AMMASCO RADIO NEWSROOM

top stories

Aƙalla sojojin Mali 50 sun mutu a kwanton-ɓauna a arewacin ƙasar

Hukumomi a arewacin Mali sun ce mayaƙan Tuareg masu neman ɓallewa tare da mayaƙan ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi sun kashe aƙalla sojojin Mali 50 a wani kwanton-ɓauna da suka yi wa ayarin motocin soji a ranar Asabar. A cewar jami'an yankin, maharan sun kuma yi garkuwa da sama da mutum 20 a yayin harin. Bayanin ya zo daidai da iƙirarin da Azawad Liberation Front (FLA) ta yi, inda ta ce mayaƙanta sun yi wa sojojin Mali da kuma dakarun Rasha da ke mara musu baya mummunar illa a harin. A cewar FLA, ayarin motocin sojin na kan hanyarsa ne daga garin Anefis , mai muhimmanci ta fuskar dabarun soja,

Shugaban Lebanon ya tafi Amurka domin ganawa da Donald Trump

Shugaban ƙasar Lebanon , Joseph Aoun , ya bar birnin Beirut zuwa Washington , inda ake sa ran zai gana da shugaban Amurka, Donald Trump , kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta sanar. Ziyarar ta zo ne bayan kammala zagaye na shida na tattaunawar Lebanon da Isra'ila , wanda aka gudanar a ofishin jakadancin Amurka da ke Rome , ƙasar Italiya, a ranakun 13 da 14 ga watan Yuli . A cewar fadar shugaban ƙasar Lebanon, Aoun zai tattauna da manyan jami'an gwamnatin Amurka kan halin tsaro da siyasar ƙasarsa, da kuma hanyoyin ƙarfafa yarjejeniyar tsagaita wuta, musamman a kudancin Lebanon. Ana kuma sa ran t

An yi zargin kutse cikin shafin intanet na fadar shugaban ƙasar Kenya

Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na Kenya sun ce wasu masu kutse ta intanet sun kutsa cikin shafin intanet na fadar shugaban ƙasar, William Ruto , tare da neman a biya su bitcoin biyar , wanda darajarsa ta kai kusan Shilling miliyan 41 na Kenya (kimanin dala 320,000 ) kafin su saki shafin. A cewar rahotannin, masu kutse sun sauya shafin farko na intanet, inda suka maye gurbin bayanan hukuma da saƙonnin cin mutunci ga shugaban ƙasar, tare da barazanar fitar da wasu muhimman bayanan gwamnati. A halin yanzu, shafin president.go.ke ba ya aiki, kuma yana nuna saƙon cewa ana gudanar da gyare-gyar

Kotu ta yi watsi da buƙatar gyaran ƙarar zaɓen fidda gwanin APC a Neja

Babbar Kotun Tarayya da ke Minna , Jihar Neja, ta yi watsi da wata buƙata da aka gabatar domin sauya sunayen ɓangarorin da ke cikin ƙarar da ke ƙalubalantar zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC a mazaɓar Magama/Rijau . Ƙarar ta samu ne daga ɗan takarar APC, Shehu Auna , ta hannun lauyansa, Abubakar Danjuma , wanda ke ƙalubalantar sahihancin zaɓen fidda gwani da aka gudanar a ranar 16 ga Yunin 2026 , wanda ya tsayar da Yakubu Auna a matsayin ɗan takarar jam'iyyar. A hukuncin da ya yanke, Mai Shari'a Abdullahi Aminu Dan-Ige ya ce masu ƙarar sun kasa gabatar da hujjojin da za su gamsar da kotu ta a

Takaddama ta ɓarke tsakanin Hisbah da Hukumar Tace Fina-finai kan sana'ar "downloading" a Kano

Takaddama ta ɓarke tsakanin Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab'i ta Jihar Kano kan ikon da ya shafi sana'ar tura fina-finai, wato downloading . Tun da farko, Hukumar Hisbah ta sanar da haramta sana'ar, tana mai zargin cewa wasu na amfani da ita wajen yaɗa fina-finan batsa da sauran abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya da al'adun al'umma. Sai dai Hukumar Tace Fina-finai ta yi watsi da matakin, tana mai cewa sana'ar halastacciya ce, kuma ita ce doka ta bai wa ikon tsara da kuma sa ido kan masu gudanar da ita. Kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman , ya ce irin wannan m

INEC na duba yiwuwar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na gwaji kafin zaɓen 2027

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ( INEC ) ta bayyana cewa tana nazarin yiwuwar gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na gwaji kafin babban zaɓen shekarar 2027 , domin gwada inganci da sahihancin na'urori da sauran kayayyakin zaɓe. Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan (SAN) , ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake karɓar baƙuncin Jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr. Richard Montgomery , a hedikwatar INEC da ke Abuja, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito. A cewarsa, matakin na daga cikin ƙoƙarin hukumar na inganta tsarin gudanar da zaɓe, musamman bayan ƙorafe-ƙorafen da suka biyo bayan

Sakatare Janar na MDD ya yi Allah wadai da hare-haren kan gine-ginen fararen hula a Iran

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) , Antonio Guterres , ya bayyana cewa bai dace a kai hare-hare kan gine-ginen fararen hula ba, yayin da rikicin tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da ƙamari. Iran ta zargi Amurka da kai hare-hare kan wasu gadoji da cibiyoyin sufuri a ƙasar, zargin da har yanzu Amurka ba ta tabbatar da shi ba. Mai magana da yawun Sakatare Janar na MDD, Farhan Haq , ya shaida wa manema labarai cewa Antonio Guterres na ci gaba da nuna matuƙar damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta'azzara, yana mai kira ga ɓangarorin da su kauce wa matakan da za su ƙara rura wutar rikici

Amurka ta tsaurara dokokin zama ga ɗaliban ƙasashen waje

Gwamnatin Amurka ƙarƙashin Shugaba Donald Trump ta sanar da sabbin ƙa'idoji da za su tsaurara dokokin zama da karatu ga ɗaliban ƙasashen waje da ke ƙasar. Sabbin dokokin, waɗanda za su fara aiki daga watan Satumba , sun haɗa da ƙayyade tsawon lokacin zama, da kuma takaita damar ɗalibai na sauya fannin karatu ko canza jami'a. A baya, jami'o'in Amurka ne ke da ikon tsawaita wa ɗalibai wa'adin zamansu bisa tsarin bizar karatu. Sai dai a ƙarƙashin sabon tsari, wannan iko zai koma hannun Gwamnatin Tarayya . Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ta bayyana cewa sabbin matakan na da nufin hana amfan

Kotu ta yi watsi da ƙarar neman INEC ta amince da kwamitin riƙon ƙwaryar PDP na Kabiru Turaki

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da wasu shugabannin Jam'iyyar PDP suka shigar, wadda ke neman a tilasta wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta amince da kwamitin riƙon ƙwaryar jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Kabiru Turaki . Mai Shari'a Salim Ibrahim ya yanke hukuncin cewa masu shigar da ƙarar ba su da hurumin gabatar da ita, saboda haka kotun ba ta da ikon sauraron shari'ar. Alƙalin ya bayyana cewa masu ƙarar sun kasa gabatar da hujjojin da ke nuna cewa INEC ta taɓa amincewa da kwamitin riƙon ƙwaryar da suke goyon baya, ko kuma cewa suna da ikon shigar da ƙara a

Chadi ta soke takardar izinin shiga ƙasar ga 'yan Afirka

Gwamnatin Jamhuriyar Chadi ta sanar da cewa za ta daina buƙatar takardar izinin shiga ƙasar (Visa) ga dukkan 'yan ƙasashen nahiyar Afirka, a wani mataki da ke da nufin ƙarfafa haɗin kan nahiyar da bunƙasa harkokin kasuwanci da zirga-zirgar jama'a. A cewar gwamnatin Chadi, sabon tsarin zai fara aiki ne daga 1 ga watan Janairun shekarar 2027 . Mahukuntan ƙasar sun bayyana cewa matakin zai sauƙaƙa zirga-zirga tsakanin ƙasashen Afirka, ya ƙarfafa cinikayya, zuba jari, yawon buɗe ido da kuma mu'amalar diflomasiyya tsakanin al'ummomin nahiyar. Ana kuma sa ran wannan tsari zai taimaka wajen aiwatar d

An ji fashe-fashe a sassan Iran yayin da Amurka ta ƙaddamar da sabbin hare-hare

An ji ƙarar fashewar abubuwa a sassa daban-daban na Iran , ciki har da yankunan da ke kusa da Tekun Fasha , bayan da rundunar sojin Amurka ta sanar da ƙaddamar da wani sabon zagayen hare-hare. A babban birnin ƙasar, Tehran , rahotanni sun ce an kunna na'urorin kariya daga hare-haren makamai masu linzami domin daƙile barazanar da ake fuskanta. Haka kuma, an ba da rahoton tashin hankali a birnin Ahvaz , da ke kudancin ƙasar kusa da Tekun Fasha. Kafafen yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa an kwashe marasa lafiya daga wani asibiti da ke kusa da wuraren da aka kai hare-haren, domin kare lafiyarsu. A

Kotu ta ba da umarnin ƙwace kadarori kusan 48 da ake alaƙanta su da tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin ƙwace kadarori kusan 48 da ake alaƙanta su da tsohon Ministan Shari'a kuma tsohon Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami . Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ce ta yanke hukuncin bayan ta amince da buƙatar da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gabatar. Kotun ta ce waɗanda suka yi iƙirarin mallakar kadarorin sun kasa gabatar da gamsassun hujjojin da ke nuna cewa sun mallake su ne ta hanyar halastacciya. Mai shari'ar ta bayyana cewa shari'ar ba ta shafi tantance wanda ya mallaki kadarorin ba ne, sai dai tana duba ko kuɗaɗen da aka yi amfani

NIHSA ta yi gargaɗin yiwuwar ambaliya a jihohi 14 na Najeriya

Hukumar Kula da Madatsun Ruwa ta Najeriya ( NIHSA ) ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar samun ambaliya a wasu sassan jihohi 14 na ƙasar tsakanin 14 zuwa 20 ga watan Yuli , sakamakon hasashen cikar koguna da tashin ruwa. Darakta Janar na hukumar, Umar Mohammed , ya bayyana cewa rahotannin hasashen da hukumar ta tattara sun nuna yiwuwar ruwa ya mamaye wasu yankuna, musamman waɗanda ke kusa da manyan koguna da madatsun ruwa. A cewarsa, daga cikin wuraren da ake sa ran za su fi fuskantar barazanar ambaliya akwai Saminaka da ke kusa da Kogin Karam , yankin Madatsar Waya da ke bakin Kogin Waya , da ku

Yadda ake zargin hukumar VIO ta kano da tilastawa mutane biyan kudin duba lafiyar mota da yin watanda da kudin ta Opay din wani jami'i Musa Abdullahi

Yadda ake zargin hukumar VIO ta kano na tilastawa masu mota gwajin lafiyar mota da biyan kudi ta Opay din ma'aikaci Musa Abdullahi maimakon bankin hukumar. Al'ummar Jihar Kano dake bin titin sharada hanyar UBA sun koka Kan yadda ma'aikatan hukumar kula da lafiyar ababan hawa VIO na Jihar kano ke tilasta musu biyan kudin duba lafiyar mota a asusun Opay na wani mai'aikacin kudi ( cashier) Mai dauke da sunan Musa Abdullahi a maimakon asusun Gwamnati Masu korafin sun bayyana cewa a lokatu da dama jami'an hukumar Kan tsare tituna sun tatsar kudi a hannun direbobi musamman wadanda suka raina shigars

INEC ta karɓi jerin 'yan takarar ADC na ɓangaren David Mark, ta yi watsi da na Nafiu Bala

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ( INEC ) ta bayyana cewa ta karɓi jerin sunayen 'yan takarar jam'iyyar ADC da ɓangaren da Sanata David Mark ke jagoranta ya gabatar domin zaɓen shekarar 2027 . Kwamishinan INEC, Mohammed Haruna , ya ce an bai wa ɓangaren David Mark damar amfani da tsarin lantarki na hukumar wajen gabatar da sunayen 'yan takara, bisa hukuncin kotu da ya tabbatar da matsayin shugabancinsa. A cewarsa, ɓangaren ya gabatar da sunayen 'yan takara 471 , waɗanda suka haɗa da: 'Yan takarar shugaban ƙasa biyu , 'Yan takarar majalisar dattawa 109 , Da kuma 'yan takarar majalisar wakil

Gwamnati ta yi watsi da kiraye-kirayen kawo ƙarshen afuwar tubabbun 'yan ta'adda

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da aiwatar da shirin yafewa, karɓar makamai da kuma sake shigar da tubabbun 'yan ta'adda cikin al'umma , duk da ci gaba da suka da kiraye-kirayen da ake yi na dakatar da shirin. A cikin wata sanarwa, gwamnatin ta bayyana cewa ta fitar da wani kundin tsare-tsare da zai jagoranci yadda za a aiwatar da shirin, domin tabbatar da karɓar makamai daga hannun tubabbun 'yan ta'adda, rusa ƙungiyoyinsu da kuma mayar da su cikin al'umma ta hanyar da ta dace. Matakin na zuwa ne yayin da wasu 'yan Najeriya ke ci gaba da nuna rashin amincewarsu

Kotu ta ba da umarnin kamo Adeniyi Adeyemi kan zargin ƙirƙirar hukumar bogi a Nijeriya

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin kamo Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da ƙirƙirar wata hukumar bogi tare da ikirarin cewa shi ne Darakta Janar na hukumar PFIPC. Kotun ta bayar da umarnin ne bayan Adeyemi ya gaza halartar zaman da aka shirya domin fara shari’ar da ake yi masa kan zarge-zargen da ake fuskanta. Rahotanni sun ce hukuncin kotun na nufin jami’an tsaro su kamo wanda ake zargin tare da gurfanar da shi a gaban kotu domin ci gaba da shari’ar. Har yanzu dai ba a samu wata sanarwa daga Adeniyi Adeyemi ko lauyansa ba kan rashin halartar zaman kotun.

Shekara ɗaya bayan rasuwar Buhari: Ina makusantansa suka dosa a siyasa?

Shekara guda bayan rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari , abokansa da na hannun damansa sun gudanar da taron tunawa da shi a Abuja , inda suka yi waiwaye kan rayuwarsa da irin gudunmawar da ya bayar ga siyasar Najeriya. Marigayi Buhari na daga cikin fitattun 'yan siyasar Najeriya da suka yi fice wajen samun gagarumar goyon bayan jama'a. Tun daga lokacin da yake neman shugabancin ƙasa har zuwa nasarar da ya samu a zaɓen shekarar 2015 , ya kasance yana samun ɗimbin ƙuri'u daga magoya bayansa. Buhari ya rasu ne a ranar 13 ga Yulin 2025 a wani asibiti da ke Landan , shekaru biyu baya

Tinubu ya nemi Majalisar Wakilai ta yi wa Kundin Tsarin Mulki kwaskwarima domin samun damar kafa 'yan sandan jihohi

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Majalisar Wakilai ta yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 kwaskwarima domin samar da damar kafa rundunar 'yan sandan jihohi (State Police), yana mai bayyana cewa mataki nada da matuƙar muhimmanci wajen sake fasalin tsaron kasarnan domin fuskantar ƙalubalen tsaro da ke ƙaruwa a ƙasar. A cikin wata wasiƙa da ya aike wa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas , shugaban ƙasar ya miƙa Kudirin gyaran kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (Kafa Rundunar 'Yan Sandan Jihohi), 2026 , domin majalisar ta yi nazari tare da duba yiwuwar amincewa

A Karon farko Daliban Najeriya za su wakilci ƙasar a gasar Spelling Bee ta Duniya da za a gudanar a birnin Shanghai na ƙasar China

Dalibai huɗu daga Najeriya za su wakilci ƙasar a karon farko a gasar Spelling Bee ta Duniya da za a gudanar a birnin Shanghai na ƙasar China daga ranar 10 zuwa 20 ga Yuli, 2026. Tawagar ta Najeriya ta ƙunshi Oluwadamilola Adeolu, Abdurrahman Yusuf, Chinedu Okediachi da Maryam Yusuf, waɗanda suka samu tikitin shiga gasar bayan bajintar da suka nuna a gasar Spelling Bee ta Najeriya da kuma ta Afirka. Masu shirya gasar sun bayyana halartar Najeriya a matsayin wani babban tarihi, suna mai cewa ɗaliban suna ɗauke da fatan al'ummar Najeriya da kuma martabar nahiyar Afirka yayin da za su fafata da fi