Yadda Rundunar yan sanda jihar Kano tayi nasarar cafke mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan Danshagamu
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan wani mutum mai suna Ibrahim Khalil Danshagamu , mazaunin unguwar Gaida da ke Karamar Hukumar Kumbotso a jihar Kano. Rundunar ta ce da misalin ƙarfe 11:30 na daren Litinin, 8 ga Satumba, 2026 , ta samu rahoton gaggawa daga kwamandan kungiyar sa-kai ta Gaida cewa wasu ’yan daba da ba a san ko su waye ba sun kutsa cikin gidan marigayin da ƙarfi tare da kai masa hari da wasu abubuwa masu kaifi. Bayan samun rahoton, jami’an sashen ’yan sanda na Kumbotso sun garzaya wurin da lamarin ya faru. An garzaya da wanda ak
