AMMASCO RADIO NEWSROOM

Kasuwanci

Air Peace Ta Ƙaddamar da Sabbin Hanyoyin Jirage Zuwa Ƙasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka

Kamfanin sufurin jiragen sama na Air Peace ya faɗaɗa ayyukansa a yankin Afirka bayan ƙaddamar da sabbin hanyoyin zirga-zirga daga Legas zuwa Bamako a ƙasar Mali, Conakry a Guinea, Douala a Kamaru da kuma Libreville a Gabon. Kamfanin ya bayyana cewa ƙaddamar da waɗannan sabbin hanyoyi na da nufin ƙarfafa haɗin kai da sauƙaƙa zirga-zirgar fasinjoji tsakanin ƙasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka. Air Peace ya kuma ce sabon tsarin zai ƙara bunƙasa matsayin Legas a matsayin babbar cibiyar haɗa zirga-zirgar jiragen sama ta yankin, tare da samar da ƙarin damar kasuwanci, yawon buɗe ido da bunƙasa cinik

Manyan Kamfanonin Mai Sun Samu Ribar Yayin Rikicin a Iran

Manyan kamfanonin mai a duniya sun ba da rahoton ribar da ba su taɓa samu ba, sakamakon tashin farashin danyen mai da ya biyo bayan rikicin Iran. Kamfanin Saudi Aramco , wanda shi ne mafi girma wajen samar da danyen mai a duniya, ya bayyana cewa ribarsa ta ƙaru da kashi 44 cikin 100 a rubu'i na biyu na shekarar nan. Hakan ya faru duk da rufe Mashigar Hormuz da Iran ta yi da kuma hare-haren mayaƙan Houthi kan jiragen ruwan Saudiyya a Tekun Maliya. Haka kuma, manyan kamfanonin makamashi na ƙasashen Yamma guda biyar— BP, Chevron, ExxonMobil, Shell da TotalEnergies —sun sanar da haɗaɗɗiyar riba da

OPEC+ Ta Amince da Ƙara Haƙar Mai Daga Watan Satumba

Ƙasashen da ke cikin ƙungiyar OPEC+, waɗanda suka haɗa da Saudiyya da Rasha, sun amince da ƙara yawan haƙar ɗanyen mai da ganga dubu 188 a kowace rana daga watan Satumba. An ɗauki wannan mataki ne domin rage tasirin rikicin Gabas ta Tsakiya a kasuwar mai ta duniya da kuma biyan buƙatun da ake da su. Masana harkar mai sun bayyana cewa wannan mataki bai zo da mamaki ba, domin tun kafin yanzu sun yi hasashen cewa OPEC+ za ta ƙara yawan haƙar mai domin daidaita farashin man fetur a kasuwannin duniya. Sai dai rikicin da ke yankin ya haddasa cikas ga safarar mai, musamman sakamakon takunkumin zirga-

Iran Ta Kulla Yarjejeniya Da China Kan Sayen Makaman Kare Sararin Samaniya

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Iran ta kulla yarjejeniya da China domin sayen makaman kare sararin samaniya da ake harbawa daga kafaɗa, tsakanin guda 300 zuwa 400. Majiyoyi uku da ke da masaniya kan yarjejeniyar sun shaida wa Reuters cewa ana sa ran Iran za ta fara karɓar kason farko na makaman cikin 'yan makonni masu zuwa. A cewar majiyoyin, darajar kwangilar ta kai tsakanin dala miliyan 60 zuwa 70, kuma ana kallonta a matsayin wani muhimmin mataki na Iran wajen ƙarfafa kariyarta daga hare-haren jiragen sama. Sai dai wasu majiyoyin sun bayyana cewa duk da an rattaba han

Farashin Danyen Mai Ya Sauka Bayan Dakatar Da Hare-Haren Amurka Da Iran

Farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya ragu zuwa kusan dala 90 kan kowace ganga , bayan da Amurka da Iran suka dakatar da hare-haren da suke kai wa juna domin bai wa tattaunawar diflomasiyya damar ci gaba. A ranar Litinin, farashin Brent Crude ya ragu da kashi 6.76% zuwa dala 90.24 kan kowace ganga, yayin da US West Texas Intermediate (WTI) ya fadi da kashi 6.04% zuwa dala 83.92 kan kowace ganga. Rahotanni sun ce faduwar farashin ta biyo bayan dakatar da hare-haren da ɓangarorin biyu suka yi a ƙarshen mako, bayan kusan makonni biyu ana musayar hare-hare. Jakadan Amurka a Majalisar Ɗinkin D

Iran Ta Fitar da Gangar Ɗanyen Mai Miliyan 73 Bayan Sassaucin Takunkuman Amurka

Iran ta samu damar fitar da kusan gangar ɗanyen mai miliyan 73 cikin ƙasa da wata guda, bayan da Amurka ta ɗan sassauta wasu daga cikin takunkuman da ta ƙaƙaba mata kan fitar da man fetur. Rahotanni sun nuna cewa daga ƙarshen watan Yuni zuwa tsakiyar watan Yuli, jiragen dakon mai na Iran da dama sun fara bayyana a yankin ruwan gabashin Malaysia, suna jigilar ɗanyen mai zuwa kasuwannin ƙasashen Asiya. Kamfanin Kepler , mai sa ido kan harkokin jigilar makamashi, ya bayyana cewa darajar ɗanyen man da Iran ta fitar a wannan lokaci na iya kaiwa kusan dala biliyan shida . Sai dai duk da wannan ci ga

Farashin Ɗanyen Mai Ya Kai Dala 100 Kowace Ganga Sakamakon Rikicin Gabas ta Tsakiya

Farashin ɗanyen man fetur a kasuwar duniya ya kai dala 100 kowace ganga, karo na farko tun watan Mayu, sakamakon tsanantar rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya. Ɗanyen mai samfurin Brent , wanda ake amfani da shi a matsayin ma'aunin farashin mai a duniya, ya ƙaru da sama da kashi shida cikin ɗari a ranar Alhamis. Hauhawar ta biyo bayan ci gaba da hare-haren da Amurka ke kai wa Iran da kuma ƙarin fargabar da rikicin ya haifar a kasuwannin makamashi. Haka kuma, hare-haren da mayaƙan Houthi na Yemen suka kai kan jiragen dakon mai a Tekun Maliya sun ƙara tayar da hankalin masu zuba jari,

Kotu ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga mutum uku da aka samu da laifin sace dalibai da malamai a Jihar Oyo

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutane uku hukuncin ɗaurin rai da rai bayan ta same su da laifin hannu a sace ɗalibai da malamai a Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo. Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Abdulrazak Umar, wanda aka fi sani da Abu Khalifa ko Abu Khalid, Yunusa Musa (Yunusa bin Musa) da Shamsu Adamu Sani (Abu Itisar). Mai shari’a Salim Ibrahim ne ya yanke hukuncin, inda ya bayyana cewa hukuncin ɗaurin rai da rai zai fara aiki daga ranar da aka kama waɗanda aka samu da laifin. An gurfanar da mutanen uku kan tuhume-tuhume guda 10 da suka haɗa da ta’addanci, garku

Matatar Dangote ta mayar da farashin sayar da man fetur zuwa dala maimakon naira

Matatar Man Dangote ta fara amfani da farashin dala wajen sayar da man fetur da sauran kayayyakin da take samarwa, maimakon tsarin farashin naira da aka saba amfani da shi. Rahotanni sun nuna cewa matakin ya biyo bayan yadda Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ke sayar wa matatar mafi yawan ɗanyen man da take buƙata a farashin dala. A cewar rahotannin, sauyin tsarin farashin na nufin cewa masu sayen man fetur daga matatar za su biya bisa farashin dala, lamarin da masana ke ganin zai iya sauya yadda ake ƙayyade farashin man fetur a kasuwar cikin gida. Masana tattalin arziki sun bayyana cewa sabo

Matatar Dangote Ta Fara Jigilar Fetur Kyauta Zuwa Jihohi Shida Da Abuja

Matatar Man Fetur ta Dangote ta fara jigilar fetur kyauta zuwa jihohi shida a faɗin Najeriya, ciki har da Babban Birnin Tarayya, Abuja. Kamfanin Dangote ya sanar da fara wannan shiri ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta na X a ranar Laraba. A cewar kamfanin, shirin na da nufin sauƙaƙa isar da man fetur zuwa sassa daban-daban na ƙasar tare da inganta samar da kayayyakin man fetur ga masu amfani. Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani kan tsawon lokacin da shirin zai gudana ko kuma sauran jihohin da za su ci gajiyarsa a mataki na gaba ba. Ana sa ran wannan m

Hada-Hadar Kudade

DOLLAR ₦ 1,370 UAE DIRHAM ₦ 378 CEFA ₦ 2,391 RIYAL ₦ 365

Mece Ce Makomar Kuɗaɗen Masu Ajiya Bayan CBN Ta Soke Lasisin Bankuna 46?

Bayan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke lasisin bankunan microfinance 46 , ƴan Najeriya da dama sun fara nuna damuwa kan makomar kuɗaɗensu da ke ajiye a waɗannan bankuna. CBN ta ce matakin ya biyo bayan gazawar bankunan wajen cika ƙa'idojin da doka ta tanada, ciki har da rashin isassun jari, dakatar da ayyuka ba tare da izini ba, da sauran matsalolin gudanarwa. Shin kuɗaɗen masu ajiya za su salwanta? A'a. Bisa dokokin Najeriya, Hukumar Inshorar Kuɗaɗen Ajiya (NDIC) ce ke da alhakin kare masu ajiya idan aka soke lasisin banki. A cewar masana harkokin banki, NDIC za ta fara tantance bayanan m

NMDPRA Ta Gargaɗi Gidajen Mai Kan Farashin Fetur

Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Najeriya ( NMDPRA ) ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauki mataki kan gidajen mai da ke sayar da fetur a farashin da bai dace da sauyin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ba. Hukumar ta bayyana cewa tana ci gaba da sa ido kan yadda ake sayar da fetur, tare da tunatar da masu kasuwanci su bi ƙa'idojin da suka shafi farashi. Wannan gargaɗi ya biyo bayan kira da wasu jami'an gwamnati suka yi na a tabbatar masu amfani da man fetur sun amfana da duk wani sauyin farashi da ake samu a kasuwar duniya.

Farashin ɗanyen mai nau’in Brent ya faɗi sosai bayan samun sauƙin rikicin Gabas ta Tsakiya da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin da ke rikici.

Yayin da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya koma matakin da yake kafin rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran, har yanzu masu amfani da man fetur a Najeriya ba su ga wani gagarumin sauyi a farashin man a gidajen mai ba. Farashin ɗanyen mai nau’in Brent ya faɗi sosai bayan samun sauƙin rikicin Gabas ta Tsakiya da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin da ke rikici. Tun da farko, tashin hankalin ya haddasa fargaba a kasuwannin duniya, musamman saboda barazanar rufe mashigin Hormuz, wata muhimmiyar hanyar jigilar mai da kusan kashi ɗaya bisa b

Farashin mai ya faɗi sakamakon hasashen yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka

Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya faɗi zuwa mafi ƙasƙantar mataki cikin kusan watanni huɗu, sakamakon ƙaruwa da fatan cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran. A safiyar ranar Juma’a, farashin ɗanyen mai na Brent ya sauka zuwa dala 87.33 a kowanne ganga, inda ya ragu da dala 3.05 ko kimanin kashi 3.4% idan aka kwatanta da ranar da ta gabata. Haka kuma, farashin ɗanyen mai na Amurka (WTI) ya ragu zuwa dala 84.88 a ganga, raguwar dala 2.83 ko kuma kashi 3.2%. Wannan shi ne mafi ƙasƙancin farashin WTI tun cikin kusan watanni uku, daga watan Afrilu da ya gabata. Dalilin fad

HADA-HADAR KUDADE

Yadda canjin kudaden kasashen ketare zuwa Naira ke gudana a kasuwannin chanji a yau 10-06-2026. • DOLLAR ₦1,390 • UAE DIRHAM ₦380 • CEFA ₦2,440 • RIYAL ₦350

HADA-HADAR KUDADE

Yadda canjin kudaden kasashen ketare zuwa Naira ke gudana a kasuwannin chanji a yau 09-06-2026. • DOLLAR ₦1,380 • UAE DIRHAM ₦360 • CEFA ₦2,440 • RIYAL ₦350

Rikicin Iran da Isra’ila ya tayar da farashin man fetur a kasuwannin duniya

Farashin danyen mai ya fara tashi a kasuwannin duniya sakamakon rahotannin musayar hare-hare tsakanin Iran da Isra’ila, lamarin da ya ƙara tayar da fargaba kan yiwuwar tsanantar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya. Masana tattalin arziki sun bayyana cewa damuwar yiwuwar faɗaɗa rikicin na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa tashin farashin mai a kasuwannin duniya, musamman ganin yankin na taka muhimmiyar rawa wajen samar da makamashi. Rahotanni sun nuna cewa farashin man Brent ya ƙaru da kashi 4.5 cikin ɗari, inda ya kai kusan dala 97.30 kan kowace ganga. Haka kuma, man West Texas Intermediat

Dangote Ya Ƙara Yawan Man Fetur Da Matatarsa Ke Tacewa A Rana

Matatar man fetur ta Dangote ta ƙara yawan ɗanyen man da take tacewa zuwa ganga 700,000 a rana, bayan wani gwajin da hukumomin da ke kula da harkokin matatun mai suka gudanar. Sabon adadin ya nuna cewa matatar ta ƙara ƙarfin aikinta daga ganga 650,000 zuwa 700,000 a kowace rana, lamarin da ke ƙara kusantar da ita ga burinta na zama ɗaya daga cikin manyan matatun mai a duniya. Mataimakin shugaban sashen mai da iskar gas na kamfanin Dangote, Devakumar Edwin, ya ce wannan ci gaban na cikin shirye-shiryen faɗaɗa ayyukan matatar domin ninka yawan ɗanyen man da take tacewa zuwa ganga miliyan 1.4 a r

NAHCON ta yi kira ga alhazan Najeriya da su cike takardun bayanan Lafiyarsu kafin komowa gida

Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta bukaci dukkan alhazan kasar da ke shirin komawa gida bayan kammala aikin Hajjin bana da su tabbatar sun cike takardar bayanan lafiyarsu (Health Declaration Form) kafin tashinsu daga Saudiyya. Kamar yadda wata sanarwa ta bayyana, tuni aka raba takardar ga tawagogin likitocin jihohi tun daga tashin jirgin farko na alhazan bana. Hukumar ta ce ana bukatar tawagogin likitocin jihohi su taimaka wa alhazan da ba su iya karatu ko rubutu wajen cike takardar domin kauce wa jinkirin da ka iya tasowa a filayen jiragen sama da zarar sun isa Najeriya. Sanarwar ta ce a