 20 ga Yunin 2026 a wasu kujerun Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da Majalisun Dokokin Jihohi. A zaɓen Sanatan Ondo ta Kudu, ƴan takara huɗu ne za su fafata, waɗanda suka haɗa da Adesanya Olaoluwa na APP, Faduyile Francis Adedayo na APC, Akinwumi Adeolu Harrison na APM da kuma Nejo Funso Clement na BP. A mazaɓar Sanatan Nasarawa ta Arewa kuwa, Halilu Danladi Envwulu-Aza ne zai yi takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC, yayin da Maku Labaran ke wakil

NDC ta ɗauki matakin sulhu bayan ɓarkewar rikici a jam’iyyar

Jam’iyyar NDC ta sanar da ɗaukar wasu muhimman matakai da nufin ƙarfafa dimokuraɗiyya, ladabtarwa da haɗin kai a cikin jam’iyyar, yayin da take shirin tunkarar zaɓuɓɓuka masu zuwa. An cimma matsayar ne a taro na biyu na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar, kamar yadda ke ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa, Osa Director, ya fitar a ranar Asabar. A cewar sanarwar, jam’iyyar ta amince da kafa kwamitin sulhu domin magance duk wata rashin jituwa da ka iya tasowa a tsakanin mambobinta tare da ƙarfafa haɗin kai a cikin gida. Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa dukkan gwam

Masu neman sulhu sun faɗa hannun 'yan bindiga a Zamfara

Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da dattijan wani ƙauye a Ƙaramar Hukumar Maradun da ke Jihar Zamfara bayan sun amsa gayyatar yin sulhu da su domin kawo ƙarshen hare-haren da suka addabi yankin. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Magamin Diddi, wanda ke kusa da wani daji da ake zargin 'yan bindigar ke amfani da shi a matsayin mafaka. Da yake zantawa da BBC, Shugaban Ƙaramar Hukumar Maradun, Sunusi Ahmed Dosara, ya ce tun watanni uku da suka gabata mazauna ƙauyen ke fama da hare-haren 'yan bindiga da suka hana su gudanar da harkokinsu cikin walwala. Ya bayyana cewa 'yan bindigar sun aika saƙon gayyata

Masana MDD kan ’yancin addini sun fara ziyarar aiki a Najeriya

Manyan jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya masu kula da harkokin ’yancin addini sun fara wata ziyarar aiki ta makwanni biyu a Najeriya domin nazarin halin da ake ciki game da ’yancin addini da zamantakewar al’umma a ƙasar. Ziyarar na zuwa ne bayan ce-ce-ku-ce da suka taso a shekarar da ta gabata kan zarge-zargen tauye ’yancin addini, musamman bayan wasu rahotanni da suka yi ikirarin cewa ana fuskantar ƙalubale wajen kare haƙƙin mabiya addinai daban-daban a Najeriya. Masana da masu bincike kan harkokin tsaro sun ce matsalolin da Najeriya ke fuskanta sun fi alaƙa da matsalar ta’addanci da hare-haren

An saki sama da mutum 400 da Boko Haram ta yi garkuwa da su a Borno

Satar mutane ta zama ɗaya daga cikin manyan dabarun da mayaƙan Boko Haram ke amfani da su a hare-haren da suke kaiwa a Najeriya tsawon sama da shekaru 17, musamman a yankin arewa maso gabas. Ƙungiyar Boko Haram ta saki fiye da mutum 400 da ta sace a farkon wannan shekara daga wani ƙauye da ke Jihar Borno, kamar yadda wani sanata da kuma wani shugaban ƙungiyar matasa suka tabbatar a ranar Lahadi. Samaila Kaigama, shugaban ƙungiyar Borno South Youth Alliance (BOSYA), ya bayyana cewa ƙungiyarsu ta tabbatar da sakin mata da yara 416 da aka sace daga ƙauyen Ngoshe. Ya ce an saki mutanen ne a ranar

Atiku ya yabawa sojojin Najeriya kan ceto mutum 360 daga hannun Boko Haram a Borno

Atiku ya yabawa sojojin Najeriya kan ceto mutum 360 daga hannun Boko Haram a Borno Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yaba wa dakarun sojin Najeriya bisa nasarar da suka samu wajen kuɓutar da mutum 360 da aka sace a ƙauyen Ngoshe da ke Jihar Borno. Rahotanni sun ce an gudanar da aikin ceton ne a yankin Dutsen Mandara, inda mayaƙan Boko Haram suka tsare mutanen bayan wani hari da suka kai kan sansanin soji da ke Ngoshe. A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, Atiku ya bayyana farin cikinsa kan nasarar aik

Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗaɗen gudanarwa na ministoci zuwa N700,000

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da sabbin matakan da nufinsu shi ne ƙarfafa bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗen gwamnati da kuma inganta gaskiya da riƙon amana a ma’aikatun gwamnati. A ƙarƙashin sabbin ƙa’idojin, an rage adadin kuɗaɗen gudanarwa da ake warewa ministoci domin ayyukan gaggawa da sauran buƙatun ofis zuwa Naira 700,000. Matakin na daga cikin sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa domin tabbatar da an bi dokokin kuɗi yadda ya kamata tare da rage almubazzaranci a amfani da dukiyar jama’a. Sabuwar ƙa’idar ta fito ne cikin wata takarda da ta tanadi iyakar kuɗaɗen da jami’an gwamnati za su

Atiku ya yabawa jami'an tsaron kasarnan Kan ceto mutane daga hannun boko haram

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya yabawa jami’an tsaro bisa nasarar ceto mutane 360 da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su a garin Ngoshe da ke jihar Borno . Atiku ya bayyana farin cikinsa da wannan nasara, yana mai cewa hakan ya kawo ƙarshen wahalar da waɗanda aka sace da iyalansu suka shafe watanni suna fuskanta tun bayan sace su a watan Maris. Ya kuma yabawa rundunar soji, musamman dakarun Operation HADIN KAI, da sauran hukumomin tsaro da suka taka rawa wajen gudanar da aikin ceton. Tsohon mataimakin s

KNARDA ta yi gargaɗi ga manoma da al’ummar jihar kan wasu mutane da ke amfani da sunanta wajen karɓar kuɗi da sunan samar da tallafin noma.

Hukumar Bunƙasa Noma da Raya Karkara ta Jihar Kano (KNARDA) ta yi gargaɗi ga manoma da al’ummar jihar kan wasu mutane da ke amfani da sunanta wajen karɓar kuɗi da sunan samar da tallafin noma. Shugaban hukumar, Dakta Farouk Ahmad Kurawa, ya bayyana cewa an gano wasu na karɓar kuɗi daga manoma, musamman a karkara, suna alƙawarin samar musu da taki, iri da sauran kayan aikin gona. Hukumar ta bayyana cewa ba ta karɓar kuɗi daga manoma domin samun tallafin gwamnati ko wani taimako, tare da cewa duk masu yin hakan ƴan damfara ne. KNARDA ta buƙaci al’umma su yi hattara da irin waɗannan mutane, sanna

Gwamnatin Tarayya ta sauya ranar fara jigilar rukunin farko na ‘yan Najeriya da ke son dawowa daga ƙasar Afirka ta Kudu, biyo bayan hare-haren kin jinin baki

Gwamnatin Tarayya ta sauya ranar fara jigilar rukunin farko na ‘yan Najeriya da ke son dawowa daga ƙasar Afirka ta Kudu, biyo bayan hare-haren kin jinin baki (xenophobia). Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin. A cewar Ebienfa, an sauya ranar jigilar rukunin farko na waɗanda ke son dawowa daga Afirka ta Kudu, wanda tun farko aka tsara yi a ranar Litinin (yau), zuwa ranar Laraba saboda wasu matsalolin shirye-shirye da ba a yi hasashensu ba. Ta ce Shugaba Bola Tinubu ya amince da jiragen kwashe mutane g

Rundunar Hisbah ta Kano ta sanar da cewa za ta fara gudanar da gwajin lafiya ga mutanen da za su amfana da shirin auren gata

Rundunar Hisbah ta Kano ta sanar da cewa za ta fara gudanar da gwajin lafiya ga mutanen da za su amfana da shirin auren gata da gwamnatin jihar ke shiryawa, wanda zai haɗa ma'aurata 3,000. Mataimakin Babban Kwamandan rundunar, Dr. Mujahideen Aminuddeen, ya bayyana cewa daga ranar Litinin 8 ga watan Yunin 2026 za a fara aikin tantancewar, inda ake buƙatar duk masu neman shiga shirin daga ƙananan hukumomi 24 su jr ofisoshin Hisbah da ke yankunan su. Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Rogo, Wudil, Tudun Wada, Warawa, Kibiya, Dawakin Tofa, Garun Malam, Kura, Dambatta, Karaye, Tsanyawa,