AMMASCO RADIO NEWSROOM

local

Mai bawa Gwamnan Jihar Oyo shawara ta musamman kan harkokin tsaro Abayomi Fagbenro ya musanta sako mutanen da sace a harin da aka kai makarantu uku a Karamar Hukumar Oriire a ranar Juma’ar da ta gabata

Mai bawa Gwamnan Jihar Oyo shawara ta musamman kan harkokin tsaro Abayomi Fagbenro ya bayyana cewa rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta dake cewa an sako mutanen da aka sace a harin da aka kai makarantu uku a Karamar Hukumar Oriire a ranar Juma’ar da ta gabata ba gaskiya ba ne. Harin da aka kai makarantun ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum biyu tare da sace kusan malamai da ɗalibai 30. Tun daga daren ranar Laraba, rahotannin ke cewa an sako malamai da ɗaliban da aka sace a harin. Sai dai da yake zantawa da manema labarai game da tabbatar da sahihancin labarin, mai bawa gwamanan shawa

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2027

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2027 A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce ya zama ɗantakarar jam'iyyar ne bayan samun kuri’un amincewa daga wakilan jam'iyyar a yayin zaɓen fitar da gwani da aka gudanar a yau Alhamis. Ta ce an gudanar da zaɓen fitar da gwanin ne a gaban jami’an hukumar zaɓe ta INEC. Shugaban kwamitin gudanar da zaɓen Hon. Hafiz Ibrahim Kawu, ya ce an gudanar da zaɓen cikin lumana.

Kungiyar malaman makarantun sakandare da firamare ta kasa (NUT) ‎, ta bayyana matukar damuwa kan yadda hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke kara kamari a makarantu

Kungiyar malaman makarantun sakandare da firamare ta kasa (NUT) ‎, ta bayyana matukar damuwa kan yadda hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke kara kamari a makarantu, tana mai gargadin cewa hakan na iya tilasta malamai janye ayyukansu idan gwamnati ba ta dauki matakin gaggawa ba. ‎A wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Audu Amba, tare da babban sakataren kungiyar suka sanyawa hannu, kungiyar ta ce makarantu sun daina zama wuraren koyarwa cikin kwanciyar hankali, inda suka koma filin hare-haren ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda. ‎Kungiyar ta bayyana hare-haren a matsayin abinda y

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano ta rantsar da ɗalibai sama da 5,000

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano ta rantsar da ɗalibai sama da 5,000, wanda suka fara daukar darasi domin a zangon karatu na shekarar 2025/2026. A yayin bikin da aka gudanar ranar Laraba, shugaban kwalejin, Dakta Abubakar Umar Farouk, wanda Injiniya Dakta Ibrahim Usman Aikawa ya wakilta, ya bukaci sabbin ɗaliban da su rungumi kyawawan ɗabi’u da manufofin makarantar da suka haɗa da gaskiya, ƙwarewa, ladabi, kirkire-kirkire da kuma mutunta juna. Ya kuma ƙarfafa musu gwiwa da su mayar da hankali wajen karatun su tare da amfani da lokacin su yadda ya kamata domin cimma nasara a rayuwa. A w

Hukumar Zabe ta kasa INEC reshen Jihar Kano Za Ta Gudanar da Zaɓen Cike Gurbi na dan majalisar wakilai a Ƙananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa.

Hukumar Zabe ta kasa INEC reshen Jihar Kano Za Ta Gudanar da Zaɓen Cike Gurbi na dan majalisar wakilai a Ƙananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa. Hakan ya biyo bayan rasuwar dan majalisar yankin a kwanakin baya. Hukumar ta sanar da hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana a shelkwatar hukumar da ke Kano. Shugaban hukumar zaɓe ta jihar Kano, Abdu A. Zango, ya ce zaɓen zai gudana a ranar 20 ga watan gobe kamar yadda hukumar ta tsara. Wakilinmu Rabiu Ahmad Kofar Mazugal ya rawaito mana cewa tuni hukumar ta fara dukkan shirye-shiryen da suka dace, ciki har da ɗaukar ma’aikatan wucin

Gwamnan kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar duba yadda aikin titin yankin Farm Centre ke gudana

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar duba yadda aikin sake gina hanyoyin cikin birni ke gudana a yankin Farm Centre da ke cikin birnin Kano. Ziyarar wadda ta gudana a ranar Laraba, 20 ga watan Mayu 2026, na daga cikin matakan tabbatar da inganci da kuma saurin kammala ayyukan more rayuwa da Gwamnatin jihar ke aiwatarwa domin inganta zirga-zirgar al’umma. A yayin ziyarar Gwamnan ya jaddada kudirin Gwamnatinsa na cigaba da bunkasa ababen more rayuwa musamman hanyoyi, domin saukaka harkokin sufuri da kasuwanci a fadin jihar.

Rundunar ƴansandan jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon sashen yaƙi da manyan laifuka irin su fashi da makami

Rundunar ƴansandan jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon sashen yaƙi da manyan laifuka irin su fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma ƙwacen motoci. Kwamishinan ƴansandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori ne ya ƙaddamar da sashen, mai suna: ‘Violent Crime Response Unit’ (VCRU), a ranar Litinin. Ya bayyana cewa an kafa rundunar ce bisa umarnin Sufeto-Janar na ƴansanda, Olatunji Rilwan Disu, da kuma tanadin dokar ƴansanda ta shekarar 2020. Ya ce rundunar zata yi aiki ne bisa tattara bayanan sirri cikin gaggawa tare da haɗin-kan al’umma domin magance matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a wasu sassan jihar

Rundunar Soji da haɗin gwiwar Joint Task Force da Operation Hadin Kai sun samu nasarar daƙile wani hari a yankin Arewa maso Gabas

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarun haɗin gwiwarta na Joint Task Force tare da Operation Hadin Kai sun samu nasarar daƙile wani hari mai ƙarfi da aka shirya kai wa a yankin Arewa maso Gabashin ƙasar, yayin ayyukan tsaro da suke gudanarwa a yankin. Rundunar ta ce sojojin nata sun kuma kama wasu da ake zargi da taimaka wa masu tayar da ƙayar baya da kuma ceto waɗanda aka yi garkuwa da su. A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, harin da dakarun da ke sansanin FOB Gajibo suka daƙile, ana zargin cewa mayaƙan Boko Haram/ISWAP ne suka shirya kai harin inda suka taho da babura daga fannoni daban-dab

Nijeriya ta tsaurara sa ido kan cutar Ebola bayan mutuwar mutane 88 a Congo

Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta sanar da tsaurara matakan sa ido da bincike a dukkan iyakokin ƙasar da filayen jiragen sama, domin hana cutar Ebola shigowa Nijeriya. Babban Daraktan NCDC, Dr. Jide Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi. Ya ce hukumar tana ƙara sanya ɗakunan bincike cikin shirin ko-ta-kwana, da shirin hana yaɗuwar cutar, da wayar da kan jama’a a duk faɗin ƙasar. Matakin ya biyo bayan ayyana cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DRC) da makwabciyarta Uganda a matsayin "babbar matsala ta lafiya da ta shafi duniya baki ɗaya"

Dele Momodu na jam’iyyar ADC ya bayyana cewa, dole su haɗa kai maimakon rarrabuwa a kan kayar da Tinubu a zaɓen 2027

Jigo a jam'iyyar ADC Dele Momodu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels. Inda ya ce, muddin ‘yan adawa na son kayar da Tinubu a 2027, dole su haɗa kai maimakon rarrabuwa a doron yanki-yanki. Dele Momodu ya shawarci ‘yan takarar Kudu irin su Goodluck Jonathan, Peter Obi da Seyi Makinde da su zauna su cimma matsaya kan ɗan takara guda domin gujewa raba ƙuri’un Kudu. Momodu ya jaddada cewa tsarin maslaha (consensus) shi ne mafi dacewa idan har ‘yan adawa suna son kafa hamayya mai ƙarfin da za ta kayar da Tinubu a zaɓen 2027

An Buɗe Sabon Sashen Bin Doka Domin Bunƙasa Tattara Haraji

Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kano, ta ƙaddamar da sabon ginin ofisoshin sashen bin doka da tabbatar da biyan haraji domin inganta aikin ma’aikata da Ƙarfafa tsarin tattara haraji a fadin jihar. Sshugaban hukumar, Dakta Zaid Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin bikin Ƙaddamar da ginin da aka gudanar jiya Talata. Ya ce samar da sabbin ofisoshin na daga cikin ƙoƙarin hukumar na samar da ingantaccen wajen aiki ga ma’aikata domin ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Shugaban hukumar ya ƙara da cewa sabon ginin zai taimaka wajen inganta tsarin bin diddigi da tabbatar da

Ma'aikatar Ilimi Ta Kano Ta Fitarda Tsarin Hutun Babbar Sallah Ga Makarantu

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta sanar da hutun Babbar Sallah ga dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na ma’aikatar, Musbahu Aminu Yakasai, ya sanya hannu yau Laraba. Sanarwar ta bayyana cewa daliban makarantun kwana za su fara hutu daga ranar Asabar 23 ga watan Mayun da muke ciki , sannan su koma makaranta ranar Lahadi 31 ga watan Mayun. Daliban jeka ka dawo kuwa, za su fara hutun ne daga ranar Juma’a 22 ga watan Mayun, tare da komawa makaranta ranar Litinin 1 ga watan Yuni mai zu

An Dakatar da Wani Waje Da Ake Zargin Ana Sarrafa Gurbataccen Man Gyada a Bompai.

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, tare da haɗin gwiwar jami’an lafiya da tsaftar muhalli, sun fara bincike kan wasu mutane da ake zargi da sarrafa gurbataccen man gyada a titin Mai Malari Bompai kusa da Ramin Ranji a Birnin Kano. Shugaban hukumar, Comrade Sa’idu Yahaya, ya ce jami’an hukumar sun kai samame wurin tare da dakatar da ci gaba da sarrafa man har sai an kammala bincike domin kare lafiyar al’ummar Jihar Kano. Shugaban hukumar ya ce bayan samun sahihan bayanan sirri, jami’an sun kai sumame wurin tare da kama kayayyakin da ake amfani da su, yay

Rundunar ’Yan Sandan ƙasar nan ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da haɗa baki wajen sace wani dattijo a Jihar Kaduna domin neman kuɗin fansa, tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47.

Rundunar ’Yan Sandan ƙasar nan ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da haɗa baki wajen sace wani dattijo a Jihar Kaduna domin neman kuɗin fansa, tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47. Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labaran Rundunar, DCP Anthony Okon, ya fitar jiya Talata. Sanarwar ta ce bincike ya nuna cewa Yusuf Rabo, ya haɗa kai da Musa Adamu da Ali Haruna, wanda shi ne jikan dattijon, domin sace mahaifinsa bisa zargin cewa yana da dukiya da dabbobi masu yawa. Binciken ya kuma gano cewa an sace dattijon har sau biyu, inda aka karɓi kuɗin fansa naira miliyan biyu a karon farko da kuma

Rundunar ’yan sandan jihar Yobe ta kama wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka daban-daban

Rundunar ’yan sandan jihar Yobe ta kama wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka daban-daban tare da kwato babur da saniyar sata a wasu samame da ta gudanar a Garin Alkali da ke karamar hukumar Bursari. ‎A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar, ya ce jami’an rundunar sun kama wani mutum mai suna Abubakar Haruna mai shekaru 30 daga Lafiya Lamurde a jihar Adamawa, wanda ake zargi da kwarewa wajen satar babura a kasuwanni da wuraren taruwar jama’a. ‎ ‎ ‎Bayan faruwar lamarin, wasu mutane sun bi sawunsa domin kama shi, inda a yayin gudun tsira ya buge wani dattijo mai

Pantami ya janye daga neman takarar gwamnan Gombe a jam'iyyar APC

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Tsohon ministan sadarwar Najeriya, Isa Ali Pantami ya fitar a shafinsa na Facebook yau Talata, gabanin gudanar da zaɓen fidda gwani a gwamnoni a ranar alhamis mai zuwa. Pantami ya ce ya janye ne saboda rashin bin ƙa'idar da ta dace wajen tuntuɓar ƴaƴan jam'iyyar a kan shawarwarin da ta yanke, da kuma rashin samun tabbacin gudanar da sahihin zaɓe.

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da samar da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana.

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da samar da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana guda 166 domin rage matsalar karancin ruwa da fadada samar da tsaftataccen ruwa ga al’ummar jihar. Mukaddashin Kwamishinan Albarkatun Ruwa na jihar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce shirin wani bangare ne na matakan gaggawa da gwamnatin jihar ke dauka domin magance matsalar ruwa a yankuna daban-daban. A cewarsa, ana sa ran rijiyoyin za su samar da kimanin lita miliyan 4.15 na ruwa a kullum tare da anfani ga mutane kusan 830,000 a yank

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya umarci jami'an tsaro da su murkushe ƴan daba dake addabar cikin birnin Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya umarci jami'an tsaro da su murkushe ƴan daba dake addabar cikin birnin Kano tare da magance ƴan fashin daji dake shigowa jihar ta kan iyakokin Katsina. Kwamishinan ƴansandan Kano, CP Ibrahim Bakori ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron gaggawa na majalisar tsaron jihar Kano. Kwamishinan ƴansandan ya ce al'ummar Kano za su fara ganin sauyi nan da kwanaki uku game da matsalar tsaron dake addabar jihar.

Shin dakatar da jarumai zai gyara Kannywood?

Kannywood ta shafe shekaru tana fama da ƙalubale daga ciki da wajen masana’antar, matsalolin da a wasu lokuta kan janyo tsaiko ga harkokinta. Daga cikin manyan matsalolin da suka fi ɗaukar hankali akwai rikice-rikicen cikin gida, musamman tsakanin Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano da wasu jarumai da masu shirya fina-finai. An kafa hukumar ne a zamanin tsohon gwamnan Ibrahim Shekarau domin sanya ido kan yadda ake gudanar da harkokin fina-finai da bidiyo a jihar Kano. Tun daga lokacin, dokokin addini da al’ada sun kasance cikin abubuwan da ake ganin suna takaita ci gaban masana’antar. Yayin

HUKUMAR YAKI DA RASHAWA TA ICPC, TA MUSANTA ZARGIN HANA TSOHON GWAMNAN JIHAR KADUNA NASIR EL’RUFAI GANAWA DA IYALANSA

Hukumar yaki da rashawa ta ICPC, ta musanta zarge-zargen cewa ta hana iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El’rufai ganawa da iyalansa ya yin da yake tsaren a hannun hukumar. Ta cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta bakin mataimakin shugaban sashin hulda da jama’a na hukumar John Odey, ta ce wadannan labarai da ake yadawa basu da tushe. Ya ce ikirarin da matar tsohon gwamnan ta yi na cewa hukumar ta hanata ganawa da mai gidan nata, ba gaskiya bane, inda ya ce tazo ziyarar ne mintuna 30 bayan lokacin da aka ware domin bada dama a gana da wanda ake tsare da shi. Hukumar ta ce ya kamata a