AMMASCO RADIO NEWSROOM

top stories

Ƙungiyar Likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta yi gargaɗin cewa matsalar tamowa na ci gaba da barazana ga rayuwar dubban yara

Ƙungiyar Likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta yi gargaɗin cewa matsalar tamowa na ci gaba da barazana ga rayuwar dubban yara a jihar Kebbi da ma yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, inda ta ce ana samun ƙaruwar yara masu fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana cewa alƙaluman da ta tattara sun nuna ƙaruwa mai yawa a yawan yara masu fama da tamowa tsakanin shekarun 2024 da 2025, lamarin da ya tilasta mata sauya dabarun agaji domin dakile matsalar kafin ta ƙara muni. MSF ta ce bayanan Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya

yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Kuda-Kuda da ke Ƙaramar Hukumar Goronyo a Jihar Sokoto

Wasu 'yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Kuda-Kuda da ke Ƙaramar Hukumar Goronyo a Jihar Sokoto, inda suka kashe babban limamin ƙauyen, Liman Audu, tare da wasu mutum uku. Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kuma yi garkuwa da mutum shida bayan sun mamaye ƙauyen da tsakar dare. Waɗanda suka rasa rayukansu sun haɗa da Yahaya Hasanu, Zahara Mu'azu da Ibrahim Dayyabu. An ce harin ya fara ne da misalin ƙarfe 12:58 na dare, inda maharan suka shafe kusan sa'o'i biyu suna harbe-harbe tare da haddasa firgici a tsakanin mazauna yankin. Haka kuma sun yi awon gaba da dabbobi masu ya

Kafa yan sandan jihohi zai taimaka wa jihohi wajen kare al’ummarsu yadda ya kamata, musamman Kiristocin da ake tsanantawa cewar dan majalisar Amurka

Dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya yi maraba da amincewar Majalisar Dattawan Najeriya da Kudirin Gyaran Kundin Tsarin Mulki da ke neman kafa ‘yan sandan jihohi, yana mai cewa wannan gyara zai taimaka wa jihohi wajen kare al’ummarsu yadda ya kamata, musamman Kiristocin da ake tsanantawa. Moore, wanda ke wakiltar Mazabar 2 ta Jihar West Virginia a Majalisar Wakilan Amurka, ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba. Martaninsa ya biyo bayan amincewar Majalisar Dattawa da kudirin da ke neman rarraba ikon aikin ‘yan sanda ta hanyar bai wa jihohi dam

Amurka sun sanar da samar da wata allurar rigakafin cutar Ebola

Jami’an Amurka sun sanar da samar da wata allurar rigakafin cutar Ebola ta gwaji yayin da ake ci gaba da fama da ɓarkewar cutar a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo (DR Congo). Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ana jigilar maganin daga Amurka domin gudanar da gwaje-gwaje a asibitoci. Kamfanin Mapp Biopharmaceutical ne ya samar da allurar, wadda aka ƙera ta amfani da sanadaran garkuwar jiki daga mutanen da suka kamu da cutar Ebola amma suka warke a shekarar 2014. Ana sa ran Hukumar Lafiya ta Duniya za ta gudanar da gwaje-gwaje domin tantance inganci da amincin maganin kafin a amince da amfani da

Majalisar Dattawan Najeriya za ta fara muhawara a yau Laraba kan wani muhimmin kudirin doka da ke neman samar da rundunonin ‘yansandan jihohi

MAJALISAR NAJERIYA ZA TA FARA MUHAWARA KAN KUDIRIN KAFAR ‘YANSANDAN JIHOHI Ana sa ran Majalisar Dattawan Najeriya za ta fara muhawara a yau Laraba kan wani muhimmin kudirin doka da ke neman samar da rundunonin ‘yansandan jihohi, wanda ake ganin zai kawo babban sauyi a tsarin tsaron ƙasar. Kudirin gyaran Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika wa majalisar, zai bai wa jihohi 36 damar kafa da gudanar da rundunonin ‘yansandansu tare da ci gaba da kasancewar rundunar ‘yan sandan tarayya. Tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, gwamnatin tarayya ce ke

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta umarci a gudanar da bincike kan wasu jami’anta

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta umarci a gudanar da bincike kan wasu jami’anta da aka gani a wani bidiyo suna jan ɗan gwagwarmaya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, bayan zaman kotu a Abuja. Matakin ya biyo bayan umarnin da Babbar Kotun Tarayya ta bayar na tsare Sowore a gidan gyaran hali na Kuje har sai an saurari ƙarar da ya shigar kan batun belinsa. Alƙali Mohammed Umar ya yanke hukuncin ne bayan ya yi watsi da buƙatar Sowore na janyewar alƙalin daga shari’ar bisa zargin nuna son kai. A wata sanarwa, mai magana da yawun DSS, Favour Dozie, ya ce shugaban huk

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da sanya dokar hana fita ta sa’o’i 16 a ƙananan hukumomi

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da sanya dokar hana fita ta sa’o’i 16 a ƙananan hukumomi 10 na jihar domin magance matsalolin tsaro da ke addabar yankunan. A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Musibau Babatunde, ya fitar, an bayyana cewa dokar za ta fara aiki daga ranar Laraba, 24 ga Yuni, 2026, daga ƙarfe 4:00 na yamma zuwa ƙarfe 8:00 na safe. Ƙananan hukumomin da dokar ta shafa sun haɗa da Oriire, Orelope, Irepo, Saki West, Saki East, Atisbo, Itesiwaju, Iseyin, Olorunsogo da Atiba, musamman yankunan da ke kusa da gandun dajin Old Oyo National Park. Gwamnatin ta ɗau

Faransa ta sanar da cutar Ebola a ƙasar

Faransa ta sanar da tabbatar da ɓullar cutar Ebola a ƙasar bayan wani likita da ya dawo daga aikin jin ƙai a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DR Congo) ya kamu da cutar. Ma’aikatar Lafiya ta Faransa ta ce an kwantar da likitan a wani asibiti na musamman domin kula da shi, kuma a halin yanzu yana cikin yanayi mai kyau. Rahotanni sun nuna cewa wannan ne karo na farko da aka tabbatar da kamuwar cutar Ebola a Faransa, yayin da hukumomi suka fara bin diddigin duk mutanen da suka yi hulɗa da marar lafiyar domin hana yaɗuwar cutar. A lokaci guda, Uganda da DR Congo na ci gaba da fama da ɓarkewar cuta

Matatar Mai ta Dangote ta karyata zargin cewa tana sayarwa tare da sake sayo mai daga Kasar Togo

Kamfanin Matatar Mai ta Dangote Petroleum Refinery ya yi watsi da zarge-zargen da ke cewa ana fitar da kayayyakin man fetur da ake tacewa a matatar zuwa birnin Lomé na ƙasar Togo, sannan daga baya a sake shigo da su Najeriya. PUNCH Online ta rawaito cewa wasu bayanai da suka yadu a kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa ana fitar da kayayyakin da matatar Dangote ke samarwa zuwa ƙasashen maƙwabta kafin a dawo da su Najeriya. A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta shafinsa na X ranar Talata, mahukuntan matatar sun bayyana zargin a matsayin marar tushe kuma wanda bai dogara da haƙiƙanin kasuwa

Gwamnatin Kaduna ta go yi bayan gurfanar da mutane 24 gaban kotu Kan kashe wata Mata a maraban Jos

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi maraba da gurfanar da mutane 24 da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa wata mata a yankin Maraban Jos, inda ta bayyana wannan matakin a matsayin wani muhimmin ci gaba wajen tabbatar da adalci da kuma bin doka da oda. Haka kuma, gwamnatin ta yaba wa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna kan abin da ta bayyana da gaggawar daukar mataki cikin kwarewa dangane da lamarin. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar, Ahmed Maiyaki, ya fitar ranar Talata, gwamnatin ta yi Allah-wadai da tarzoma da kuma daukar doka a hannu mutane suka yi, tare

Da ni kadai ke da ikon hukunci da na haramta amfani bakin gilashi a mota, cewar sufeto Janar na Yan sandan Najeriya

Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya bayyana cewa da a ce ikon yanke hukunci yana hannunsa shi kaɗai, da ya zai haramta amfani da motoci masu gilashi masu duhu (tinted vehicles) gaba ɗaya a faɗin ƙasar nan. Ya ce motoci masu gilashi masu duhu na barazanar ga tsaro, kuma masu garkuwa da mutane, ’yan fashi da makami da kuma masu aikata laifin “one-chance” na yawan amfani da su wajen aikata miyagun ayyuka. Disu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake mayar da martani kan damuwar da Shugaban Nigerian Bar Association, Afam Osigwe (SAN), ya nuna dangane da sabunta lasisin gilash

Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu, Garba Maidoki, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa ADC

Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu, Garba Maidoki, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa ADC, inda ya danganta matakin da rikice-rikicen cikin gida da kuma zargin rashin adalci a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a jihar Kebbi. An karanta wasiƙar ficewarsa a zauren Majalisar Dattawa a ranar Talata ta hannun Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin. A cikin wasiƙar, Sanata Maidoki ya ce rikice-rikicen da ke addabar APC sun shafi harkokinsa na siyasa, kuma ya zaɓi ADC ne saboda manufofinta da yake ganin za su fi amfani ga al’ummarsa da ƙasa baki ɗaya. Ya kuma zargi APC da gazawa wajen

Sarkin ya yi wannan kiran ne lokacin da ya karbi bakuncin  kwamishinan ruwa muhalli da sauyin yanayi Dakta Tahir Muhammad Hashim a fadar sa domin kaddamar da aikin dashen bishiyu a fadin jihar ban.

‎ Mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sunusi II ya yi kira ga al'ummar jihar Kano da su dasa bishiyu a muhallan su domin inganta muhalli. ‎Sarkin ya yi wannan kiran ne lokacin da ya karbi bakuncin kwamishinan ruwa muhalli da sauyin yanayi Dakta Tahir Muhammad Hashim a fadar sa domin kaddamar da aikin dashen bishiyu a fadin jihar ban. ‎Da yake jawabi Mai martaba Sarki ya yaba wa kwamishinan bisa kaddamar da wannan aiki mai muhimmanci na inganta muhalli, tare da godiya bisa gudunmawar bishiyu 500 da aka kawo masa. ‎A nasa jawabin kwamishinan ruwa muhalli da sauyin yanayi na jihar Kano Dakta Tahir M

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Hadin Kai sun ceto mutum 47

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Hadin Kai sun ceto mutum 47, mafi yawansu mata da ƙananan yara, daga hannun mayaƙan ISWAP a yankin Kangarwa da ke ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno. A cewar rundunar, an samu nasarar ceton mutanen ne a ranar 20 ga Yuni, 2026 bayan wani samame da sojoji suka kai, wanda ya tilasta wa ‘yan ta’addar tserewa tare da barin waɗanda suka tsare. Sanarwar ta ce hare-haren ƙasa da na sama da aka kai wa sansanonin ISWAP a yankin Tafkin Chadi sun haddasa rikicewa a tsakanin ‘yan ta’addar, lamarin da ya bai wa waɗanda aka tsare damar samun ‘yanci baya

Rundunar yansanda na shirin fara amfani da na’urorin daukar hoto da bidiyo da jami’ai za su rika sanyawa a jikinsu yayin aiki

Rundunar yansanda na shirin fara amfani da na’urorin daukar hoto da bidiyo da jami’ai za su rika sanyawa a jikinsu yayin aiki, domin tabbatar da gaskiya, rikon amana da kuma inganta hulda tsakanin jami’an tsaro da al’umma. Mataimakin babban sufeton yansanda mai kula da sashen horaswa da ci gaba, DIG Frank Mba, ne ya bayyana hakan, inda ya ce shirin na daga cikin matakan da rundunar ke dauka wajen zamanantar da aikin yansanda da kuma kara amincewar jama’a ga hukumar. A cewarsa, amfani da wadannan na’urori zai taimaka wajen rage zarge-zargen cin zarafi, tabbatar da adalci yayin gudanar da aiki d

Kungiyoyin fulani sun yi Kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Oyo da su gargadi Sunday Igboho, kan kalaman da suka ce na iya haddasa rikicin kabilanci

Kungiyoyin Fulani a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya sun yi gargadin cewa zargin kabilar Fulani da hannu a ayyukan garkuwa da mutane ba tare da hujja ba na iya haifar da rikicin kabilanci da kuma dagula zaman lafiya a yankin. Kungiyoyin sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Oyo da su gargadi mai fafutukar kare hakkin Yarabawa, Sunday Igboho, kan kalaman da suka ce na iya haddasa rashin jituwar kabilanci. Wannan na zuwa ne bayan da Sunday Igboho ya bai wa masu garkuwa da mutane wa'adin sa'o'i biyu su sako wasu daliban da aka sace a Jihar Oyo, tare da yin barazanar daukar mataki idan ba a s

Magoya bayan Sowore sun zargi DSS da cin zarafinsa ta hanyar kama ci da karfin tuwo da kuma raunata shi

Magoya bayan mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, sun zargi jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da kama shi da ƙarfi a ranar Litinin duk da umarnin kotu da ya tanadi a tsare shi a gidan gyaran hali. Zargin ya biyo bayan umarnin da Mai Shari’a Mohammed Umar ya bayar na a tsare Sowore a Gidan Gyaran Hali na Kuje har sai an yanke hukunci kan buƙatarsa ta neman dakatar da aiwatar da wani umarni na baya da ya soke belinsa. Mai shari’ar ya kuma yi watsi da buƙatar da Sowore ya gabatar na ya janye da

Ku sauko da farashin siminti don saukaka gine gine a najeriya- FG

Gwamnatin Tarayya ta yi ga kamfanionin Samar da siminti a Najeriya da su rage farashin siminti domin saukaka manyan aiyukan gine gine a kasarnan. Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a wajen ƙaddamar da sabon tambarin kamfanin Lafarge Africa, wanda yanzu aka sake masa suna zuwa HBM bayan kamfanin HUAXIN Group na ƙasar Sin ya mallake shi. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga Ministan kan Harkokin Yaɗa Labarai, Francis Nwaze, ya fitar a ranar Litinin. Da yake jawabi a gaban shugabannin masana’antu, masu zuba jari da sauran mas

DPO ne ya cire wa matata hijabi, ya tura ta kan titi

Aliyu Muhammad ya bayyana alhininsa bayan da wasu fusatattun mutane suka kashe tare da ƙona matarsa, Ummulkhairi, a jihar Kaduna bisa zargin satar yara. Ya ce tun kwanaki biyu kafin faruwar lamarin yana jin gabansa na faɗuwa, amma bai gaya mata ba domin kada ta damu. A ranar da lamarin ya faru, sun yi sallama da safe yayin da matar ta tafi wani wa’azi, shi kuma ya tafi aiki. Daga baya aka sanar da shi cewa an kama matarsa da zargin satar yara kuma an kai ta gidan mai unguwa. Sai dai kafin a gudanar da bincike ko tabbatar da zargin, mutane sun taru a gidan suna neman a miƙa musu ita domin su hu

Ma'aikatar kula da lafiya a matakin farko ta jijar kano, ta dakatar da dukan sugabannin masu aikin Rigakafi da aka tura Hotoron Arewa

Ma’aikatar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kano (KSPHCMB) ta amince da wasu muhimman matakai domin ƙarfafa ingancin ayyukan rigakafi, tabbatar da sahihancin bayanai da kuma inganta yadda ake gudanar da gangamin rigakafin BCU/IBRA na watan Yunin 2026. An cimma waɗannan matsayai ne a taron kwanaki biyu na masu ruwa da tsaki da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar na ma’aikatar, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, kamar yadda ke kunshe cikin wata sanarwar manema labarai da Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta KSPHCMB, Sa’adatu Sulaiman ANIPR, ta sanya wa hannu a ranar 21 ga Yunin 2026. Bayan naz