AMMASCO RADIO NEWSROOM

top stories

Dole Najeriya ta karfafa tsaron iyakokinta don kare kasar daga barazanar tsaro - Christopher Musa

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yi kira da a ɗauki matakan kariya na gaggawa domin ƙarfafa tsaron iyakokin Najeriya daga laifuffukan ƙetare da kuma sabbin barazanar tsaro da ke tasowa. Da yake jawabi a wani taron ƙasa na wuni guda mai taken “Tsaron Iyakoki, Haɗin Gwiwar kasahen Ƙetare ” wanda Hukumar Kula da Iyakokin Ƙasa (NBC) ta shirya, Musa ya ce wajibi ne Najeriya ta sauya tsofaffin hanyoyin tsaro ta rungumi zamani , da fasahar gargaɗin Kai tsaye da fasaha ke jagoranta, da kuma ƙarfafa musayar bayanan sirri da ƙasashen maƙwabta. Ya bayyana cewa ingantaccen kula da i

Kwastam Ta Yi Bayani Kan Zargin Rashin Miƙa Naira Biliyan 62.2 ga Asusun Tarayya

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta yi karin haske kan zargin rashin miƙa Naira biliyan 62.2 ga Asusun Tarayya, yayin wani zaman bincike da Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Asusun Jama'a ya gudanar. Hukumar ta bayyana cewa kuɗaɗen da aka bayyana a matsayin waɗanda ba a miƙa ba a shekarar 2017, harajai ne da ta karɓa a madadin wasu hukumomi, kuma ba kuɗaɗen da ya kamata a tura kai tsaye zuwa Asusun Tarayya ba ne. Bayanin ya zo ne a matsayin martani ga tambayar bincike da Ofishin Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Tarayya ya gabatar, wadda ta samo asali tun daga shekarar 2019. Babban Kwanturola Janar na Hukum

Jihohi na da isassun kudaden Samar da aiyukan more rayuwa da gina kasa, karkashin Mulkin Shugaban Tinubu

Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da Shugaba Bola Tinubu ya aiwatar sun ƙara wa jihohi kuɗaɗen shiga domin gudanar da ayyukan raya ƙasa. Onanuga ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Umuahia, babban birnin Jihar Abia, yayin wani taron karɓar baƙuncin tawagar yawon duba ayyukan gwamnatin tarayya Karkashin shirin Renewed Hope ta kafafen yaɗa labarai, wadda ta kai ziyara jihar domin duba ayyuka daban-daban da aka aiwatar tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya da kuma waɗanda gwamnatin jihar ta gudanar. A cikin jawabinsa,

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ɗaukar ma’aikatan tsaron gandun daji (Forest Guards) guda 1,000 a Katsina

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ɗaukar ma’aikatan tsaron gandun daji (Forest Guards) guda 1,000 domin ƙarfafa ƙoƙarin da ake yi na magance matsalar tsaro a Jihar Katsina. Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawa da malamai na addinin Musulunci da sauran masu ruwa da tsaki a Gidan Gwamnati da ke Katsina. Taron ya ba da damar tattaunawa kan hanyoyin da al’umma za su taka rawa wajen magance matsalolin fashi da makami da kuma garkuwa da mutane. Radda ya ce ganawar da aka yi da shugabannin addini

Majalisar Dattawa ta karyata ikirarin Sanata Adams Oshiomhole na cewar an sanya hannun bogi a dakatar da Natasha

Majalisar Dattawa ta yi watsi da zargin da Sanata Adams Oshiomhole ya yi cewa an ƙirƙira sa hannun bogi na wasu sanatoci ba bisa ka’ida ba a cikin rahoton da ya ba da shawarar dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, tana mai bayyana zargin a matsayin marar tushe. Jarida punch ta rawaito cewa, mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, a yayin wata tattaunawa da Wakilinnsu ya ce matakin ladabtarwa da aka ɗauka kan sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ya bi dukkan matakan doka da ka’idojin majalisar, kuma an gudanar da shi a fili a zauren majalisar. Adaramodu ya ce Majalisa

Ma’aikatar Harkokin Waje da NLNG Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Kan Diflomasiyyar Tattalin Arziki

Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta bayyana Kamfanin Nigeria LNG (NLNG) a matsayin wata muhimmiyar kadara ta ƙasa, tana mai cewa nasarorin da kamfanin ke samu sun yi daidai da manufofin gwamnati na tabbatar da tsaron makamashi da jawo hannun jari da bunƙasa masana’antu. Ministar ta bayyana hakan ne lokacin da ta karɓi bakuncin Manajan Daraktan NLNG, Injiniya Adeleye Falade, a Abuja. A yayin ganawar, ɓangarorin biyu sun amince da ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa domin bunƙasa diflomasiyyar tattalin arzikin Najeriya da kuma jawo ƙarin zuba jari a fannin makamashi. Shi ma Manajan

Kotun Katsina ta Yanke wa Hauwa’u Mukhtar Hukuncin Mutuwa ta Rataye

Kotun Tarayya ta Jihar Katsina ta yanke wa Hauwa’u Mukhtar hukuncin mutuwa ta hanyar rataye bayan da aka same ta da laifin hadin gwiwa don aikata ta’addanci da taimakawa da goyon bayan ta’addanci. Hukumar Tsaro ta Jiha (DSS) ce ta gabatar da ƙarar. An kama Mukhtar a ranar 16 ga Satumba, 2023, a tashar mota ta Jibia a Jihar Katsina, lokacin da take ƙoƙarin jigilar harsashi 438 na 7.62mm zuwa wani sanannen shugaban ‘yan bindiga mai suna Ado, wanda ke aiki a cikin Dajin Dunburum na Jihar Zamfara. Hukumar DSS ta gabatar da tuhumar maki biyu a gaban Kotun Tarayya mai lamba 3 a Katsina, a ƙarar KTH/

Daliban UTME Sun Fara Duba Sakamakonsu Bayan JAMB Ta Fitar da Sakamako

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Ƙasa (JAMB) ta fitar da sakamakon jarabawar UTME ta maimaitawa, wadda aka gudanar ga ɗaliban da ba su samu damar rubuta jarabawar farko ba, saboda matsalolin fasaha da tantance bayanan halittu (biometric verification). A cikin sanarwar da Mai Ba da Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai na Hukumar, Dakta Fabian Benjamin, ya fitar, ya buƙaci ɗaliban da abin ya shafa su duba sakamakonsu ta hanyoyin da hukumar ta amince da su. Dakta Benjamin ya bayyana cewa, bayan fitar da sakamakon, hukumar za ta fara tantancewa da tsara jerin ɗalibai bisa ga maki da

Yan Sanda Sun Tabbatar da Mutuwar Jami’an Tsaro Uku a Cibiyar NIPSS da ke Jos

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Plateau ta tabbatar da mutuwar jami’an tsaro uku a wata matsalar tsaro da ta faru a Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun Ƙasa (NIPSS) da ke Kuru a Jos da sanyin safiyar ranar Talata. A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, SP Alfred Alabo, ya fitar, ya ce lamarin ya shafi wasu jami’an tsaro da ke bakin aiki a cibiyar a lokacin da abin ya faru. Alabo ya bayyana cewa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Plateau, CP Bassey Ewah, ya tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin tare da ƙarfafa sintiri domin tabbatar da tsaron mazauna yankin da kuma hana sake afkuwar m

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya sanar da sabbin matakan tsaro domin daƙile ayyukan ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar.

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya sanar da sabbin matakan tsaro domin daƙile ayyukan ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar. A cikin umarnin da ya fitar bayan taron gaggawa na tsaro, gwamnatin ta haramta saye, sayarwa, jigilar kaya da adana man fetur a cikin jarkoki a faɗin jihar baki ɗaya. Haka kuma, an rufe dukkan cibiyoyin POS da wuraren cajin wayoyi na kasuwanci a ƙananan hukumomin Matazu da Musawa, bayan rahotannin tsaro sun nuna cewa masu laifi na amfani da su wajen gudanar da ayyukansu. Bugu da ƙari, gwamnatin ta hana amfani da babura a duk faɗin ƙananan hukumomin Mata

Gwamnatin Kano ta kaddamar Kwamitin mutum 10 don bincikae zargin karkatar da gyadar tamowa, da sauran abinci yara Mai dauke da magani

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani babban kwamitin da zai gudanar da bincike kan satar gyadar tamowa abincin yara mai suna RUTF.da aka tanada domin kula da yara masu fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki a faɗin jihar. Yayin ƙaddamar da kwamitin a madadin Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne domin gano haƙiƙanin abin da ya faru na zargin karkatar da waɗannan muhimman kayayyakin ceto rayuka, tare da tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamari

Anyi amfani da son zuciya da sa hannu na bogi wajen dakatar da Sanata Natasha na watanni shida - Oshiomhole

Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya yi zargin cewa an yi amfani da sa hannun jabu ko kuma aka saka sunayen wasu sanatoci ba tare da amincewarsu ba a rahoton da ya ba da shawarar dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida. Jaridar Punch ta rawaito cewa, Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na AIT, inda ya ce akalla sanatoci uku sun shaida masa cewa ba su sanya hannu a rahoton ba duk da cewa an saka sunayensu a ciki. Ya ce Sanatar Babban Birnin Tarayya (FCT), Ireti Kingibe, na daga cikin wadanda suka ce ba su sanya hannu a rahot

Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Aƙalla Mutum 20 a Harin da Suka Kai Kebbi

Aƙalla mutum 20 ne suka rasa rayukansu bayan da mayaƙan ƙungiyar Lakurawa suka kai hari ƙauyen Fasken Rafi da ke ƙaramar hukumar Arewa a jihar Kebbi. Rahotanni sun ce harin ya faru ne a ranar Lahadi, inda mazauna yankin suka bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin hare-haren da aka tsara sosai da aka kai kan al’umma a kwanakin baya-bayan nan. Harin ya kuma jikkata wasu mutane da ke karɓar magani a cibiyoyin lafiya da ke kusa. Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta tura wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamnan jihar, Umar Tafida, domin jajanta wa iyalan waɗanda

Sojoji Sun Ceto Matar Marigayi Janar Rabe Daga Hannun ’Yan Bindiga

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da ceto matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar daga hannun ’yan bindiga bayan wani samame da dakarun haɗin gwiwa suka kai a jihar Katsina. A wata sanarwa da Daraktan Sashen Yaɗa Labarai na rundunar, Sama’ila Uba, ya fitar, ya ce dakarun Operation Fansan Yamma ne suka gudanar da farmakin a Ƙaramar Hukumar Matazu. Sanarwar ta ce jami’an tsaro sun yi arangama da ’yan bindigar a ƙauyen Tunga, lamarin da ya tilasta musu tserewa sakamakon matsin lambar da dakarun suka yi musu. Sai dai kafin su gudu, ’yan bindigar sun harbi matar marigayin. Duk da haka, sojojin sun

Gwamnatin kano ta ayyana Talata 16 ga watan yuni a matsayin hutun na sabuwar shekarar musulunci.

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar Talata 16 ga Yuni, 2026 a matsayin ranar hutu domin gudanar da bukukuwan sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 bayan hijira. Wannan na cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labaran jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar a yau litinin. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya al'ummar Musulmi murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci da ta fara da watan Muharram. Ya bukaci al'ummar jihar da Musulmi baki daya su yi amfani da wannan lokaci wajen yin tunani kan ayyukansu na shekarar da ta gabata tare da yin addu'o'in zaman lafiya, hadin kai da ci gaba ga jihar da kas

Jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ganowa ta kam tare da gurfanar da mutane da kungiyoyin da ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya

Jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ganowa ta kam tare da gurfanar da mutane da kungiyoyin da ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya. tana mai gargadin cewa matsalar tsaro ba za ta kau ba matukar ba a hukunta masu daukar nauyin kungiyoyin masu tayar da kayar baya ba. Jam’iyyar ta kuma sake jaddada goyon bayanta ga kafa ‘yan sandan jihohi, tana mai cewa tsarin tsaro da aka karkata zuwa matakin jihohi zai karfafa magance matsalar tsaro a yankuna tare da taimakawa wajen magance tabarbarewar tsaro a kasar. Da yake magana a wani taron mane

Tsadar Rayuwa Ta Ƙaru Yayin da Hauhawar Farashi Ta Kai Kashi 15.93

Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ta ƙaru zuwa kashi 15.93 cikin ɗari, lamarin da ke nuna ci gaba da tsadar rayuwa da al’ummar ƙasar ke fuskanta. Sabbin alkaluman sun nuna ƙarin hauhawar farashin kayayyaki idan aka kwatanta da watan da ya gabata, inda farashin abinci da sufuri da sauran muhimman kayayyakin masarufi suka ci gaba da tashi. Masana tattalin arziki na danganta hauhawar farashin da sauye-sauyen tattalin arziki, tsadar makamashi da kuma ƙalubalen samar da kayayyaki a wasu sassan ƙasar. Hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke shafar ƙ

Sojojin Najeriya Sun Ƙaddamar da Hare-Hare Kan Maɓoyar ’Yan Bindiga a Katsina

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da ƙaddamar da wasu zafafan hare-hare kan maɓoyar ’yan bindiga a wasu yankuna na jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar. Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan rasuwar wani tsohon janar na soja a hannun masu garkuwa da mutane a jihar. A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa an ƙaddamar da farmakin ne ƙarƙashin wani aiki mai suna Operation Clean Sweep III , domin fatattakar ’yan bindiga daga ƙaramar hukumar Matazu da sauran yankunan jihar Katsina. Sanarwar ta ce an fara aikin

NDC Ta Tsayar da Mustapha Kwankwaso a Matsayin Mataimakin Ɗan Takarar Gwamnan Kano

Jam'iyyar NDC ta tsayar da Mustapha Rabi’u Kwankwaso a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamnan jihar Kano a zaɓen shekarar 2027. Ɗan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ne ya sanar da matakin, inda ya bayyana cewa Mustapha Kwankwaso zai kasance abokin takararsa a zaɓen mai zuwa. Mustapha Kwankwaso ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Kano a shekarar 2023, kafin ya ajiye muƙamin a shekarar 2026. Hadimin Rabiu Musa Kwankwaso, Saifullahi Hassan, ne ya tabbatar da wannan mataki ta wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Rahotanni sun ce

Tashin Hankali Ya Mamaye Wurin Taron G7 Yayin Da Aka Yi Arangama da Masu Zanga-Zanga

An samu arangama tsakanin ’yansanda da masu zanga-zanga a birnin Geneva na ƙasar Switzerland, gabanin fara taron ƙasashen G7 da za a gudanar a Évian-les-Bains na ƙasar Faransa. Rikicin ya faru ne a wajen hedkwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Geneva, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen taron shugabannin ƙasashen G7. An gudanar da zanga-zangar ne a ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar “No-G7” , wadda ta haɗa fiye da ƙungiyoyi 60 da suka haɗa da masu fafutukar kare haƙƙin Falasɗinawa, masu rajin kare haƙƙin mata da kuma masu kare muhalli. Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun jefa kwalabe da duwat