AMMASCO RADIO NEWSROOM

top stories

Dole shugaban Tinubu ya ayyana dokar ta baci Kan matsalar tsaro kafin ya gagari kundila - makarfi

Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon sanata, Ahmed Mohammed Makarfi, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci kan matsalar rashin tsaro a Najeriya. Makarfi ya bayyana cewa halin da ƙasar ke ciki na rashin tsaro ya kai matakin da ke bukatar daukar matakin gaggawa domin dakile yawaitar hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da kuma kashe-kashen jama’a. Akwai bukatar gwamnati ta ƙara ƙarfafa hukumomin tsaro, tare da samar musu da kayan aiki da dabarun zamani domin tunkarar matsalar cikin inganci. Makarfi ya Kara da cewa, Najeriya na buƙatar haɗin kai tsakan

Yakubu Kingsley ya shigar da Donald Duke kara gaban kotu yana kalubalantar zamansa Dan takarar shugaban kasa a jam’iyar PRP

Mai neman takarar kujerar shugaban ƙasa a jam’iyyar PRP, Yakubu Kingsley, ya kalubalanci nasarar tsohon gwamnan Jihar Cross River, Donald Duke, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasar jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027. A cikin ƙarar da aka shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/1234/2026, Kingsley ta hannun lauyansa, D.A. Sulyman, ya shigar da ƙara a kan jam’iyyar PRP, Duke INEC a matsayin waɗanda ake ƙara na farko, na biyu da na uku bi da bi. Mai ƙarar na neman kotu ta soke ayyana Duke a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, inda yake zargin cewa tsohon gwamnan ba cikakken ɗan jam’iyyar ba ne kum

Dala Biliyan 6 Na Cikin Tayin Da Amurka Ke Yi Wa Iran

Wani rahoto da kafar yaɗa labarai ta Axios ta wallafa ya ce Amurka na neman Iran ta amince da bai wa masu binciken Majalisar Ɗinkin Duniya damar duba cibiyoyinta na nukiliya, a wani yunkuri na farfaɗo da tattaunawar da ke tsakanin ɓangarorin biyu. Rahoton ya ambato wasu majiyoyi daga yankin da suka ce Washington na son a cimma yarjejeniya inda Iran za ta sake buɗe ƙofofin cibiyoyinta na nukiliya ga masu bincike na ƙasa da ƙasa. An bayyana cewa wasu daga cikin waɗannan cibiyoyi sun taɓa fuskantar hare-hare daga Amurka da Isra’ila a baya, kuma ba a gudanar da irin wannan bincike ba tun watan Yun

Hukumar dake kula da aiyukan Gidajen gyaran Hali, Kashe gobara da civil defence ( CDCFIB) ta karyata rahotonnin dake cewa ta dage daukar sabbin jami'ai

Hukumar Kula da Ayyukan tsaro na farar hula, Gidajen Gyaran Hali, Kashe Gobara da Shige da Fice (CDCFIB) ta karyata wata sanarwar bogi da ke yawo a kafafen sada zumunta wadda ke ikirarin cewa an dage aikin daukar ma’aikatan shekarar 2026. Hukumar ta karyata Labarin ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Lahadi. Hukumar ta bukaci masu neman aiki da daukacin jama’a da su yi watsi da takardar saboda ba ta da inganci. Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta saki sunayen wadanda suka samu nasara a jarabawar da hukumar ta gudanar da akayi da kwamfuta a watan nuwanbar 2025. Inda hukuma

muna murnar soyayya, juriya da sadaukarwar da iyaye maza ke nunawa a faɗin Najeriya da ma duniya baki ɗaya - Remi Tinubu

Uwar gidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta taya iyaye maza a Najeriya da ma duniya baki ɗaya murnar Ranar Uba ta Duniya da ake gudanarwa a yau Lahadi. A cikin saƙonta na murnar ranar, ta yaba da ƙoƙari, juriya da jajircewar iyaye maza wajen kula da tarbiyyar ’ya’yansu da kuma ɗaukar nauyin iyalansu. Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana cewa iyaye maza na taka muhimmiyar rawa wajen gina tunani, tarbiyya da ƙwarin gwiwar yara, lamarin da ke taimakawa wajen kyautata makomarsu. Ta kuma ce soyayya, jagoranci, kariya da sadaukarwar da iyaye maza ke yi suna taimakawa wajen gina iyalai masu ƙarfi

Hon wanzam Zaki Dan Majalisa a Jihar Bauhci ya rasu a safiyar wannan rana

Dan majalisar dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Sakwa kuma Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar, Wanzam Zaki, ya rasu. Wanzam ya rasu ne a safiyar ranar Lahadi a garin Bauchi bayan gajeriyar rashin lafiya. Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Abubakar Sulaiman, ne ya sanar da rasuwar cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mukhtar Garba Kobi, ya fitar a ranar Lahadi. Kakakin Majalisar ya bayyana matuƙar alhininsa kan rasuwar, inda ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen kuma sadaukararren mai hidimar jama'a wanda ya yi wa mazabarsa da Jihar Bauchi hidima ta gari da kwarewa.

Shin da gaske ne Kasar Iran ce ta yi Nasara a yakin gabas ta tsakiya?

Wani sabon bincike da aka gudanar a Isra’ila ya nuna cewa mafi yawan ‘yan ƙasar na ganin Iran ce ta fi cin moriyar rikicin Gabas ta Tsakiya da kuma yarjejeniyar da ta kulla da Amurka. Binciken da jami’ar Hebrew ta Urushalima tare da cibiyar Agam suka gudanar tsakanin 17 zuwa 20 ga watan Yuni ya nuna cewa kashi 92 cikin 100 na waɗanda aka tambaya sun yi imanin cewa Iran ce ta yi nasara ko ta fi amfana da rikicin. kashi 83 cikin 100 sun ce tsaron Isra’ila na dogon lokaci ya raunana sakamakon rikicin. Kazalika binciken ya nuna cewa kashi 72 cikin 100 na mahalarta ba su yarda da ikirarin Firamini

MDD Ta Nuna Damuwa Kan Rashin Hukunta Masu Laifi a Najeriya

Wakiliya ta musamman ta Majalisar Ɗinkin Duniya kan ’Yancin Addini ko Imani, Nazila Ghanea, ta bayyana cewa rashin hukunta masu aikata laifuka da kuma raunin aiwatar da doka na daga cikin abubuwan da ke ƙara haddasa zarge-zargen tsanantawa da ma kisan kare-dangi a Najeriya. Ghanea ta bayyana hakan ne bayan wata ziyarar bincike ta tsawon makonni biyu da ta kai Najeriya domin tantance halin da ake ciki dangane da ’yancin addini da zaman tare tsakanin al’ummomi. Ta ce yawaitar hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da kuma gaza gurfanar da masu hannu a laifuka na ci gaba da tauye ’yancin add

Rundunar Sojin Najeriya Za Ta Fara Ɗaukar Ƴan Jarida A Lokacin Ayyuka

Gwamnatin Tarayyar Najeriya na nazarin wani sabon tsari da zai bai wa ƴan jarida damar yin rakiya da dakarun sojin ƙasar a lokacin da za su ƙaddamar da wasu farmaki na musamman. Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya bayyana hakan a yayin wani taro da Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta shirya a Abuja. Ministan ya ce matakin zai taimaka wajen inganta yadda ƴan jarida ke bayar da rahotanni kan haƙiƙanin abin da ke faruwa a yaƙin da ake yi da masu tayar da ƙayar baya da sauran matsalolin tsaron cikin gida. Ya ce hakan zai ƙara fahimtar da jama’a ayyukan da rundunar sojin ƙasar ke yi. Mai ba s

Majalisar Dokokin Zimbabwe Ta Amince da Tsawaita Wa'adin Shugaban Ƙasa Zuwa Shekara Bakwai

Majalisar dokokin Zimbabwe ta amince da ƙudirin doka na tsawaita wa'adin mulkin shugaban ƙasa daga shekara biyar zuwa bakwai. Wannan matakin zai bai wa Shugaba Emmerson Mnangagwa damar ci gaba da mulki har zuwa shekara ta 2030. Fiye da yan majalisa 200 ne suka kada ƙuri’a don amincewa da daftarin dokar a ranar Alhamis, abin da ya zarce kashi biyu bisa uku da ake buƙata domin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin ƙasar. Ƙudirin ya kuma soke batun zaɓen shugaban ƙasa kai tsaye, inda daga yanzu ƴan majalisa za su kasance masu zaɓen shugabannin ƙasar. Mnangagwa, mai shekara 83, ya karɓi mulki ne

Tsoffin Janar-Janar Sun Bukaci Garambawul a Tsarin Tsaro Bayan Kisan Janar Rabe Abubakar

Tsoffin hafsoshin sojin Najeriya da abokan aikin marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su sake duba tsarin tsaron ƙasar tare da ɗaukar matakan da suka dace domin magance matsalar rashin tsaro. Sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna, bayan rasuwar tsohon Janar ɗin wanda aka ce wasu ƴan bindiga sun sace tare da kashe shi a Jihar Katsina. Birgediya Janar Isma’ila Abdullahi (mai ritaya), wanda ya yi magana a madadin abokan aiki da iyalan marigayin, ya ce lokaci ya yi da za a yi wa tsarin tsaron ƙasar garambaw

An Kashe Mutane 30 a Harin da aka Kai Filin Jirgin Sama na Niamey a Nijar

An kashe sojoji 11 a harin da aka kai filin jirgin sama na birnin Niamey a Jamhuriyar Nijar, inda aka ce an kashe mutane 30 gabaɗaya. Ma’aikatar Tsaro ta ƙasar ta ce daga cikin mutanen da aka kashe akwai sojoji 11 da fararen hula biyu, yayin da aka kashe mutum 22 daga cikin maharan. Da sanyin safiyar yau Alhamis ne aka fara jin ƙarar harbe-harbe da fashe-fashe a babban filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na birnin Niamey. Har yanzu ba a bayyana waɗanda suka kai harin ba. Hukumomin ƙasar sun ce an daƙile harin, kuma za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama a filin. Nijar tare da maƙotanta Mali da

Firaministan Equatorial Guinea Ya Yi Murabus Tare da Gwamnatinsa Bayan Gaza Cika Alƙawura

Firaministan ƙasar Equatorial Guinea, Manuel Osa Nsue Nsua, ya yi murabus tare da dukkan mambobin gwamnatinsa bayan zargin cewa sun gaza cika alƙawuran da aka ɗora musu. Mataimakin Shugaban Ƙasar, Teodoro Nguema Obiang Mangue, wanda shi ne ɗa ga Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, ya bayyana cewa gwamnatin ta kasa cimma har ma da kashi 10 cikin 100 na manufofin da aka ɗora mata tun lokacin da aka kafa ta. Ya ce firaministan ya miƙa takardar murabus ɗinsa tare da sauran ministoci da manyan jami’an gwamnati, bayan an yi nazari kan yadda suka gudanar da ayyukansu. Ko da yake ba a bayyana takam

JD Vance Ya Bukaci Isra'ila Ta Mutunta Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Mataimakin Shugaban Amurka, J.D. Vance, ya bayyana cewa kowace ƙasa na da haƙƙin kare kanta, amma ya jaddada cewa Isra'ila dole ne ta mutunta yarjejeniyoyin zaman lafiya da ake ƙoƙarin cimma a yankin Gabas ta Tsakiya. Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan sukar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi game da hare-haren da Isra'ila ta kai a Lebanon, Vance ya ce ba ya son tauye wa Isra'ila haƙƙinta na kare kanta daga barazanar tsaro. Duk da haka, ya bayyana damuwarsa game da wani hari da ya afku a wani yanki da jama'a ke zaune a birnin Beirut, yana mai cewa abin ya faru ne a daidai lokacin da

Tara Buhunan Ba-Haya a Ƙofar Gida Ya Jawo Wa Mutum Ɗauri da Tara

Wata kotu a birnin Kano ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗauri da tarar kuɗi bayan an same shi da laifin tara buhunan ba-haya a ƙofar gidansa, lamarin da ya haddasa mummunan wari tare da barazana ga lafiyar maƙwabtansa. An gurfanar da Mohammed Sa’idu ne bayan mazauna unguwar sun kai ƙorafi kotu, suna zargin cewa buhunan ba-hayar da yake jibgawa a ƙofar gidansa sun jawo wari mai tsanani wanda ya hana su walwala da zama cikin kwanciyar hankali. Mai shari’a Halima Wali ta yanke hukuncin ɗaurin wata huɗu tare da tarar Naira 100,000, tana mai bayyana abin da ya aikata a matsayin barazana ga lafiyar

Najeriya Ta Sanya Hannu Kan Sabon Alƙawarin Goyon Bayan MDD

Gabanin zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA), Najeriya ta sanya hannu kan wata sabuwar takardar jaddada goyon baya ga Kundin Tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ajandar gyaran tsarin MDD ta UN80. Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ne ya sanya hannu a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana cewa Najeriya na ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa. Jakada Ibrahim, wanda kuma shi ne shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi, Kashe-Kashe da Gudanarwa na MDD, ya ce matakin ya nuna cikakken amincewar N

Jihohi da Kananan Hukumomi Sun Raba Naira Tiriliyan 2.3 Na Kudin Shiga na Mayun 2026

Kwamitin Raba Kudaden Tarayya (FAAC) ya raba jimillar Naira tiriliyan 2.3 ga matakan gwamnati uku a matsayin rabon kudaden shiga na watan Mayun 2026. Adadin da aka amince da shi a taron FAAC na watan Yunin 2026 ya kunshi Naira tiriliyan 1.611 daga kudaden shiga na doka (Statutory Revenue) da kuma Naira biliyan 688.785 daga harajin ƙarin darajar kaya da ayyuka (VAT). Daga cikin kudaden da aka raba, Gwamnatin Tarayya ta karɓi Naira biliyan 818.680, yayin da gwamnatocin jihohi suka samu Naira biliyan 759.141. Haka kuma, kananan hukumomi sun karɓi Naira biliyan 534.277. Jihohin da ake hako mai kuw

Rashin Tsaro a Kan Iyakoki Na Kara Rura Matsalar Tsaro a Najeriya – Ribadu

Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa rashin cikakken tsaro a kan iyakokin Najeriya na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa matsalolin tsaro a ƙasar. Ribadu ya ce matsalolin sun haɗa da ta’addanci, safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba, fasa kwauri, safarar mutane da kuma ƙaura ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda ke ci gaba da barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasa. Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja yayin buɗe taron ƙara wa juna sani na ƙasa karo na 15 kan harkokin tsaro, wanda Ƙungiyar Tsofaffin Daliban Kwalejin Tsaron Ƙasa (AANDEC) ta shirya

Ragin Farashin Dangote Ba Ya Kai Tsaye Zuwa Gidajen Mai – PETROAN

Ƙungiyar masu gidajen mai ta Nijeriya (PETROAN) ta bayyana cewa rage farashin man fetur da matatar Dangote ke yi ba ya bayyana kai tsaye a gidajen mai saboda wasu dalilai da suka shafi samarwa da rarraba man fetur. Shugaban ƙungiyar, Billy Gillis-Harry, ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce farashin man fetur ga masu amfani da shi na dogara ne da abubuwa da dama, ciki har da wadatar man a wurare daban-daban, kuɗin jigila, ajiya da kuma yadda ake kai man zuwa gidajen mai. Ya ce idan farashin man ya ƙaru, masu gidajen mai kan ɗaga farashi cikin gaggawa domin

Matar shugaban kasa Oluremi Tinubu ta bada tallafin Miliyan 100 ga mata Yan kaduwa 200 a jihar Benue

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ba da tallafin naira miliyan 100 ga ƙananan ’yan kasuwa mata 2,000 a Jihar Benue domin su fara ko kuma su bunƙasa harkokinsu na kasuwanci. Ta bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da Cibiyar Yaɗa Bayanai da Fasahar Sadarwa ta Al’umma (ICT) da ke Ihugh, a Ƙaramar Hukumar Vandeikya ta jihar, inda ta jaddada cewa fasahar ICT muhimmiyar hanya ce ta ƙarfafa al’umma, musamman mata. Remi Tinubu ta ce a yanzu Benue tana da cibiyoyin ICT guda huɗu, yayin da aka kafa wasu guda 15 a jihohin tarayya da suka haɗa da Abia, Cross River, Rivers, Delta, Ebonyi, Edo,