Ƙasashen Turai sun yi watsi da daftarin sabon tsarin tsaron Amurka

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya ce ƙasashen Turai za su iya kare dimokradiyyarsu, kuma ba sa buƙatar wani katsalandan daga Amurka.

Mista Merz na mayar da martani ne kan sabbin tsare tsaren tsaron Amurka da ta wallafa, wanda a ciki a ka ce Turai na fuskantar barazanar shafewar ala’adu saboda yawaitar baƙi.

Mista Merz ya ce ba za su amince da wasu sassan tsare tsaren ba, kuma hakan na sake nuna buƙatar ƙasashen Turai su tsaya da ƙafarsu a fannin tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *