Gwamnatin Tarayya ta yi Allah wadai da kisan wasu ’yan Najeriya biyu da aka yi a Afirka ta Kudu, tare da neman gudanar da bincike cikin gaggawa kan musabbabin mutuwarsu.
Mai magana da yawun ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Oluwafemi Adeniyi, ya ce lamarin ya ƙara jefa shakku kan tsaron baƙi a Afirka ta Kudu, musamman ’yan Afirka, a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar hare-haren ƙyamar baƙi a ƙasar.
Ya ce zargin hannu ko sakaci daga jami’an tsaro a mutuwar ‘yan Najeriya na ƙara dagula dangantakar da tuni ta yi tsami tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu.
Gwamnatin Najeriya ta buƙaci hukumomin Afirka ta Kudu su gudanar da bincike mai zurfi, da gaggawa kan mutuwar mutanen biyu, tare da gano waɗanda ke da hannu a lamarin kuma a hukunta su bisa doka.
Lamarin ya zo ne yayin da dangantakar Najeriya da Afirka ta Kudu ke fuskantar sabon rikici sakamakon hare-haren ƙyamar baƙi da ake kai wa ’yan Najeriya da sauran ’yan Afirka.
A ranar Juma’ar da ta gabata, Majalisar Dokokin kasar nan ta dakatar da duk wata ziyara da hulɗar hukuma da Afirka ta Kudu saboda hare-haren da ake kai wa baƙi, musamman ’yan Najeriya.