Rundunar ‘yansandan ta kasa reshen Jihar Zamfara ta ce ta fara bincike domin gano wasu malaman Addinin Musulunci shida da aka sace a kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara a Zamfara.
Rahotanni dai sun ce malaman suna hanyarsu ta komawa gida bayan zuwa wani taron addu’a na Jam’iyyar APC a Zamfara.
‘Yansandan sun ce tuni suka baza jami’ansu domin ceto malaman da aka sace.
’Yan bindiga sun sace limaman Musulunci shida a kan hanyar Dakko–Damri da ke ƙaramar hukumar Bakura ta Jihar Zamfara.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar jiya Asabar, lokacin da wasu ’yan bindiga ɗauke da muggan makamai, waɗanda ake zargin suna da nagartattun makamai, suka yi wa wata mota da ke ɗauke da waɗanda lamarin ya rutsa da su kwanton ɓauna.
A cewar ’yan sandan, mutanen shida, waɗanda dukkaninsu limaman Musulunci ne, suna tafiya ne zuwa Talata Mafara lokacin da maharan suka tare su tare da yin garkuwa da su.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, CP A. M. Bello, ya umarci jami’an da ke gudanar da aikin ceton da su ƙara kaimi tare da amfani da dukkanin kayayyakin da suke da su domin tabbatar da an ceto waɗanda aka yi garkuwa da su cikin aminci.