AMMASCO RADIO NEWSROOM

business

Bankunan Nijeriya sun tara N209bn daga ladan kula da asusu cikin watanni ukun farkon shekarar 2026

Bankunan Nijeriya sun tara N209bn daga ladan kula da asusu cikin watanni ukun farkon shekarar 2026 Wasu sabbin bayanai da jaridar Punch ta tattaro sun nuna cewa bankunan Nijeriya sun tara Naira biliayan 209 daga kudaden da suke cira na kula da asusu (Account maintenance fees) cikin watanni uku na farkon shekarar 2026. Hakan na nuna cewa an samu kari kan Naira biliyan 183 da suka samu a watanni ukun farkon shekarar 2025.

Hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya, ta fara aiwatar da sabbin dokokin da za su bai wa masu amfani da solar damar sayar da wutar lantarki

Hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya, ta fara aiwatar da sabbin dokokin da za su bai wa masu amfani da solar damar sayar da wutar lantarkin da ta yi musu yawa ga kamfanonin rarraba lantarki. Jaridar punch ta bayyana cewa sabon tsarin zai ƙarfafa amfani da makamashi musamman na hasken rana, tare da bai wa masu zuba jari a fannin samar da wuta damar samun ƙarin riba. A ƙarƙashin sabon tsarin, masu amfani da solar za su fara amfani da wutar da suka samar domin bukatunsu, idan kuma an samu wutar fiye da abin da suke buƙata, za su iya tura wa ga kamfanin rarraba lantarki domin sayarwa.

Matatar Dangote Ta Ce Tana da Isasshen Man Jirgi da Zai Iya Wadata Bukatun Duniya

Matatar Mai ta Dangote da ke Najeriya, wadda ke da ƙarfin tace gangar mai 650,000 a kowace rana, ta bayyana cewa tana da isasshen man jirgin sama da za ta iya fitarwa zuwa kasuwannin duniya baki ɗaya, in ji Babban Daraktan kamfanin, David Bird. Bird ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin da yake magana a taron S&P Global Energy Middle East Petroleum and Gas Conference da aka gudanar a birnin London. Ya ce ƙarancin bukatar mai a nahiyar Afirka idan aka kwatanta da sauran yankuna na duniya ya sa matatar ke samun rarar man da za ta iya fitarwa zuwa ƙasashen waje. Ya kuma ce man jirgin sama na da

Cibiyar gas ta South Pars ta janyo wa Iran asarar dala biliyan huɗu

Wani ɗan majalisar dokokin Iran, Jafar Pourkabagani, ya bayyana cewa ƙasar ta yi asarar da ta kai kusan dala biliyan huɗu a filin gas na South Pars sakamakon hare-haren da suka afku yayin rikicin baya-bayan nan. A cewarsa, wannan ƙiyasin ya samo asali ne daga binciken haɗin gwiwa da ƙwararru da masana daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha suka gudanar. Ya ƙara da cewa raguwar ayyukan da aka samu a filin na haifar da asarar kusan dala miliyan biyu a kowace rana. Rahotanni sun nuna cewa a lokacin rikicin, Amurka da Isra’ila sun kai hare-hare kan wasu wurare a filin South Pars, wanda ake ɗauka a matsayi

Gwamnatin Ghana ta amince da aikin haƙar zinare na dala biliyan ɗaya

Gwamnatin Ghana ta zaɓi wani kamfanin cikin gida mai suna Engineers & Planners Ltd domin ya karɓi ragamar gudanar da aikin haƙar zinare na Damang daga kamfanin Gold Fields, kamar yadda ministan harkokin ma’adinai na ƙasar ya bayyana a ranar Talata. Matakin na daga cikin ƙoƙarin da Ghana ke yi na ƙarfafa kamfanonin cikin gida a fannin haƙar ma’adinai, musamman a masana’antar zinare da ƙasar ta shahara da ita. A bara ne gwamnatin Ghana ta ƙi sabunta lasisin kamfanin Gold Fields mai hedkwata a Johannesburg, inda ta karɓe ikon gudanar da aikin haƙar ma’adinan na Damang, lamarin da ya kawo ƙarshen

Gwamnatin jihar Anambra ta bayyana cewa tana kokarin bunƙasa noma ta hanyar sarrafa amfanin gona

Gwamnatin jihar Anambra ta bayyana cewa tana kokarin bunƙasa noma ta hanyar sarrafa amfanin gona a matakin masana’antu domin bai wa manoma damar samun kuɗaɗen ƙasashen waje ta hanyar noma na kasuwanci da fitar da kayayyaki zuwa waje. Kwamishinan Noma na jihar, Ben Odoemena, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da kamfanin sarrafa amfanin gona na Ideal Agro Allied Produce Limited da ke yankin Akwaeze a ƙaramar hukumar Anaocha. Kamfanin, zai riƙa sarrafa doya, rogo, dankali da sauran nau’o’in amfanin gona domin fitar da su zuwa ƙasashen waje. Odoemena ya ce gwamnatin Gwamna Chukwuma Soludo za ta f

Attajirin ɗan kasuwa Femi Otedola, ya bayyana shirin sa na saka hannun jarin dala miliyan 100 a matatar mai ta Dangote.

Attajirin ɗan kasuwa Femi Otedola, ya bayyana shirin sa na saka hannun jarin dala miliyan 100 a matatar mai ta Dangote. Otedola ya bayyana hakan ne bayan wata ziyara da ya kai matatar a ranar Laraba. Ya ce hannun jarin na daga cikin shirin tara dala biliyan biyu da matatar Dangote ke yi daga hannun masu zuba jari masu zaman kansu kafin fitar da hannun jarin kamfanin a kasuwa. A cewarsa, ya tattauna da Aliko Dangote sau da dama, inda ya nemi a ware masa hannun jari na dala miliyan 100 a cikin tsarin sayar da hannun jarin kamfanin. Otedola ya bayyana cewa daya daga cikin dalilan da suka sa ya sa