Fararen hula 1700 aka kashe tun fara yaƙin basasar Sudan – Bincike

Wani bincike da aka gudanar ya gano cewa an kashe fararen hula 1700 a hare-hare ta sama da sojojin Sudan suka kai tun bayan fara yaƙin basasar ƙasar fiye da shekaru 2 da suka gabata.

Binciken ya ce an kai hare hare kan gidajen jama’a da kasuwanni da makarantu da kuma sansanonin ƴan gudun hijirah inda aka kashe adadin waɗannan mutanen.

Sojojin Sudan ɗin ne dai kawai suke da irin waɗannan jiragen da suka kai hare haren.

Mayaƙan RSF da ke faɗa da sojojin Sudan kuma ake zarginsu da aikata kisan kiyashi ba su da irin waɗannan jiragen.

Wakiliyar BBC ta rawaito cewa rundunar sojin Sudan ɗin ba ta ba wa BBC amsa akan bukatar da ta yi na mayar da martani akan wannan binciken da aka yi ba, kodayake a baya ta sha musanta zarge zargen kai wa fararen hula hari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *