Matar Gwamnan Jihar Osun ta jagoranci zanga-zangar Mata kan tashe -tashen hankula da kamen Yan jam'iyarsu gabanin zaben Gwamnan jihar
Uwargidan Gwamnan Jihar Osun, Titilola Adeleke, ta jagoranci zanga-zangar mata a jihar domin nuna adawa da abin da suka bayyana a matsayin kame-kame ba tare da ka’ida ba da kuma tashin hankula, gabanin zaben gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar. Matan, wadanda suka fito daga kungiyoyin ’yan kasuwa da masu sana’o’i daban-daban, sun yi tattaki daga hanyar Osogbo zuwa Ilobu, inda suka nufi hedikwatar rundunar ’yansandan jihar da ke Osogbo. Adeleke ta bukaci ’yansanda su gudanar da bincike kan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da take zargi da hannu wajen tashin hankulan da ake samu a jihar. Ta
