Iran Ta Fara Zaman Makoki Yayin da Ake Shirye-shiryen Jana'izar Ayatollah Ali Khamenei
Iran ta fara gudanar da zaman makoki na ƙasa baki ɗaya yayin da ake shirye-shiryen jana'izar tsohon Jagoran Addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei , wanda aka kashe fiye da watanni huɗu da suka gabata a hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai. Hukumomi sun bayyana cewa za a ajiye gawarsa a babban ɗakin taro na Grand Mosalla da ke birnin Tehran daga ranar Juma'a, inda jama'a za su samu damar yi masa bankwana, kafin a kai gawar zuwa garinsu na Mashhad domin binne shi a ranar Alhamis mai zuwa. A cewar kamfanin dillancin labarai na AFP , ana sa ran sama da mutane miliyan 20 daga sassa daban-daban
