AMMASCO RADIO NEWSROOM

local

HUKUMAR TACE FINA-FINAI TA KANO TA DAKATAR DA ADAM GARBA DA AMINA UBA HASSAN

cikin wata sanarwa da Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a madadin Shugaban Hukumar Abba Elmustafha Mai dauke da kawanan watan 16 ga watan mayu 2026, ya bayyana cewa hukumar ta dakatar da Amina Uba Hassan da Adam Garba bayan samun su cikin wannan bidiyo daya sabawa tarbiya. Abdullahi Ya ƙara da cewa, dakatarwar na nufin an hana su gudanar da duk wani aikin fim a Jihar Kano har tsawon shekara guda. Abdullahi ya kuma bayyana cewa dokar hukumar ta bai wa hukumar ikon dakatar da duk wani ɗan masana’antar Kannywood daga gudanar da harkokin fim a Kano, kuma karya wannan doka na iya jawo hukunci mai ts

Rundunar ƴansanda a Najeriya ta kori jami'anta biyar masu muƙamin speta da ke aiki a Patakwal

Rundunar ƴansanda a Najeriya ta kori jami'anta biyar masu muƙamin speta da ke aiki a Patakwal da ke jihar Rivers saboda zarginsu da hannu a ayyukan garkuwa da mutane da fashi da karɓar kuɗi a hannun mutane da kuma cin haci. Jami'in yaɗa labarai na rundunar ƴansanda, DCP Anthony Okon, cikin sanarwar da ya wallafa a shafin rundunar ya ce ƴansandan da aka kora sun haɗa da Speta John Okoi da Speta Eyibo Asuquo da Speta Udo Ndipmong da Speta Bright Nwachukwu da Speta Anele Ikechukwu. Placid ya ce akwai wasu ƴansanda shida daga rundunar da aka samu da hannu wajen haɗa baki da fashi da garkuwa da mut

Gwamnatin Jihar Zamfara ta hana rakiyar maniyyatan aikin Hajji zuwa filin jirgin sama na Gusau yayin fara jigilar su zuwa ƙasa mai tsarki.

Gwamnatin Jihar Zamfara ta hana rakiyar maniyyatan aikin Hajji zuwa filin jirgin sama na Gusau yayin fara jigilar su zuwa ƙasa mai tsarki. Wannan na cikin sanarwar da Mai Taimaka wa Gwamnan Jihar Zamfara kan Kafafen Sadarwa na Zamani Mugira Yusuf ya fitar. Sanarwar ta bayyana cewa maniyyatan jihar za su fara tashi zuwa ƙasa mai tsarki yau Jumu’a ta filin jirgin sama na Gusau. Sanarwar ta jaddada cewa, duk wanda ke da ɗan uwa ko aboki cikin maniyyatan to ya yi musu bankwana a sansanin Alhazai, domin an hana rakiyar su zuwa filin jirgin saman.Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an dauki matakin ne d

Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana shirin ta na gudanar da auren gata karo na uku

Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana shirin ta na gudanar da auren gata karo na uku, inda za ta aurar da zawarawa 300 domin tallafa wa mata da kuma inganta rayuwar iyalai a fadin jihar. Kwamishinar Mata da Ci-gaban Yara ta jihar, Hajiya Halima Hassan Kamba, ce ta bayyana hakan yayin da take gabatar da bayanin ayyukan ma’aikatar ta ga manema labarai a Birnin Kebbi. Ta ce za a gudanar da auren ne a watan Yulin wannan shekara, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin jihar na rage matsalolin zamantakewa da kuma taimaka wa marasa ƙarfi. A cewar ta, shirin yana daga cikin hanyoyin da gwamnati ke bi

Gwamnatin Kano ta bada kyautar Riyal 200 ga kowane maniyyaci.

Gwamnatin Kano ta bada kyautar Riyal 200 ga kowane maniyyaci da ya fito daga jihar, da nufin tallafa musu ta yadda zasu ji dadin gudanar da aikin hajjin su na bana a kasar Saudiyya cikin nutsuwa. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi a wajen horaswa ta musamman a aikace ga maniyyatan Kano yadda ake gudanar da ibadun aikin hajji gabanin tafiyar su kasa mai tsarki. Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Murtala Sule Garo, ya bukaci maniyyatan da su mutunta dokokin kasar Saudiyya yayin gudanar da ibadar ta su, inda ya ce gwamnati ta dauki matakai masu kyau domin

Barista Nuhu Hamza Dantani ya gana da IGP kan zargin tauye haƙƙin jama’a

Fitaccen lauya mai kare haƙƙin bil’adama Nuhu Hamza Dantani ya bayyana cewa ya gana da Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya Olayunji Disu domin tattauna batutuwan da suka shafi zargin take haƙƙin jama’a da ake yi wa wasu jami’an ‘yan sanda. Dantani ya wallafa bayanin ganawar a shafinsa na Facebook ranar Juma’a, inda ya ce a yayin tattaunawar ya yi zargin cewa wasu jami’an ‘yan sanda na tsare mutane ba bisa ƙa’ida ba, tare da cin zarafi ta hanyar duka da kuma barazana. Haka kuma an tattauna batun yadda za a daƙile matsalar faɗan daba a Jihar Kano, tare da neman hanyoyin gudanar da bincike kan k