Aƙalla mutum 20 sun mutu sakamakon gobara a Indonesia

Wata gobara da ta tashi a wani gini mai tsawo a babban birnin Indonesia, ta yi ajalin mutum aƙalla ashirin.

Shugaban yansandan Jakarta ya ce masu kashe gobara na ci gaba da duba ginin ko akwai sauran mutanen da ke makale a ciki.

Wakiliyar BBC ta ruwaito cewa hukumomi sun ce da alama gobarar ta samo asali ne bayan da wani batir ya fashe a wani kamfanin da ke ƙera jirage marasa matuƙa da ke ginin.

Hukumomin sun ƙara da cewa akasarin waɗanda suka mutu mata ne, ɗaya daga cikinsu tana da juna biyu, kuma da alama sun mutu ne sakamakon shakar hayaƙi.

Hayaki mai kauri ya turniƙe saman benen yayin da masu kashe gobara suka yi amfani da motocin kashe gobara 28 da kuma ma’aikata kusan 100 domin shawo kan gobarar.

An dai kashe gobarar kuma ma’aikatan agaji na mayar da hankali kan neman waɗanda ake tunanin sun maƙale a cikin ginin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *