Atiku ya zargi cewa akwai wani sabon shiri da ake yi na hana jam'iyar ADC Shiga zaben 2027
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa akwai wani sabon shiri da ake yi domin hana jam’iyyar ADC shiga zaɓen shekarar 2027. A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce ya samu sahihan bayanai da ke nuna cewa ana amfani da hanyoyin siyasa da na shari’a domin hana jam’iyyar shiga zaɓen. Ya ce manufar wannan shiri ita ce raunana ‘yan adawa tare da hana ‘yan Najeriya damar zaɓar shugabanninsu cikin ‘yanci. Atiku ya zargi jam’iyyar APC mai
